← Book details Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 45

Sashe 8

Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tare da sunkuyar da kansa k'asa yana tusayin yayan nashi don shi kad'ai yasan irin k'aunar auntyn yara da yakeyi amma dayake bai gama karatunshiba shiyasama baiyiwa mahaifinta magana akaiba yafiso seya gama komai na karatunshi. Ibrahim yace kaje ina zuwa,sannan abdallah ya tafi jikinshi a sanyaye. Ibrahim ya kunna wayanshi ya kira number'n maryam ringing d'aya ta d'aunka tare da salma,wani irin dad'i yaji har cikin ranshi dajin daddad'ar muryanta. Yace aunty wai kina nemana,murmushi tayi tace eh na kira wayanka ban samuba,yace wlh na kashene saka makon damuna da akayi,tace eyyah,yace ganinan ina zuwa ki basu hakuri kinji,tace laa bakomai wlh sunanan a waje dama gurinka kawai sukazo. Yace tonagode da mutuntani da kikayi aunty se anjuma,tace bakomai aikafi haka a guna uncle ibrahima nima nagode. Koda ya ajiye wayan shi kad'ai yasan meyakeji a cikin ranshi game da maryam. Ya k'arasa gumsu da sallama suka gaisa sosai kuma cikin fara'a dama shi ibrahim na kowane kamar dai maryam d'in. Hira sukayi sosai kamar sun dad'e da sanin juna,yayi musu tambayoyi suka bashi amsan gaskya domin wani abunba manosh b'oyewa yakeyi,sam bayaso asan mahaifinshi mai arzikine. Haka sukaitayidai har suka gama sannan suka sallama ibrahim ya wuce gida,se manosh ya kira maryam a waya yace aunt pls ki fito in ganki zamu wuce,tace har gun gaisa kenan zaku tafi,yace eh wlh ibrahim yana da kirki sosai wlh gaskya naji dad'in had'uwa dashi,dad'i taji da aka yabi ibrahim tace nagode nidai bazan fitoba aiba gurina kazoba,ya marairaice murya yace pls aunt kinga marwan yanata min dariya ai gara shi tunda rashi bata nan hankalinsa a kwance "pls come aou aunt"kodon fita kunya a idon marwan don wlh yau idan muka koma shimenan ya samu abun tsokana harsu majid sesunji. Dariya tayi tare da katse wayar d'inkin atamface a jikinta na fitet gaun seta sa himar iya gwinwanta ta fito. Tunda ya hangota yake murmushi tare da k'are mata kallo harta iso gunsu tana murmushi,marwan yace ai wlh banso ki fito har addu'a nakeyi a raina amma se gashi kin fito meyasa aunt,mirmushi tayi tace saboda banaso ku mishi dariya,manosh yace "thankyou aunt"tare da kaiwa marwan bugu a bayansa yayi saurin shigewa mota gurin tuk'i ya rufe kofar maryam tanata dariya. Manosh ya dawo da kallonshi kan maryam yace wato har kin fara min yanga ko,tace aiba yana bane dama gun uncle ibrahim kukazo ba gunmuba,yace eh amma dai ai kinsan zanso in gaki ko,tace to ai gashi ka ganni kuma ni zan wuce gida,yace nidai ban sallamekiba tukunna,tace to sallameni,murmushi yayi wanda ya k'ara mishi kyau tana kallonshi shi kuwa wani gurin yake kallo daban. Tace wlh ka dingayin mirmushi yana k'ara maka kyau,dad'i yaji sosai yace wauace ki kalleni,mirmushi tayi tace ni ban kallekaba kawai dai na fad'a makane,yace kin kalleni mana kuma ai ke kika sani na fara murmushi sosai wlh,tace ahakan,yace "yes" ki tambayi miher zata gaya miki ni gaskya bancikayin fara'aba, yace hmmm to gaskya nidai ka dinga yi kaji,yace ai inayi kuma danke. Tace to shikenan zan wuce,yace meyasa kikemin hakane aunt kodon kinga ina sonki sosaine shiyasa kike min haka,tace a'a wlh aiba guna kazoba kuma ai min gaisa,yace to shikenan mun tafi,tace kayi fushi kenan,yace a'a banyiba kawai dai zamu tafine,kallonshi takeyi amma sam yak'i kallonta