← Book details Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 45

Sashe 27

Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tsoro sosai taji da yadda yake buga kofan,toilet ta shiga tayi alwala tazo tayi sallah raka'a 2 ta zaunayin addu'a sosai. Manosh ta jiyo yana cewa wlh idan kika yadda na bud'e kofannan tofa gawanki za'afitar. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un taketa yi tare da addu'uoi. Yah ibrahim ne kawai ya fad'o mata arai,nan ta d'auki waya ta kirashi lokacin 10:5pm bugu d'aya ya d'auka baice komaiba tace yah ibrahim dan Allah kazo yanzu,akwai matsala amma pls karka gayawasu mama komai,hankalinshi atashe dajin yadda take kuka yayi saurin zuwa gun babanta yace abashi aron mota yanzu zai dawo,batare da b'ata lokaciba baba ya bashi keyn hondansa,dan motar maryam kam tun ran biki yakai mata shi gida. 15minit sega ibrahim a gate d'in gidan manosh,amma maigadi ya hanashi wucewa seda ya kira maryam ta waya ya had'asu kafin yabar ibrahim ya shigo da saurin. Jin tsayuwar mota yasa manosh yadawo daidai, take ya fara cewa apple meyasameki ,meyasa kike kuka bud'emin kofan kinji apple, ita kanta taji sauyin mura tattare dashi, mamakine ya kamata amma sam tak'i bud'e mishi. Bugun kofan falon k'asane yasa manosh barin gurin yaje ya bud'e kawai seyaga yah ibrahim ne a tsaye suna kallon juna cikeda mamaki,manosh baisan babu riga ajikinsaba sedayaga irin kallon da ibrahim yake mishi sannan yalura da jikinsa dagashi se boxers..... [7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by sad-nas *this page is dedicated to fans of tana raina,i luv u all* 59-60 Bismillah yace da ibrahim,cikin jin kunya ya wuce sama domin sa kaya. Ibrahim ya zauna yana jiran fitowan maryam. Bayan manosh ya sako jallabiyane yaje kofan d'akin maryam saboda kukanta dayakeji,take hankalinsa ya tashi yanta cewa apple pls apen d door,ahankali ta bud'e tana rakub'e ajikin kofa sanye da doguwar riga da kuma gyalenshi. Rungumeta yayi sosai dan ganinta wani iri,ita kuwa sam takasa sake jikinta se fama kwacewa takeyi,manosh ya lura da hakan yace apple meke faruwane meyasa kike kuka,kallonshi ta tsayayi cike da hawaye tace bakaivabe ka shak'eni kace zaka kasheni dak'ar na kwaci kaina agunka dubi wuya kaga yadda kamin peach mena maka hakane, kallon wuyanta yake ga alamun hannun mutum kuma yayi jah shatin hannun ya zauna a wuyanta sosai. Hannu manosh yakai yana tab'a tare da cewa apple ni kuma,yaushe na miki hakan,kallonshi ta tsayayi cikin mama da kuma tsoro tace ka matsamin zanje gun yah ibrahim,se anan ya tuna da yah ibrahim yazo,tace nina kira yah ibrahim a waya nace yazo dan ka biyo har nan kashe idan ka shigo kasheni zaki nikuma ina jin tsoro shine na kirashi. Rungumeta yayi yana magana cikin nadama yace apple wlh bansan komai akan abunda kike gayaminba pls apple kiyi hakuri karki gayayawa ibrahim komai,yaushe akayi airen har za'a fara jinmu,pls apple wlh niban miki komaiba taya za'ayi in miki haka kuma? Itadai gabad'a bata gane mishiba dan haka tace to muje gun yah ibrahim,yace kimin alkawarin bazaki fad'a,shuru tayi tace muje bakomai,nan suka firo a tare tana sauka k'asa tayi gudu taje inda ya ibrahim yake ta zauna kusa dashi tare dayin kuka tace yah ibrahim ka d'aukeni mu tafi gida wlh kasheni zaiyi kaga abinda yaminfa. Afusa ibrahim ya mik'e dan yasan maryam bazata tab'a mishi karyaba,yace captain meke faruwane,metayi haka da irin wannan shatin dake wuyanta? Manosh ya juya a sanyaye yana kallon maryam yace haba apple yanzu haka