Sashe 1
Auntyn Yara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Root Entry WordDocument 0Table Data [7:07am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: BISMILLAHIR RAHMANUR RAHEEM... AUNTY'N YARA Written by Sad-Nas & Hama gee muh'd 1-2 Had'ad'd'un motocine guda uku ne suke wucewa 406 ne a gaba,se prado a tsakiya, sannan benz a karshe suna tfy a titin GIREI local government. Daga nesa kuwa wani tsohone kwance akan titi yanata birgima,sega wata budurwa tana rik'e da kwanon abinci da kuma ruwa mai sanyi tana tfy a gefen titi se idonta yakai gun wannan tsohon daya fad'in. "Da sauri ta ajiye abinci tayi gun wannan tsohon da bisimillah sannan ta d'agoshi tana cewa sannu baba lfy? Meke damunka? Ita kanta tasan bazata samu amsar tambayanta daga gareshiba gashi babu yadda zatayi seta hango motocinnan suna zuwa. Kwantar da tsohon tayi ta mik'e tare da tsayawa akan titi tanata k'ok'arin tsaida motocin amma sam basu da niyan tsayawa. Ganin halin da tsohon yake cikine setak'i matsawa akan titin dole dai 406 d'innan ya tsaya ganin budurwan tak'i kaucewa. Da saurinta ta k'araso gun motan tanata buga glass, d'aya daga ciki ya sauke glass d'in gaba yace ke wace irin...bata bari ya k'arasaba tace dan Allah malam fito ka taimakamin wancan tsohon ya fad'i bansan meke damunshiba. Suka kalli junansu sukace bazamu iyaba, mamaki ya cikata seta rabu dasu taje gun pradon tanata buga glass d'in gaba dana baya. Glass d'in baya aka sauke nidai SAD-NAS idanu na bud'e da kyau dan ganin wani had'ad'd'en saurayi a ciki yana sanye da suit fari tas k'amshine kawai yake tashi. Budurwan ta had'iyi yawu sannan tace bawan Allah pls ka taimaka min wancan tsohon yana neman taimako sannan ni kad'ai bazan iya d'agashi daga kan titiba shiyasa na tsai daku. Cikin mamaki seya cire glas d'in idonshi ya ajiye a gefensa sannan ya bud'e mota ya fito batare daya ce mata komai seyayi mata nuni da hannunshi alaman muje. Da sauri ta wuce gaba yana biye da ita har suka k'arasa gun tsohon,budurwan tace toya ka tsaya kuma d'agashi ka maidashi gefe mana, saurayin yana kallonta har cikin ido yayi magana a hankali yace to ai ke nake jira mu d'agashi tare. Mamaki ya kamata tace yanzu kai a matsayinka NAMIJI bazaka iya d'agashiba harse na taimaka maka? Kai kawai ya d'aga mata alamar EH. Ba musu ta kama tsohon suka d'agashi zuwa gefen titi, saurayin ya lura da cewa farfad'iyace take damun wannan tsoho, dan haka ya koma gun 406 ya karb'i inhela sannan ya dawo ya taimakawa tsohon cikin ikon Allah tsohon ya dawo hayyacinsa sannan saurayin yace sannu baba Allah ya baka lfy sannan ya juya ya koma motarshi. Budurwan tace sannu baba ina zuwa kaji, sannan ta mik'e taje gun pradon ta sake buga glass d'in a hankali lokacin motar tana k'ok'arin tashi. Saurayin ya sake sauke glass tare da cewa me kuma? Budurwan tana murmushi tace nagode da taimakonka. Saurayin yace me alakarki dashi? Tace MUSULUNCI bayan wannan bakomai, saurayin yace dama "you don even know him? Budurwan tace yeah na taimaka mishine saboda yana buk'atan taimakon dan haka nagode Allah ya kiyaye hanya, harta juya ta fara tfy seyace 'yan mata. Na'am tace dashi tare da dawowa gun ta tsaya, yasa glass d'inshi yace nima nagode da kikasa na samu wannan ladan. Budurwan tace karkamin godiya bawan Allah amaimakon godiyan da zaka min, inaso idan ka sami dama toka taimaki mutum UKU kuma suma