← Book details Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 45

Sashe 29

Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

maganin sannan suka kwanta bacci. 11:30am suka farka inda ya wuce yayi musu wanka suka shirya sanna ya had'a musu tea da bread ta soya musu egg suka sha tana jin kunyanshi sosai. Shi kanshi ya lura da haka bayan sun gama ya d'auketa se d'akinshi can suka koma suka kwanta yana mata hira mai dad'i ita kuwa se dariya takeyi cikin k'ank'anin lokacin ta sake dashi sosai sukaci gaba da soyayyarsu. Mum ce ta kira maryam suka gaisa take tambayarta babu wata matsala dai ko,maryam tace bakomai wlh,tace to shikenan Allah ya muku albarka tace ameen tare da kallon manosh tana dariya. Manosh da friends nashi suka shirya sukaje yiwa surukansu gidiyan aure kamar yadda akeyi,sannan ya bada kud'i sosai dan a k'ara fad'ad'a masallacin unguwansu ya kuma bada kud'i a gyara musu gidan. Godiya sosai maryam tayi tare sadu zahida dan duk sun yiwa iyayensu hidima sosai. Ya ibrahim kuwa girma dad d'in manosh ya k'ara mishi a companinsa dake kaduna wanda aka bashi asistan director a gurin. Kud'i sosai yake samu cikin k'ank'anin lokaci ya sayi mota EODbarka na musam maryam da rash sukaje sukayi mishi,murna sosai mama tayi da ganin yadda maryam ta k'ara kyau, itama maryam dad'i taji sosai da ganin yadda aka gyra musu gidansu,rash ta shigo tana tayi musu hotuna,inda maryam take sanye da green atamfa tasha ado tare da coffee bag a hannunta. Da yamma mazajensu sukazo d'aukansu, inda suke koyawa matansu driving,sannan result ya fito duk aka sasu a FUTY YOLA inda dukkansu suke level one. Hmmm sosayya sosai suke zubawa junansu,inda duk suke d'auke da ciki amma na marya dabanne dan wahala sosai takesha. Lubna kuwa taga ba sarki se Allah dan haka tatsai da zuciyanta kawai agun yah ibrahim musamman lokacin da bro marwan ya kirata yace lallai ta cire son manosh a ranta dan manosh baya ganin kowa se maryam,sannan yace mata ibrahim mutumin kirkine ga addini wanda duk wani uba ko yaya zaiso ace 'yarsa ko k'anwansa ta auri miji irin yah ibrahim. Hakanne yasa lubna saduda tabashi dukkan soyayyarta,inda suke soyayyarsu mai tsafta sosai. Ciwon maryam se gaba gaba yakeyi,abun harya fara damun kowa,tunba yah ibrahim da iyayen manosh bare sunsan abinda shukra tace,amma dukda hakan se suka barshi akan laulayin cikine,hakadai taketa fama ga laulayi ga zuwa makaranta ga kuma kula da peach. Hajiya hadiza mahaifiyar lubna da kuma hajiya iya kullum idan suka had'u banda kuka da nadama babu abinda sukeyi. ********* Kwanci tashi su maryam har sunyi hutu,se abin yad'an mata sauki kad'an. Mum da mamanta kusan kullum suna hanya zuwa dubata,kuma sam har yau yah ibrahim bai gayawa kowa abinda ya faru,iya tsakaninsu kawai sukabar zance. Cikin maryam yafi nasu rash girma da kuma yawan watanni,ranan tana yankawa manosh fruit kawai seta zube a k'asa,dab kuwa lokacin manosh yazo gida,ai da sauri ya d'auketa se hospital d'insu muh'd, tun azahar akace musu haihuwace amma har magriba tanata fama. Hankalin mama da hajiya iya ya tashi sosai dama tunda manosh ya kira baba yace ga maryam sunzo haihuwa se yah ibrahim ya kaisu hospital d'in. Addu'a maryam taketa samu kota ina,mama kuka kuka takeyi dan bazata tab'a mance haihuwan maryam ba wanda bata cikin hayyacintama ta haifi maryam d'in. Hajiya iyace taketa kuka tana rarrashi mama,maryam bata haihuba har 2 na dare,anan akace jinin jikinta yayi kad'an dole asa mata wani,yah ibrahim kamar zaice a d'ibi nashi dayake yanaba mutane sosai jininshi. Amma seyayi shuru manosh ne yabada nashi aka sama mata. Ana kiran sallan asuba maryam ta haihu amma sam bata iya gane kosu waye akanta. Kukan bby ne yasa kowa yasan maryam ta haihu,dan manosh yaso ya kwana a hospital d'in amma dan kunyan su mama yasa ya tafi gida sam ya kasa bacci 4am cib yazo hospital d'in yana dawowa daga masallaci yaji kukan bby,hamdala yayi tare dajin farin ciki aransahi. Mata biyune suke kula da bbyn, d'aya ta fito tace dasu maryam ta sauka lfy an sami 'yan biyu. Manosh ya kasa b'oye murnanshi yace maryam fa,lfyanta k'alau dai ko,tace eh lfyanta k'alau sedai tasha wahala sosai dan haka tana buk'an hutu yanzuma ruwa nasa mata,hamdala kowa yakeyi muh'd yace bari na shiga na dubata,lokacin an rufeta bbys kuwa an shiryasu tsaf,dama ba kaya d'aya aka rik'oba. Suka fito da yara kyawawa kamar iyayensu,manosh yace zan iya shiga inga maryam,sukace eh kaje,da sauri ya wuce baima kalli jariranba,inda mama da hajiya iya suka k'arb'esu. Manosh yana shiga ya rungumeta tana bacci,muh'd yace kwantar da hankalinka idan ta farka garau zata tashi insha Allah,ina taya baban twins murna,murmushi yayi yace nagode sannan suka fita danta samu bacci sosai. Boy ne da kuma byy kyawawan gaske,manosh da muh'd suka karb'esu tare da murna. Daidai sega yah ibrahim yazo tare dasu mum d'in manosh. Murna sosai akayi kowa se cewa yake masha Allah. Kinya yasa manosh barin gurin ya kira mai shiryawa bbys nashi d'aki yace matata ta haifi wtins mace dana miji dan haka ka shirya gobe sekazo a gyara musu d'aki.yana ajiyewa yayita kiran abokan arziki yana shaida musu haihuwan maryam kowa se tayashi murna yakeyi,kafi 8am hospital ya shiga da friends nasu ga kuma su rash da miher. Gefe d'aya hajiya iya ta koma tanata kuka tare da cewa ohh Allah,meyake shirin faruwane dani,kodai lokaci yayne dazan fasa wannan kwan kowa ya sani.. [7:14am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by sad-nas
Chapter 29 · 0% Book details