← Book details Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 45

Sashe 33

Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

majid yake iya k'ok'arinsa domin kwantar mata da hankali,hakama maryam kullum nasiha iyayenta suke mata da kuma yah ibrahim dasam baya son ganinta cikin damuwa,hakan yasa zaibada k'odanshi guda d'aya asawa maryam,amma sam koda aka gwada baiyi daidaiba. K'awayen maryam gabad'aya sun zama abin tausayi domin ganin irin halin da maryam take ciki,rashida tace da marwan ita aje a gwadata idan har a'a iya sawa maryam k'odanta to wlh ta bayar da guda d'aya tunda zasu iya rayuwa da d'ad'd'aya, marwan yace karki dau luv zamu samo mafita amma ina tausayin aunty sosai wlh,friend na manoh dukkansu basa iya kocin abinci saboda rashin abokinsu,kowa yasan irin shak'uwar da take tsakaninsu. Mahaifiyar manosh kuwa ta zama Allah sarki domin sun d'auki son duniya sun d'aurawa manosh dayake shine d'ansu na fari. Kuma duk wanda yasan manosh ko kuma wata alak'a dake tsak'aninsu tofa dole ya shiga damuwa. Cikin sati biyu lbrn manosh ya baza ko ina dayake sojane mai kwazo ga kuma taimakon marasa k'arfi,sam bayida kyama kamar dai matarsa wato *auntyn yara*. Lubna ce kwance a gidansu tana cewa mum nata gaskya mum lokaci yayi daya kamata in taimakawa maryam akan taimako da rufin asirin data min,mum zanje inba maryam k'odata guda d'aya,bazan iya bari anemo k'odan wani dabamu saninshiba asawa maryam. Hajiya khadija tace lubna lfyarki kuwa bana so ki sake sa bakinki cikin maganannan,kuma wace irin taimako maryam tayi miki haka? Lubna cikin muryan kuka tace mum kinsan me,ada bani da wata mak'iya irin maryam saboda yadda nake k'aunar bro manosh araina,babu wanda yasan hakan dagani se miher naso in sanar dashi amma dayake shiba mijina bane senaji cewa ya samu mata a girei,nayi bak'in cikin hakan sosai tunma bansan wacece yake nemaba,ranan muka had'u da maryam da kuma friends nata a yakubu shopping plaza na yarda keyn motata batare dana saniba ta biyoni ta bani anan ne muka san juna da maryam harna karb'i numbernta. Mum daga bayane na san cewa maryam itace yarinyar da bro manosh yake so,tun daga lokacin tsanarta ya shiga zuciyata nayi niyan d'aukan mataki sosai dan in raba maryam da bro manosh. Lubna tayi shuru tana kuka sosai cikin tausayawa tace mum kinsan me? Nice nasa akayi kidnaping maryam lokacin da aka kusayin aurensu,nasa akayi nesa da ita yayinda nake samun duk wata lbr agun miher wanda ita kanta basan inada hannuba,tun daga numan nasan aka sakeyin nesa da ita mum zuwa jejin yankari dake jihar bauchi,amma dayake Allah ba azzalumin bawansa bane dukda cewa ita maryam tasan cewa nine nasa ayi mata hakan amma sam tak'i gayawa ko iyayenta da suka haifeta ta b'oye zancen cikin ranta domin bataso asamu matsala tsakanin familynmu da kuma familyn su bro manosh saboda tasan irin shak'uwa da soyayya dake tsakanin bro marwan da kuma bro manosh hakan yasa tayi shuru tabar komai aranta mum. Marwan yana tsaye abakin k'ofa ya kasa shigowa yana sauraron lbrn da lubna take baiwa mum nasu,wanda mamakine sosai abaiyane a fiskarsa. Lubna taci gaba da cewa mum bayan maryam ta dawo gidane,shi wanda na basu aikin yace inje muyi magana domin maryam tasan komai kuma k'ila zata tauna musu asiri,tsoron kar sunana ya fito dan yadda nake tsoro bro marwan yasa ranan na fita naje can inda saddam yake ya bayan GG..kuka lubna ta fashe