kace musu su taimaki mutane UKU inaga K'ASARMU zataci gaba tayin hakan se'anjima sannan ta tafi. Kalaman yarinyar sun burgeshi sosai yace da driver'n shi "lets go" nan driver yayi hon se 406 d'in tayi gaba sannan suma suka wuce saurayin yanata bin budurwan da kallo se karkad'ewa tsohon jiki takeyi sannan ta rik'e hannunshi ya mik'e yana cewa nagode sosai yarinya Allah ya miki albarka. Budurwan tace ameen baba, amma banason godiyan nafiso idan ka samu dama a rayuwarka toka taimaki mutum UKU kuma suma kace musu su taimakawa mutane UKU. Tsohon yace to shikena yarinya ya sunanki? Tace sunana MARYAM amma amfi sanina da AUNTY'N YARA,seta d'auki abincinta ta tafi yanata binta da kallo. Shi kuwa wannan saurayin kalaman MARYAM kawai yaketa mishi yawo a kwakwalwanshi. Suna cikin tfyane seya hango wasu mutane UKU suna bin wata yarinya a guje se kuka takeyi. Yace da driver tsaya, bayan driver ya tsayane seya cire farin suit nashi da glass d'insa ya fita da sauri ya fara bin bayan mutanennan da gudu harya cafko biyu. Jin hakan yasa yarinyar tsayawa tana cewa bawan Allah ka taimakamin wai fyad'e zasumin. Duka ya fara musu kamar ba gobe suna bashi hakuri, yace baku da tausayi sam,yanzu ku zakuso ayiwa k'anwarku fyad'e? Sukace a'a kayi hakuri bazamu sakeba, yace ina fata zaku gyara halinku inba hakaba wataran se anyiwa k'annenku koma 'ya'yan cikinku. Jikinsu yayi sanyi sukace kayi hakuri kema kiyi hakuri daga yau mun dena kuma mungode. Saurayin yace karkumin godiya,amaimakon godiyar da zakumin inaso arayuwa idan kun samu dama toku taimaki mutane UKU2 suma kuma kucemusu su taimakawa wasu mutane UKUN ya juya ya kalli yarinyar yace harda kema sannan ya tafi sunata binshi da kallo sukacewa yarinyar muje zamu rakaki har gida, dad'i taji sannan suka tafi. Shi kuwa ya koma mota yasha ruwan FARO mai sanyi sannan ya goge takalminshi tare dasa suit da glass nashi sannan driver yaja mota se gida. Suna isa saurayin ya fito ya shiga ciki. Wata kyakkyawar budurwace ta fito daga d'aki tana sanye da wandon jeans fari da kuma black top mai hannu d'aya kanta ba d'ankwali ta baza gashinta tana danna TAP ahannunta daga ganinta kasan k'anwar wannan saurayinne dan kamannin harya b'aci. Murmushi takeyi tare da cewa "The Prince! "The Captain!! "And d Bro MANOSH!!! Daga ina ka fito hakane dukka dawo a gajiye bro MANOSH? Suit d'inshi yake cirewa yanacewa "pls not now MIHER" Bari na watsa ruwa se inzo kinji? Alright tace dashi sannan ya wuce side d'inshi ita kuwa MIHER ta zauna tanata buga game d'inta. Sallama taji, ta masa batare data kalli kosu wayeba, tap d'in hannunta taji an karb'e seta d'ago kai da murna sosai tace "The 6 Emms" (M) yaushe kuka shigo k'asar without alartn me? dariya sukayi mata amma banda d'aya daga cikinsu, MIHER tace bro MARWAN miskilancin ya tashi kenan? Marwan yace ke ina MANOSH, tace yana ciki,duk suka wuce sukabar MAJID yana rik'e da TAP d'in yace bana hanaki irirn wannan shigarba? Tace am sorry luv aidan ina gidane kuma bansan kun dawoba wlh amma promise daga yau bazan sakeba tana murmushi. Shima murmushin yayi yace to shikenan kije kisa himar ina jiranki a side d'in PRICE, ok luv ina zuwa me za'a kawo muku? Karki damu a k'oshe muke ruwa kawai muke buk'ata kuma zamu samu agun bro naki dan haka ki huta my luv yana mata murmushi sannan ya bata TAP d'in ya wuce itama ta shige ciki dansa