Sashe 25
Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
tace lfy lau,yace yasu yapendo dasu hadiza,tace duk lfyansu lau. Kallonshi takeyi da alamun tambaya ganinshi sanye da kaki,murmushi ya mata yace yadai,tace zakaje wani gurinne,ya rik'o hannunta yana wasa dashi da hannunsa masu laushi gashi sunyi sanyi yace eh zan fitane amma zuwa azahar zan dawo. Tace lfy dai ko,yace lfy lau sema alkhairi idan na dawo zakiji komai kinji,tace toh Allah ya taimaka Allah yasa ka fita a sa'a,yace ameeen thankyou sannan ya mik'e tsaye itama ya mik'ar da ita tare da rungumeta tsam,tace dan Allah ka bari idan wani ya shigofa,yace babu wanda zai shigama ki saki jikinki kinji,jin hakan yasa ta sake sosai a jikinsa tanajin k'amshi jikinsa. D'agowa yayi yace kardai har kin fara bacci,mirmushi tayi tace bacci kuma anan,yace eh mana gashi naji kin sake kamar kin samu gado,kunya sosai taji tare da k'ok'arin janye jikinta amma sam yak'i,tace toni ka barni tunda har tsokanata kakeyi,yace nifa wasa nake miki,murmushi tayi tace to muje,ya saketa tare da cewa ina kenan,suna kallon junansu,taace muje ku gaisa dasu yapendo kafin ka tafi,yace apple a hakan tare da nuna jikinshi,tace eh mana aiba komai,yace wlh dai bazan iyaba tare da rik'o hannunta suka wuce d'akinshi. Agado ya zaunar da ita tare da mik'a mata flower mai kyau yace naso in baki jiya amma sena mance har kika tafi,tayi murmushi tace thankyou tarr da sashi a hanshinta tana jin kamshinsa,yace bari in canja kaya idan naje muka gaisa se inzo inmaida kakin ko,tace to tare da mik'ewa zata fita yace ina zakije,tace zanje in sanar dasu zaka shigone,yace a'a kijirani mu tafi tare dawo ki zauna,bata soba amma haka taje ta zauna,shi kuwa wall drop ya bud'e ya d'auko jallabiyarsa fara tas mai adon glod sannan ya cire kayansa daga shi se boxer da singilet,sam maryam tak'i kallonsa harya saka jallabiyar yasa turare,inda taji kamshi seta juyo dan taga turaren nan suka had'a ido shi kanshi ya lura da abinda take kallo sannan ta juya,zuwa yayi har inda take yace kinason turarenne? Kai ta d'aga mishi alaman eh,murmushi yayi tare da bud'e gun ajiye turarensa ya d'auko mata guda d'aya a cikin kwalinsa yazo ya bata,murna tayi tare da cewa nagode,yace bakomai tashi muje,mik'ewa tayi kuma yana tsaye a gabanta da turarensa a hannunshi,yace bari in fesa miki nawa tunda a bud'e yake,to tace dashi sannan yahau fese mata harda cire lullub'inta da hannunshi yayita fesa mata yana k'arewa kirjinta kallo,kunya sosai tajitace aiyi haka,yace kin tabbata tace eh,nan ya ajiye turaren batare dayaje ko inaba sannan ya d'auki gyalenta ya yafa mata kamar yadda tayi,kallon juna sukeyi suna murmushi tace nagode,yace nima nagode sannan ya d'auki takalminsa yace muje yana rik'e da hannunta suka k'arasa gun steps. Anan ya tsaya ita kuwa ta haura yanata kallonta taje ta sanar musu sannan ta dawo tace mishi bismillah,yace ok sannan yaa rike da ita a kafad'a har suka isa gun k'ofa shinefa ya saketa tayi saurin wucewa d'akinta shi kuwa ya tsuguna yana gaishesu. Maryam tana shiga ta ajiye turaren da kuma flower tana mai murmushi,hadiza tace tofa hmmm wato seda kika sakeyin wanka acan harda turare,tace eh d'in banafa nason sa ido ni inadai yazama mijina tofa ku kiyayeni kuma kar wanda ya bud'e turarennan bare kuma ku tab'amin flower yara sesa ido kuka iya tana murgud'a musu baki ta fice sunata binta da kallo. D'akinsa ta shiga da sallam harya maida kakin sojojinsa,seya ganta da tea a hannunta da kuma bread ga blueband duk a tirei tasasu ta ajiye tace kasha kafin ka fita. Hakan yayi mishi dad'i sosai data nuna kulawarta akansa,shi kuwa manosh baya shan tea mai madara amma dayake ta had'o bayaso yak'i sha haka ya zauna ta mik'a mishi cup d'in take yaji zuciyarsa tana tashi da madaran dayaji,yannunsa yasa a kirjinsa,tace lfy,yace zuciyanane yake tashi wlh,tace toko in had'o maka lipton kawai,yace wannan kuma fa,tace nise insha,yace ok sannan ta fita taje ta had'o ta kawo nishi. Ya karb'a tare da cewa thankyou yasha kuwa sosai tanata kallon yadda yake cin abinchi abin birgewa,kunnenta yaja yace banace miki banaso kallo ba,hannunta tasa akan nashi tace kayi hakuri nifa bakai nake kalloba,seya saki kunne yace nayi karya kenan,tace a'a haka yaci gaba tanata kallonshi harya gama. Sannan yace tokisha,tace zansha