kuma yana tsaye yana fiskantarta,tace toshikenan Allah ya kiyaye hanya,yace ameen sannan ta juya ta shiga gida,mota ya bud'e yashiga marwan yaja suka tafi. Manosh ya saba idan suka bar girei seya kira maryam a hanya,amma yau sam sebai kirataba abun yad'an dameta tace to kodai fushi yayine? Har bayan 2hrs bai kiraba,kuma a wannan lokacin tasan suna gida,marwan ne ya kirata yace aunt mun iso gida lfy,tace alhamdulillah tona gode sosai,yace bakomai wlh mune da godiya sannan sukayi sallama. Har bayan isha manosh bai kira maryam se taji taba kyauta mishiba dan tasan fushi yayi dukda dai basu tab'a samun matsalaba se yau. Har 9:00pm seta d'auki wayanta ta kirashi yanata ringing harya d'auke,zata sake kira kenan setaga call d'inshi,ta d'auka cikin sanyin murya tace hello Shuru yayi baice komaiba Ta sake cewa hello Nanma shuru yak'i yayi magana, tace hello manosh, Karon farko data kira sunanshi kenan,seyaji dad'i har cikin ranshi amma baice komaiba,ta sake cewa "manosh pls talk 2me" yace me kike so nace miki aunt? Tace wai fushi kakeyi danine, shuru yayi uanajin daddad'ar muryanta,ta sake cewa "manosh am talking to you" yace inace ni kike kora agaban marwan ko? Wani iri taji a ranta dan yadda yayi maganan batasan lokacin datace "am so sorry manosh i din't main to hurt you pls?" Nanma shuru yayi,ta sake cewa manosh wai bazaka min magana bane kuma kanajina? Yace "yes" take jikinta yayi sanyi tace manosh am sorry pls,nanma shuru yayi seta katse wayan. Hankalinta ya tashi sosai tayi dana sanin yimasa hakan. Har 10pm manosh bai sake kirantaba,seta tsinci kanta cikin damuwa sosai sam ta kasa sakewa,dan tana son manosh sosai acikin ranta. K'arar shigowar texs tayi a wayanta da sauri ta d'auka ta bud'e taga _Am sorry too apple_ _I love you so much_ _Nd i will call you leta_ _Am talking with my dad now okey,manosh loves you so verry much apple_. Maryam tana gama karanta texs d'in taji dad'i sosai a ranta tayi murmushi tana mai k'ara jin sonshi na ratsa jikinta,tace i love you too peach tare da rufe idanunta tana murmushi..... [7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by sad-nas & Hama gee muh'd *Dedicated 2 sarah katagum* 23-24 Seda manosh suka gama magana da dad nashi,sannan ya koma d'aki ya kira maryam har gurin 11:00pm. Maryam har tayi bacci,ta jiyo wayanta na k'ara da d'auka tare da sawa a kunnenta amma idonta a rufe yake tace hello,cikin muryan bacci, yace "apple am sorry for waking you up"tace "don worry manosh am fine"muryanta ya kashe mishi jiki gabad'aya atake yaji inama tana kusa dashine. Sakeyin k'asa da muryanshi yayi yace "are you sure" tace "yeah am fine"ai manosh aiseya fara juyi akan gadonshi yace "no apple you have to sleep"zan kiraki da asuba kinji,tace "okey good night" yace sweet dreams apple,murmushi kawai ta mishi tare da katse wayar. Manosh ya sauke ajiyar zuciya yace "ooh my apple"Allah ya nunamin ranar da zan mallakeki a matsayin matata,da wannan tunanin bacci ya kwasheshi. Wannan karon manosh baiyi tfy ba,har akayi nisa da azumi sannan suka kaiwa 'yan matansu kayan sallah a d'inke kuma masu tsada,da kuma redimate ga fashions ga takalma da jaka da turare komai dai suka had'o musu kowa da irin nashi,sannan sukayiwa iyayensu,harta abdallah seda manosh da marwan suka mishi kayan sallah. Almajirai sam basa so azumi ya k'are,gashi indai a girene to kusan rabinsu sunsan maryam. Daidai da sabulun wanki ko omo haka zatayita raba