Sashe 17
Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sunban abinci amma bazan iya cibane ka gaida mama kuma dan Allah karka kira numbern nan domin na d'aya daga cikinsune ya taimakamin idan ka kira suka gane zasu kasheshi. Hankalin mahaifinta a tashe yace shikenan maryam na fahimceki amma dan Allah ki daure kici abinda suka baki kodan lfyarki,to baba ya mama take,lfy lau karki damu damu maryam ki kula da kanki,insha Allah zaki dawo garemu da izinin Allah,Allah ya amshi addu'ar mahaifina na gode....bata k'arasa maganarba ta katse saboda kuka daya ci karfinta. Mahaifin maryam hankalinsa a tashe ya kira manosh ya gaya mishi komai,manosh yace karka damu baba insha Allah zata dawo kudai tayamu da addu'a. Shi kuwa bawan Allah kallon maryam yakeyi tare dajin tausayinta ya bud'e ledanshi ya d'auko *maltina da biskits* d'aya ya bata ta karb'a tare dayin godiya,yace bakomai ki koma inda kike dan nasan sun kusa dawowa zanyi iya k'okarina dan in taimakeki ki dena damuwa kinji? To nagode sannan ta koma taje ta zauna tare da bud'e malt d'in da biskits tana sha. Wayarta ta bud'e sega texs d'in manosh dana miher,na miher ta fara bud'ewa inda taga hoton manosh sanye da maroon jaket,ita kanta maryam tasan manosh ya shiga wani hali daga ganin hoton nashi,sannan ta karanta texs nata kamar haka _slm 2u my aunt_ _bansan mezance mikiba aunt,amma ina cikin damuwa sosai musamman yadda naga bro manosh ya zama kamar bashiba dan rashinki_. _Aunt munanan munata addu'a Allah ya d'auraki akansu,kinga dai yadda bro nah ya zama wlh tun jiya baici komaiba har yabar gida yanzu_. _ina sonki wifeynmu,pls koda empty rexs ne ki aiko min dan inji sanyi a raina_. Yours miher.... Koda maryam ta karanta setaji kwalla ya zuba mata,nan ta tura mata da _thankyou so much sis,nagode sosai da kulawarki,kuma nayi farin cikin ganin pic d'in peach,dan yasani farinciki sosai wlh_. *nagode* Koda taga texs d'in manosh batayi reply ba se kawai ta kirashi. Katsewa yayi ya kirata ta d'auka tare da cewa *captain*, sanyi yaji har cikin ranshi yace yes apple a wani hali kike yanzu? Karka damu ina halin lfy,sedai nayi fushi dakai,meyasa mena miki apple? Saboda kabar cikinka da yunwa rabonka da abinci tun breakfast d'in safe meyasa hakan peach? Am sorry apple amma kema ai bakici komaiba,eh amma yanzu haka ina shan malt da biskits,naga pic naka yanzu miher ta turo min peach a jiya kawai amma ka canja. Yadda yaji muryanta kamar zatayi kuka yacewa sojan da yake driving tsaya anan ka karb'o min malt da biskits,sannan yace "apple am goying to eat now okey" pls banaso kisa damuwa aranki muna hanyan bauchi kinji? Murmushi tayi tace "thankyou peach" cikin sanyin murya. Sunanta ya kira a hankali *aunt*, cikin muryan kuka tace uhmm,yace pls stop it apple i will soon come to u okey? Har yanzu kukan takeyi "tace okey i have to peach byee... Bayan ta katse wayanne ya had'iye tausayinta a wuyanshi daidai lokacin aka kawo malt da biskit d'in ya bud'e ya fara sha,bayan ya gamane ya karb'i driving d'in gudu yakeyi kamar zai tashi sama.. Can kuwa koda maryam ta ajiye wayan da sairi ta kashe ta mayar pant d'inta dan taji zuwan mota. Saddam ne tare da sauran abokanshi 3 suka dawo,wannan d'ayan da suka bari yana kwance ya mik'e yare da cewa ya kuka dad'e ne haka? Saddam yace wlh bari kawai,ta tashi kuwa,eh ta tashi tayi