amma ba'a nanba,yace toshikenan nizan tafi,ta mik'e tace to Allah ya dado da kai lfy,yace ameen sannan ya mik'a mata kud'i yace karb'i wannan maybe zaki aiken wani abu kasuwa kodai wata buk'ata,tace wlh a'a bana buk'atan komai kuma akwai kud'i a hannuna sosai wlh,yace sam seta karb'a take ta b'ata rai tace ni wlh bana so wlh akwai kud'i a hannuna mai yawa,yace nawane,tace 70k,yace apple kin tabbata,tace wlh kuwa,yace toshikenan gadai kud'i anan ya nuna mata walldrop nashi yace idan kina da buk'ansu kina iya d'auka koma nawa kinji jealousy nah,nan ta b'ata rai yayi saurin rungumeta yace am sorry sunanne kawai yazomin a baki yanzu sorry my luv,shuru tayi,yace haba apple yanga zakiminne to shikenan na fasa fita mukwanta muyi bacci,ido ta zaro tare da cewa na hakura wlh,dariya yayi yace dama kina da idanu manya haka,kunya taji tace muje karkayi late,yace ok tare dasa takalminsa se kallonshi takeyi tanajin dad'i tare da godewa Allah,d'agowa yayi yace apple pls bana son yawan kallo kinji,itadai abin yana bata mamakiyi kuma taga da gaske yake,tace meyasa to? Yace idan na dawo zan gaya miki,tace to tare daci gaba da kallonshi,rungumeta yayi tare da tsotsar lips nata sannan ya saketa yace idan na dawo zan naidasu yapendo kinji,tace to sannan ya tafi ita kuwa ta d'auki tirai ta fice ta dawo ta gyara mashi ko'ina sannan ta rufo kofan ta taho da key d'in d'aki. Lubna ce agun miher tanata kuka tace yanzu shikenan wanda zuciyata take k'auna ya zama mijin wata,kuka sosai takeyi miher amarya se bata hakuri takeyi tace haba lubna tunfa jiya kike abu d'aya,kiyi hakuri kibarwa Allah komai idan bro manosh mijinkine tofa dole seya aureki. Lubna ta bud'e jajauen idanunta tace pls kidena zolayata nafasan irin k'aunar da captain yakeyiwa maryam,baya iya 5minit baiji muryantaba kuma bro marwan yacewa mum wlh manosh yayi alk'awarin cewa maryam ita kad'aice manosh yake kauna duk fad'i duniya. Miher tace hakane amma ai komai yana gun Allah ne bagun bro manosh,lubna dai sam tak'i se kuka takeyi tare dajin haushin maryam kuma ayanzu. Azuciyarta tace wlh dabadan saddam ya cuceniba dasena auri manosh kota wace hanyace danni shi kad'ai nake so,ibrahim kawai dan dai asirina zai rufune badan ina sonshiba wlh,kai amma maryam kinyi sa'an samun miji kamar bro manosh,mik'ewa tayi ta shige toilet tanata kuka sannan ta wanke fiskanta ta fito miher sebinta da kallo takeyi tare dajin tausayinta gashi duk sunyi aure banda ita. Abinci lafiyayya aka kaiwasu maryam daga gidansu manosh,na safe daban na rana ma daban. Tunda manosh ya fita bai kira maryam ba se 3:37pm yace da ita albishirinki,tace goro,yace fari ko ja,tace fari tas kamar fiskarka. Murmushi yayi yace toshikenan ganinan dawowa nafiso inga fiskarki lokacin da nake sanar dake,murmushi tayi tace to seka iso. Zuwa 4pm manosh ya iso gida,wayanta ya kira taje d'aki ta sameshi,ya cire kayanshi harya shiga wanka,kayan nashi ta nad'e ta mayar walldrop,sannan ta fito mishi da wanda zaisa. Tana zaune ya fito da towel a west nashi,sam tak'i d'agowa har seda yasa data fito mishi dashi yace nagode,tace dame,yace da fito min da kayan sawana,murmushi tayi tace kaci abincine? Yace nachi wlh acan akoshe nake apple "thanks for d care" zama yayi kusa da ita yace juyo kina kallona,ba musu ta fiskance,yace k'iran da akamin bana koai bane sena k'arin girma daga captain manosh zuwa asistan major,kallonsa tayi har cikin ido cikin mamaki tace kad'in,yace wlh kuwa, rungumeshi tayi sosai sedaya fad'i akan gadon. Kunya taji tayi saurin tashi tace kayi hakuri murnane yamin yawa,alhamdulillah Allah ya tayaka rik'o akan gaskya da adalci peach nah,yace ameen my luv tare da kissing d'in hannunta yace su yapendo sun shirya,tace eh tun d'azu,yace ok muje bari abokina yaje ya musu magana,tace to tare da komawa d'akinta. Bayan isarta da 5minit abokin yayi sallama yace hadiza wai kufito muje inkun gama,tace to sannan ta gayawa su yapendo suka shirya tsaf suka fito,nan maryam ta fara kuka dataga zasu tafi a barta ita kad'ai. Su nafisa kuwa se zolayarta sukeyi haka suka tafi aka barta ita kad'ai agidan tanata kuka. Manosh bai dawoba harse bayan magrib abokanshi suka rakoshi lokacin maryam tana karatun qur'an yashigo d'akinta da sallamarshi...... [7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by sad-nas