musu 1/1 tace suyi wanki dashi,dan haka suna sonta sosai. Azumi ya k'are yau gobe sallah se murna akeyi su maryam ansha kitso gata da gashi amma sam ita tafi so tayi kitso akan tabar kanta haka,su rashida kuwa wanke kai kawai sukayi amma zahida kitso tayi da ameena babale,su samirane yan wanke kai,gashi suna lalle gayu dai sosai sukayi. Manosh bai samu zuwa rananba dan haka maryam tayi *cake* mai dad'i kuma had'ad'd'e dama duk sallah tanayi. Mhaifinta kuwa drinks ya sayo kala kala dan yasan 'yar tashi da jama'a bugu da k'ari suna son maryam sona hak'ik'a zai iya kashe duk dukiyarsa dan farin cikin maryam,shiyasa ma idan ka shiga d'akin maryam wlh bazaka tab'a zatan cewa a cikin gidansu d'akinta yakeba dan yadda mahaifinta ya gyara mata shi,gurin zuba littattafaima na musammanne,ga computer komai dai se wanda ya gani. Yau take sallah kowa se murna su maryam suka shirya shirya tafiya *idi* anko suka sha ita da rashida da samira da himar nasu neavy blue toyobo dogaye har k'asa masu hannu sunyi ado sosai se k'amshi sukeyi. Mama tazo tace to maryam kinyi bak'o a waje,tace bako kima mama,tace eh,da sauri ta mik'e ta fita kawai setaga drivern manosh ne da *406* ash wai yazo ya kaisu masallaci. Mamaki ya kama maryam tace wlh kaje kawai masallacin fa babu nisa da k'afa zamu tafi,yace a'a madam idan na koma fad'a zaimin kiyi hakuri. Shuru tayi tace to ina zuwa,nan ta koma ta sanar da mamanta,mamanta tace to maryam kuje kawai tunda haryazo, haka suka fito abdallah ne a gaban motan su kuwa ukun suna baya sunata salati zikiri har suka isa, sannan yayi pakin a gefe shima yaje akayi sallah. *Allahu Akbar Allah ka k'ara dauwamar damu a musulunci ameen* Bayan an idarne sukaita hotuna a wayansu,ai se suka hango uncle ibrahim da friends nashi nan suka wuce aka gaisa sannan sukayi pictures da uncle ibrahim da kuma friends nashi yana tsaye kusa da maryam hotunan sunyi kyau sosai,shima driver se d'aukansu yakeyi a tap batare da sun saniba,amma sam bai d'auki su ibrahim ba. Bayan sun gama ne sukayi sallama sannan suka zo gun drivern ya maidasu gida. *cake din* maryam ta zuba mishi a kula tare da soyayyen naman kaza da kuma ruwan faro mai sanyi ta bashi,karb'a yayi tare da godiya ya tafi. Bayan tfyanshine ta kira manosh tace mun godefa,yace bamun b'ataba meyasa kika kirani,tace godiya na kira in maka sannan kuma....yace sannan kuma me, tace inaso ka kawo min *miher* anjuma mu yini,yace coman kike bani kenan,tace *no captain* alfarma nake nema,yace nak'i bazan kawotaba,tace haba mana pls ka kawota,yace nak'i d'in,tace to shikenan ni zanzo gurinta anjuma,murmushi yayi yace zan turo azo a d'aukeki sannan ya katse wayar ya sake kiranta. Ta d'auka tace bana bukata dama zamuje gun zahidane se mu wuce gurin ameena. Yace wa kika tambaya babu inda zakije,tace saboda da me,yace ra'ayinane hakan,shuru tayi tace to shikenan ka kawomin miher dan tace seka yadda kafin take fita wani girin pls ka barta,yace sekin ce *am sorry peach* dariya tayi tace menayi to,yace nidai na gaya miki,tace ok am sorry peach,murmushi yayi yace tosekin fad'a da muryana,tace ni mace kai miji ai muryanmu dabanbanci bazan iya ba,yace to bazata zoba,tace pls mana captain,yace wlh sekinyi muryana, nan dai ta gyara muryanta wai a dole zatayi irin nashi,ai tun bata k'arasaba take dariya shima haka take ta katse wayar tanata dariya shima hakanne muhsin yace ku kamashi muje gun malam
Chapter 8 · 0% Book details