zakimin,wlh ibrahim niban mata komaiba meyasa kikamin haka apple? Maryam tana kuka tace wlh yah ibrahim shine,sedana buga mishi flower a wuyansa sannan ya sakeni wlh kaine peach babu yadda za'ayi inyi maka karya wlh yah ibrahim cewa yayi zai kasheni kuma wlh banyi ishi komaiba. Manosh kamar zaiyi kuka se rantsuwa yakeyiwa ibrahim yace shi wlh baiyi mata komaiba,ibrahim yace yanzu maganan waye zan kama acikinkune kaina ya d'aure wlh. Maryam tace yah ibrahim na tab'a maka karya,kuma menene ribana idan nayiwa mijina karya,wlh Allah shine ya shakeni tare dayin wasu maganganu wlh yah ibrahim ba karya nake mishiba. Manosh yayi shuru danya rasa mema zaice,ibrahim ya kira marwan a waya yace kazo ina gidan manosh yanzu pls. Marwan ya kalli rash da take kwance ajikinshi yace kiyi hakuri zanje gun ibrahim in dawo kin,tace pls karka dad'e dan tsoro nakeji,yace bazan dad'eba my darling sannan ya shirya ya tafi. Cikin k'ankanin lokaci ya iso cike da tunanin komeya faru ibrahim ya kirashi kuma gidan captain. Da sallama ya shigo tunda yaga maryam kusa da ibrahim yasan akwai matsala,bayan ya zaunane yace captain,manosh yace yane,sannan suka gaisa da yah ibrahim. Yah ibrahim yace marwan wani abune ya d'aure min kai sosai gaskya shiyasa na kiraka ko zamu samu mafita,marwan yace okey meya faru yana kallon maryam kanta a sunkuye,ibrahim ya gaya mishi,mamakine bayyane a idon marwan yace gaskya kozaka kwana kana gayamin bazan tab'a yadda abokina zaiyiwa aunty hakaba saboda mune shaida akan irin k'aunar da yake mata taya kuma za'ace manosh ya shak'eta da sunan zai kasheta a wani dalili? Ibrahim yace kamar yadda ka yarda da manosh ka kuma san halinshi,tonima haka na yarda da aunty na kuma san halinta bazata tab'amin karyaba wlh,sannan idan ka dubi wuyanta zaga shaidan abinda take fad'a,kuma lokacin dana shigo da kuma yanayin danaga captain ya tabbatar min acewa akwai matsala,kodai manosh yana da wata matsala ko kuma wani abu da baya so? Marwan yace gaskya bayi da wata matsala ko damuwa,abu d'ayane muka san baya so shine mace tayita kallonshi sam bayason haka. Ibrahim yace bayasan mace ta kalleshi,to saboda me? Marwan yace shidai haka nashi tsarin yake kuma komu bamusan dalilinba kawai dai yace mana shi kawai baya sone. Ibrahim yace to aunty kodai kallonshi kiketayi,dariya abin yabaiwa marwan yace to idan aunty ta kalleshi kuma seya shaketa? Ibrahim yace eh mana tunda dama baya so,marwan yace amma kuma harda aunty gaskya dai ban ganeba abokina meke faruwane? Wani irin mugun kallo manosh yakeyiwa maryam wanda tsoro ya kamata tace yah ibrahim kaga kallon da yakemin ko,wlh ni bazan zaunaba zan bika mu koma gida dan idan kun tafi kasheni zaiyi wlh...bata k'arasaba manosh yayi kanta tare da sake shak'eta yana cewa wlh bazaiyuba baki isaba wlh! Ibrahim da marwan suka mik'e domin tsaidashi,amma ina sun kasa ita kuwa maryam se tari takeyi suna kallon juna da manosh wanda babu alamun tausayi a fiskanci gashi su marwan sun kasa karb'armaryam a hannunshi kuma da hannu d'aya ya shaketa. Marwan yace manosh meke damunkane me kuma haka,aunty cefa saketa mana dama ashe gaskiya zaka kasheta kenan? Yace eh kasheta zanyi dan wlh baki isaba maryam kinyi kad'an,maryam ta fara fita hayyacinta tana magana dakyar tana cewa yah ibrahim zai kashenifa. Ibrahim yace marwan matsa baya,ba musu marwan ya matsa dan abin yabasu tsoro,ran yah ibrahim a bace ya bige hannun manosh da dukkan karfinsa take manosh ya fad'i akan carpet,ita kuwa maryam bayan ya ibrahim ta koma tare da rik'e mishi riga