hima... [7:07am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: AUNTY'N YARA Written by Sad-Nas & Hama gee muh'd 3-4 Palon manosh suka wuce kai tsaye suka baje akan kujerunsa masu kyau ga laushi. Muhammad ya kunna musu TV tare da d'ansa volume ta yadda manosh zaisan akwai mutane a palon,ball suke kallo suna hira. Manosh ya fito sanye da shets fara da kuma bak'in jeans,mamakine ya kamashi su kiwa dariya sukasa tare da cewa the prince captain manosh. Karasawa yayi ya zauna kusada muhsin da marwan yace gaskya bakuda kirki wlh,ashe kuna hanya shine har marwan kana cemin wayankane ba charg,marwan yai mirmushi yace muhsin ne yace karmu gaya maka,muhsin yace haba dude haka zakamin kuma,dariya sukasa dukkansu manosh yace to ina tsarabana naganku empty hand. Majid yace babu ya ibada ya hanya kawai se tambayan tsaraba,gaskya bakada kirki,manosh yace wannan tambayan ai mata kad'ai akeyiwa dan sune sakaltattu amma kana namiji dan kaje UMRAH harse anyi maka wani sannu,muhammad yace sosai kuwa ai haka ya dace,manosh yace toku rik'e tsarabanku indai hakane nasan marwan zai bani. Marwan yace ni ibada kawai naje ba sayan tsaraba ba my friend,muhsin ya mik'e ya d'auko ruwan sanyi yasha sannan yace to nidai zanje hira,kuda bakuda kowa sekuyita hiranku da kallon ball,harzai wuce manosh ya janyoshi yace wlh baka isaba nima na samu matar aure had'add'iya kuwa tamafi MIHER d'inka dan haka ka dena wani cika baki,ba majid kad'aiba dukkansu suka juya suna mishi kallon mamaki,domin duk cikinsu manosh ne kawai tun tashinsu bai tab'a ganin wata 'ya mace yace yana soba koda wasa. Muhsin yace "wow dude" gaskya zanso inga mai wannan SA'AN yau kaine da budurwa kodai wasa kakeyi? Manosh ya bisu da kallo dan dukkansu idonsu a kanshi yake suna jiran jin mezaice,yace wlh yauna had'u da wata yarinya bafulatana nitsatsiya gata tason taimakon wanda bata saniba sedai k'aramace,amma wlh ta burgeni sosai kuma kunsan wani abu dayasa na damu da ita "we luk alike dudes" zanso ku ganta she's so sweet. Majid yace harka tab'ata kenan,bugun wasa yakaiwa majid yace kai d'an iskanefa a hakanma wai k'anwata kake so shine kake min wannan maganan,majid yace to ai naji kace she's so sweet ne shine ban kane ba,manosh yace eh ina nufin voice nata yadda kasan mutum in yana mura kasan muryanshi yana canjawa,to amma nata yayi dad'i sosai kuma ba muran takeyiba natural voice nata kenan,bari dai in tak'aice muku kunsan dai muryan RANI dabanyake a cikin sauran matan indians da suke FILM,to haka dai itama yarinyan amma nata yafi na RANI dad'i idan tana magana bazakaso ta gamaba wlh nd.....marwan yace enoght me sunanta? Manosh yace nidai bansan sunantaba but zan dinga kiranta da MY APPLE. Ajiyar zuciya suka sauk'e muhammad yace gaskya zanso in ganta ko zan samu k'awarta nima,manosh yace ai wannan ne nakeso in samamishi k'awarta dan naga ya kusa ya tsufa baiti aureba,marwan yayi murmushi yace kai baka tsufaba seni,muhsin yace gara dai kam ka taimakawa marwan dan tunda FADILA ta rasu ta barshi gabad'aya bana gane mishi. Majid yace kuka sani kozai bitane ku kyaleshi kawai,duka marwan zaikawa majid se yayi sauri wucewa gun k'ofa yana cewa to ai gaskyane nidai na tafi gun luv d'ina prince ina tayaka murna dolene muje nemo soyayyar APPLE namu,manosh yace gaskya na baka k'anwata koba'ayi tambayana nariga dana baka ita. Dariya suka sa sannan majid ya tifa gun MIHER,su kuwa