sallah,saddam yace gaskyafa ni a matse nake wlh dan haka kawai zan sauke gajiyata akanta wlh,d'ayan yace haba saddam karkayi haka pls da safiyannan idanma hakane ai gara ka bari se dare kai kanka zakafi jin nishani idan duhu yayi. Saddam yace hakanefa,to gaskya dole na koma cikin gari in nemo wata dan wlh a matse sosai nake kasan abunka da sabo,yana kaiwa nan yaje ya duba maryam tana rakub'e a gefe tana kuka. Dariya sosai saddam yayi yace garama ki dena wannan kukan domin anjuma zakiyi wanda ya fishi sauti hhhhhhhh Hankalin maryam ya sake tashi domin taji hiransu. Abinci wani ya kawo mata ya e gashi kici ko fine girl,ko kallonshi batayiba ya ajiue ya k'ara gaba. Tana jin motarsu ya tashi ya tafi ta lek'o taga duk sun tafi seshi wannan bawan Allah. Wayarta ta kunna ta nemi layin manosh amma sam baya shiga,ta tabbatar da suna hanyane dan haka taje tayi alwala tare dayin sallan walaha tayi addu'oi sosai sannan ta sake gwada numbern manosh har yanzu dai shuru yak'i shiga,haka ta koma gefe tana zaune tanata karatun qur'an a cikin zuciyanta har azahar tayi. Maryam tanayin alwala yazo yace amma ki gayamin sunan k'awayenki mana,tace lfy? Yace lfy lau,nan dai ta dinga kiransu harta gama yace babu wasu da kike tunanin sun tsaneki? Tace gaskya babu,yace to shikenan jeki kiyi sallah. Bayan ta idarne seta bud'e wayanta cikin ikon Allah call d'in manosh ya shigo,da sauri ta d'auka tace hello,yace peach kina dai lfy ko? Tace lfy lau manosh kuna ina,pls kazo da sauri domin suna da niyan aikata wani abu a kaina pls..karki damu apple inanan a inda kike yanzu zanzo gareki,mik'ewa tayi da sauri tare da jujjuyawa tana kallon jejin tace ina kake peach?... Wayan hannunta ya karb'a tare da kashe wayar gabad'aya yana binta tana komawa da baya tana cewa dan Allah kayi hakuri. Ran saddam a b'ace yace wato dama da waya a hannunki ko,to wlh bazaki b'ata min aikiba sedai in kasheki in kashe banza. Bindiga ya d'au zai harb'eta d'aya mutumin yace haba saddam kar kayi haka mana mace zaka kashe kuma k'aramar yarinya,kawai muyi gaggawan barin nan d'in shine mafita,domin yarinyar data saka aikin itace take baiwa masu binciken address d'in inda muke dan a kamaka ka fita daga rayuwarta for good. Kan saddam ya d'aure sosai yace kana nufin *LUBNA AHMAD* tana min wasa da hankali ,yace kwarai kuwa. Mamaki ya cika maryam ta nanata sunan a cikin ranta *lubna ahmad*? Kawai seta d'iba da gudu ta barsu atunaninta ai su manosh sun iso inda take. Bindiga saddam ya d'aga tare da harbinta ai kuwa seya sameta a saman hannunta kusa da kafad'arta,ihu sosai maryam ta saka tareda fad'uwa k'asa tana kuka. Saddam zai kara mata se d'ayan ya bige bindigan yace meyasa hakane saddam wai kasheta zakayine? Sauran ukun ne sukazo da mota sukace kuzo mu sampe sojoji sunji k'aran bindiga zasuzo kuma,d'ayan yace bari in d'auko yarinyar dan bazamu barta a hakaba ai. Da gudu saddam yahau mottafi suka tafi suka barshi,gashi sam baiga maryam a inda ta fad'iba kamar wanda ta b'ace. Yanata tsaidasu saddam amma sam sunk'i tsayawa sema harbinsa dasukayi a k'afa ta yadda bazai iya guduba. Ai kuwa segasu manosh da gudu ya k'araso yana cewa apple, apple na iso ina kike? Kan mutumin ya nufa tare da d'agoshi yace ina maryam! Take mutumin ya fara b'ari dan yasan shikenan kashinsa ya bushe tunda ya shiga hannun *sojoji*, yace *sir* wlh