tana tari tace yah ibrahim kaganiko,wlh bazan zauna dashiba,tausayinta ya kamasu dukkansu,da sauri marwan ya d'auki wayanshi ya kira dad d'in manosh yace dad kazo gidan manosh akwai babban matsala. Shi kuwa ya ibrahim zaunar da maryam yayi akan kujera ya nufi kan manosh yanata karatun qur'an danya fahimci cewa balaifin manosh bane tun lokacin da yaga irin kallon da manosh yakeyiwa maryam kafin ya nufi kanta. Maryam dai kuka kawai takeyi marwan yace mata sannu,shi kuwa ibrahim karatu kawai yakeyi da k'ira'a irinta abdallah,hakan yasan maryam tsananta kukanta sosai fiye dana dah. Take manosh ya fara magana yana cewa wlh ibrahim idan ka shiga hannuna zakasha wuya,ni kake yiwa haka ko,wlh to maryam zatasha wuya aguna tunda ni kake wahalarwa,ibrahim dai baya ko sauraronshi karatu kawai yakeyi yayinda maryam ta tsaya dayin kukanta suna mamaki ita da marwan cewa dama manosh yana da aljanune kenan? Sallamar dad da mum ne ya juyo da maryam da marwan,shi dai yah ibrahim karatu kawai yakeyi yayinda manosh yaketa surutai. Maryam ta sunkuya k'asa ta gaishesu kanta a sunkuye suka amsa dad ya nufi gunsu manosh,ita kuwa mum mamakine ya shikata da abinda ta gani,yau manosh d'antane da aljanu? daidai nan manosh yace kayi hakuri ibrahim zanyi magana wlh zanyi magana ka dena k'onani dan naga bakada imani ko kad'an,ibrahim yace kai kana da imanine,me manosh yayi maka haka kake k'okarin kashe matarsa? Yace nifa ka dena dangantani da naniji ni macece,ibrahim yace macece ke? Tace eh tunda na fara ganin manosh naji ina sonshi saboda kyawunsa yamin,toh tun a wannan lokacin na shiga tsakaninsa da duk wata macen dake fad'in duniyannan wanda bazaiji mace tamishibama bare har yace yana sonta,dukda dai baya wasa da ibadanshi amma senayi nasara akanshi,se rana d'aya ya had'u da wannan makiran wai ita maryam,ibrahim yace karki sake ce mata makira domin zan k'ona gabad'aya,tace saboda kana sonta kenan,meyasa ka bari akayi aurensu da manosh d'ina to tunda dai itace yarinyar daka dad'e kana kauna? Kunya sosai ibrahim yaji,yace ki dena min wannan shirmen ki gayamin abinda yasa kika shigo rayuwarsu,tace tunda ya had'u da maryam ya fad'a mata ra'ayinshi akanta,abin yamin zafi nayi iya k'okarina in cutar da maryam d'in kuma amma shegiya na kasa samun nasara akanta,ibrahim yace ta Allah batakiba tafi karfinkine shiyasa. Hhhh tayi dariya tace wlh batafi karfinaba ina tarata ne kawai,nice nake hana manosh kallon ko wace mace,shiyasa nasashi tsanan kallo,duk wata mace da zata dinga kallonshi tise nasa tsanan hakan agareshi,itama maryam d'in batajine ai amma soda yawa ina gaya mata cewa bana son kallon da takemin amma taqi,tunda akayi auren banbar manosh yaje kusa da maryamba,duk lokacin dayayi yunk'urin zuwa se'in rikitashi inyita bashi wahala,sena tabbata yaji jiki sannan nake barinsa idan ya farka da asuba kuma garau yake se kuma wata daren,dan bana barin yazo d'akinta sam itace take zuwa gaisheshi da safe,shine yau ta ibi kafafunta taje gunshi daidai lokacin da nake bashi wahala,yayi iyakar kokarin yaga ya hanata karasowa inda yake,amma dayake ita d'in mai taurin kaine sedata k'araso dan taga halin da yake ciki,shine na shike jikinsa nake son kasheta domin in rabata dashi.. Jikin kowa a palon yayi sanyi tare dajin mamakin abinda aljanan take cewa. Ibrahim yace to ina gargad'inki daki fita daga jikinsa kona k'onaki,tace wlh bazan fita ibrahim ina tausayinka wlh,yace baki fitabako,nan yaci gaba da karatu se ihu takeyi tana cewa kayi hakuri wlh zan
Chapter 27 · 0% Book details