dashi tace mum koda naje juice ya siyaya mana nidashi,ban kawo komai a rainaba saboda k'ishin danakeji a wannan lokacin kawai sena canye wannan juice d'in,shikenan ban sake sanin inda nakeba kodana farka senaji jikina wani iri mum saddam ya cuceni yamin fyad'e.... Mum ta kama salati tare da kwalla a idanunta itama lubna haka tace naso na kira miher amma senayi tunanin bazata rufamin asiriba dole za'a sani,shine na kira maryam ban b'oye mata komaiba na gaya mata komai,kinsan me mum hankalin maryam ya tashi sosai take tazo inda nake mum ta taimakamin ta kimtsa kaina hawayene cike a idanunta tare da tausayawa,muna tare da ita su bro manosh sukazo gun nida maryam muna ciki d'akin ab'oye a toilet munata addu'a saboda maryam tayiwa bro manosh k'aryan cewa tana cikin kasuwa suna sayayya se kuma gashi yazo inda muke a d'akin saddam,hankalin maryam ya tashi sosai badan komaiba sedan jinin dake kan katifar saddam kuma gashi ni babu yadda nake alokacin jikina rawa kawai yakeyi. Cikin ikon Allah mukaji suna cewa saddam ya gudu kenan tunda gashi harda kwad'o ajikin kofan,kuma wlh mum babu wanda ya kullemu ta waje,seda suka tafi muma muka fito da sauri shine maryam ta kawoni har gida tayi miki k'aryan cewa bigeni akayi da mota naji ciwo a k'afa,kuma mum maryam itace ta had'ani da ibrahim wanda yake matsayin yayanta,bata b'oye mishi komai akan batun fyad'en da aka minba ta gaya mishi komai,tare da neman amincewarsa akan ya aureni,k'aunar da ibrahim yakeyiwa maryam ne yasa ya aureni badon yana sonaba,kuma wlh mum koda na rana d'aya ibrahim bai tab'a nuna kyamarsa akainaba se kauna da kulawa na musamman kuma har gobe babu wanda yasan da wannan zance fyad'e dagani se maryam da ibrahim duk maryam tayi hakanne don ta rufamin asiri mum da kuma k'aunar da take min,gaskya mum maryam macece wanda ba'a samun irinsu a zamanin yanzu,ina ganin k'aunarta aduk lokacin da muka had'a ido da ita. Dan haka zan iya yiwa maryam komai koda hakan zaisa in rasa rayuwatane to lallai zanbawa maryam k'odata guda d'aya watak'il zan iya biyanta da alkhairan datamin arayuwa...... Ba mum kad'aiba harta marwan dake tsaye a waje ya shigo rai a b'ace,take lubna ta gudu bayan mum dan yadda ta ganshi tasan sarai yaji komai dan haka ta fara kuka sosai tana cewa waiyo mum dan Allah karki bari ya dakeni wlh ina da ciki mum,bro marwan dan Allah kayi hakuri. Mum tace karka tab'ata marwan nace ka kyaleta! Cak marwan ya tsaya yana kaima lubna sakon harara yace baga irintananba mum,daga taimako gashi ta b'ata mana suna tayi abin kunya,ke bari kiji ingaya miki dabadan cikin dake jikinkiba wlh yau dase na kusan karyaki wawiya mara hankali dole kibar mana gidanmu dan dama ke 'yar tsuntuwace ni kad'ai iyayena suka haifeni tsintattiyar mage kawai ya fita rai a b'ace ya fisgi mota. Daga lubna har mum kuka sukeyi lubna tana bin mum da kallo mai d'auke da tambaya tace mum menaji bro marwan yake cewa? Wainiba 'yarku bace? Tsuntoni kukayi hakane mum? Mum da kuka yaci karfinta tace hakane lubna keba 'yarmu bace. Lubna ta tsaya da kukanta tace tosu waye iyayena mum,a ina kuka samoni mum,meyasa kuka b'oyemin mum? Mum cikin kuka ta rik'o hannun lubna tace shi kanshi dad naku baisan iyayenkiba lubna domin ce mishi nayi na tsuntokine,lubna keba 'yar kowa bace se 'yar Alhaji muh'd atta. Zaro ido lubna tayi tace wanne kenan mum? Mum ta rungumeta tace wanda dai kika sani mahaifin maryam *auntyn yara* ku 'yan biyune lubna maryam itace babba sannan ke uwarku d'aya ubanku d'aya da ita lubna ki gafarceni dan Allah,cikin mamaki lubna ta janye jikinta tace taya hakan ya faru kenan mum? Kina nufin kowa yasan hakan kenan? Mum tace babu wanda ya sani dagani se hajiya iya kakarki lubna. Kuka sosai lubna takeyi tare da barin palon da gudu...... [7:14am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by sad-nas & Hama gee muh'd *dedicated to sis fatima tahir* 71-72 Da sauri auntyn yara ta waigo donjin me lubna take cewa,kai se sukayi gwaru akansu atare sukakai hannu goshinsu don sunji zafi dukkansu. Maryam ta karb'i wayan hannunta tare da cewa sannu lubna ita lubna sannu take mata suna masu kallon junansu cike da murmushi,maryam tabar d'akin da sauri ta koma d'akinta tare dasa wayan a kunnenta tace cikin zumud'i tace *hello peach*, muryan manosh yace apple ya kike yasu abdallah,lfyanmu lau peach nah ina ka shiga ka barmu da tashin hankali da kewa,yace kiyi hakuri apple yanzuma na kirakine dan in gaya miki cewa ki mance dani a rayuwarki kwatakwata kamar baki tab'a had'uwa daniba domin bazan sake dawowa garekuba apple ki cireni a zuciyarki su abdallah kuwa ki gaya musu cewa na mutu kuma mamaci baya dawowa ta yadda zasu manceni daga k'arshe kuma ki samu miji wanda kike ganin zai rik'e min su alfiya ki aura koda d'aya daga cikin abokainane wannan shine dalilin dayasa na kiraki kinji apple,ya k'arashe maganan cikin murya maiban tausayi. Ita kuwa maryam tunda taji abinda ya fara fad'a taketa zubda hawaye harya k'arasa. Jin tayi shurune ya sake kiran sunanta apple pls am sorry,na zab'i hakanne dan in cetoki daga sharrin shukrah bawai don wani abuba...bai k'arasa maganaba naryam ta katseshi da cewa ya isheni haka peach bana son sakejin komai daga gareka indai akan wannan magananne mubarta kawai,yanzu ka gayamin ya yake a ina kake me kuma shukrah tayi maka haka peach? Yadda manosh yaji muryan apple bashi yasan tana cikin tashin hankali,yace karki damu da sanin halin da nake ciki apple dama abinda na kira in gaya miki kenan ina miki bankwana ta karshe. Da sauri da kuma ihu tace pls peach karka katse wayannan ka saurari abinda zance maka,ina cikin wani hali sosai peach na rashin lfy,k'odata gabad'aya sun b'aci dole se an min dashe,yanzu haka ana shirye shiryen fita dani india ne dan haka ka saurareni wata k'ila maganata dakai na k'arshe kenan zaiyu idan najema bazan dawoba dan haka inaso ka yafemin dukkan wasu abubuwa dana maka na rashin sani,sannan ina so ka sani har inbar duniya babu wani d'a na miji dazan iya zama dashi bayan kai kuma har inbar duniya bazan dena yin addu'a Allah ya d'auraka akan shukrah daduk wani abu mai cutarwa ameen,inaji ajikina cewa zaka dawo garemu peach,sedai bana tunanin zaka sameni sedai iyayenka da kuma yaranmu peach dan Allah ka kula min dasu domin kune farin cikina daga k'arshe ina k'aunarka k'auna ta hak'ik'a wanda baya k'arewa _i love you so much peach_, alfarma d'aya zan nema agunka shine inji kalmar soyayyata abakinka pls...? Kwalla sosai manosh yakeyi idanunshi kamar attarugu,amma ina bazai iya gaya mata kalmar so ko d'ayaba,dan haka yace ina miki fatan alkhairi apple se anjuma...... Kuka sosai maryam ta fashe dashi tana cewa peach dan Allah karka barni ka tsaya ka gayamin cewa kana sona dan Allah my captain,kuka sosai takeyi tana kallon wayan. Mama da
Chapter 33 · 0% Book details