ban saniba acan ta fad'i nima ita nake nema... [7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by sad-nas & Hama gee muh'd *dedicated 2 Adon gari group* 41-42 Hajiya khadija ce zaune agidansu maryam tanata kuka,maman maryam se hak'uri take bata,tace yanzu fisabilillahi me maryam tayi haka dahar za'a d'auketa a rabata da iyayenta,se kuma ta sake fashewa da kuka mamace taketa bata hak'uri. Auntyn yara ta dubi tsohon dade rik'e da hannunta yana tab'a inda aka harb'etan da hannayensa,cikin ikon Allah sam bataji zafiba. Se alokacin da take kallon tsohonne seta tuna cewa wannan shine wannana tsoho mai farfad'iyan data tab'a taimakawa lokacin daya fad'i akan titi rananne farkon had'uwanta da *peach* shiyasa bata bance fiskanshiba sam. Murmushi tayi tace baba,yace na'an maryam kin ganeni ashe,tace sosaima kuwa meya kawoka nan bab ya jikinka? Murmushi yayi yace jiki da sauk'i maryam tun bayan rabuwana dake na taimakawa mutane hud'u yanzu kece ta biyar,tace eyyah baba Allah ya saka da alkhairi,dama a nan jihar bauchi kakene? A'a a jihar adamawa nake ca *hong* ayyah baba a hong kake dama toya akayi kazo nan? Maryam saboda ke nazo danaga kina cikin damuwa kuma dama nace kece mutum ta biyar dazan taimakawa shiyasa nazo. Har zatayi magana ya katseta da cewa maryam ki saurari abinda zan gayamiki da kyau,tace to baba ina jinka amma akwai wanda ya kamata mu had'u dashi nasan kuma sun iso yanzu gashi sun karb'e wayana nasan zaiyita nemana baba. Yaga dai ta damu sosai seyace karki damu zan kaiki har inda suke kiban hankalinki anan maryam,tace to baba ina jinka yare da kallon hannunta daya d'aure mata bayan wasu abubuwa dayayi wanda basan meneneba. Baba ya kalli maryam yace nasan zaki gayawa mutane cewa *lubna ce* tasa akayi miki haka ko? Tace eh baba,yace to karki gayawa kowa maryam,cikin mamaki tace meyasa amma dolene in gayawa iyayena ai,baba yace harta iyayennaki kada ki gaya musu komai kuma bana so ki tabbayeni dalili indai har kin yadda dani kinsan bazan cutar dakeba to rashin gayawa kowa shine afi akhairi a gareki maryam. Mamaki sosai ya baiyana a fiskar maryam tace to baba idan ban fad'a an d'auki matakiba ai zata sake bin wata hanyan,yace bazata sakeba maryam maganar gaskya niba mutum bane kamar ke maryam ni alja....bai k'arasaba maryam ta tsorata sosai tare da mik'ewa tana komawa dabaya dukda dai tasan batasan kota inda zatabiba. Baba ya mik'e yace maryam karkiji tsorona ki d'aukeni kamar kina tare da mahaifinkine,dan Allah karki sanar da kowa cewa lubna ce ta miki haka kigayawa kowa cewa su saddam ne,sannan yanzu haka bawan Allah can yana can hannu sojojin zasu gana kece zaki iya dakatar dasu tawajen gayamusu cewa shi bayida hannu taimakonki yake da niyanyi shine suka miki rauni kinji maryam? Cikin rawan jiki dama tunda taji shiba mutum bane taketa add'ua,setace to baba dan Allah inaso in koma gida,yace ba gidaba maryam karki rud'e ki nitsu kinji,kibi wannan hanyan gabanki zaki samesu nina tafi. Yana kaiwa nan ya b'ace,gudu maryam tasa tare da kiran sunan manosh...! Kamar daga sama manosh yaji muryanta ta gefensu da sauri ya juya ya nufin gun da gudu yana apple, "where are you?" Can ya hangota tanata gudu tana juya bayanta har suka iso gun juna. Kallon juna suka tsayayi yayinda take ta waige waige,manosh ya lura da cewa bata cikin hayyacinta sam.