← Book details Amfanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 46

Sashe 46

Amfanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai da suka samu kebewa yake tambayar mum zarah fa? bata gaya masa me ya faru ba kam amma ta sanar da shi tana shirin hidiman ta itama kuma tace zata zo yace ok.. Aran shi sai yaji bai damu ba cos a halin yanzu so yake hankalin sa ya kwanta sosai

Ranar da ya tashi sosai suhan ma bata samu ganin sa ba sai da aka gama shirya shi tsaf da special uniforms amma sai taga wannnan ba white bace asalin khaki ce amma da banbance sosai da na sojoji...ko wani contry sun sa amma badge ke banbance su....

ita da mum ma shirya su na musamman akayi don har anyi odering white longeries desiners da companies a dubai wanda ko wa zai sa kamar anko ne amma ya hadu sosai..

Da shike babban events ne da ya kunshi world class learders da safe aka yi...
aka kira duka captain din da suka bada qudumawar su aka basu awards da karin girman su...

Sai a karshe aka kira shi
Bayan bayanai na yabo da ban grima aka maida masa igiyoyin mahaifin sa yanzu ya amsa suna fn admiral abdl majeed mahmud....
mum sai da tayi hawaye ...musamman lokacin da ake dressing dinsa akan stage yana daukar oath sai tana ganin kamar mijin ta ne ya dawo cikin ruhin dan su..

Ba bata lokaci aka soma watsa hotuna da labarai akan kafafun yada zumun ta ...

its a very bright and beautiful day ita kanta suhan sai da tasan ta kai wani level arayuwa cos yau ta soma yin ido hudu da mutanen da tasan in ba atv ba har ta mutu bazata ji kamshin su ba...

she looks stunning so kowa yana haba haba da ita ana masa san barka cos sai yanzu dacewar su yake dada fitowa fili.....
kalar hotunan da aka sharing wajen ba iya ka da wanda suna sane da wanda basu sane ...har aka ci taro ya watse..

Wajajen 4 pm na yamma mum ta tarkata zata dawo nigeria ta kyale su anan don yanzun kunya suke bata sosai...

bayan tafiyar mum
Ranar ma haka suka raya daren su cikin kaunar da kewar juna..

Washe gari a ka soma hidiman zarah a london
Bata samu lokacin kiran shi ko kadan don kanta sosai yayi zafi already su faiza sun gama kallon news sun ga meke gudana so take ko na dan 5 minute su sami zama ta shafa mata..

amma ena hakan baiyuwa ba don mumy rabiatu tana nan wajen sai yadda tace da zarah zata jiya ta hana ta sakat...

Anan ma wajen hidiman zarah ta ci kyau dama ba dama wajen kware adaka anyi mata yadda take so an bata girma an nuna mata ita wata ce sai dai duk abunda take yi ranta a cunkushe yake ta so ace majeed na tare da ita da abun zai fi haka ....

Ace mijin ta sananne kuma aganshi kyakkwa tare da ita amma is not happening sai ta daure aka kammala komai cikin nishadi da friends...

Dan karamaar dinner da ake yi ana refreshment anan gulma ya soma samun waje...
saboda duk wanda ya bude instagram sai yayi arba da hot pics dinsu altho wasu tags ne kawai mutane ke sharing waje daban daban...
tuni wanda suka san ta suka soma cece kuce ana nuna ta da dan yatsa

Zarah dake lura sai jikin ta ya bata somthing is ongoing amma sai ta basar ..

hajiya anty mariya ta zo mata congarts suka dan rungume juna..tace mata Allah ya bada ikon riko
Ena maman naki ni zan wuce.

Ta dan duba bata gan ta ba tace maybe tayi wani wajen..anty mariya ta sake duban ta tace and what about your man ..nifa na zo hidiman ki yafi sau biu banga majeed ba atleast this is your big day he should be here to support ta sauke ajiyan zuciya tace antu majeed baida lpya ne shiyas abai zo ba...ta tabe baki tace i seeee...

amma ai yau naga kamar shima yana hidima wani wajen daban...wani rass kan ta ya sara tace what nooo sai ta shiga bada labarin abunda ya same shi agurgije Anty bata yi magana ba ta zaro
Waya ta ce look..

.ta mika mata ta shiga kallon news update da pics kala kala ...wasu zufa na ban mamaki ke keto mata she dont knw what to do murnan samun karin girman majeed zatayo ko kishin ganin sa manne da wata daban ?

Ta ce oohh ai ena hidima ban ma sani ba ..ai gobe zanje na duba sa kawai tayi yake mai daci...anty ta ja hannun ta tace zauna zarah...

Ba musu ta zauna cos shes feeling depressed and confused now ..
.
Anty tace bazan boye miki ba dagangan na zo nan don naji ko da sannun ki hakan ke faruwa....ta dago ta kalle anty wani rin tasan halin ta da wa'azzi but honestly she feels like listening..anty tace
Ke ysushe zaki zame ma mijin ki mata wannan ba kishiyar ki bace? Murya kasa kasa tace itace..

.hmmm good..
Wai akace kukan kurciya jawabi ne...just look around you ki juya mana ki kalle mutanen nan wajen mafi akasar gulman ki suke yi....kin bar mijin ki achan yana sha'anin sa da wata some are even saying baki da power a gida sai awaje wata ke rulling dinsshi..

maganan yayi mata zafi a haukace ta dago tana kallon anty...tana so ta waroro zagi na bacin rai amma sai tayi calming kanta....tace anty ke daina jin wayyannan kanananun magaman banzan...its just a coincednce bana tare da shi shima bai tare da ni ai shi ya daura ni akan nan...
sannan kuma na yanke shawara zanyi 3months leave a gidan batare da nayi wani aiki ba saboda na duba aure na da kyau...anty batayi tsammanin jin haka ba cos tasan ra'ayin zarah akan aure da soyaya

Sai tayi murmushin in a very amusing way tace da kin sama kanki lpya kuwa..

Ni zan tafi da kyar ta iya daurewa ta ce mata ta gode....

Tun da anty ta tafi ta wuce dakin hotel din ta kulle kanta worst part sai gashi ana nuna event din a tv zuciyan ta na hawa na tafasa amma sai da ta gama kallo tass....

Ta soma tambayar kanta meye majeed yake nufi da yarinyar nan? Shine harda kai ta wannan matsayin ita bai neme ta ba wannan wani irin pics ne haka.most he shows so much love and intimacy me hakan yake nufi duk don bana nan ake min wannan cin kashin ta dada firgita ta dauko wayar ta ta shiga instagram tana sake dubawa tsanan suhan ke damunta but why..

ta koma bada kanta answer tace miji na nawa ne nafi karfin n hada da wata kazama matsiyaciya almajira tayi jefa da wayar akasa...

Chan ta shiga huci tana calming kanta ita daya..
Daga bisani tace i cant wait for tomorow zamu je gidan ai ..ni dake ne zamu ga waye mai miji..am back its time to take evrything thats mine...ta fada a zuciye eVent din ma bata samu halin karasa shi ba tayi baccin dole

So tunda asubahin farko ta koma nigeria...

Su majeed kuwa suna nan us suna shan love din su sun gama shiri zau dawo nigeria amma sai ta nace suke su yi ma mahmud ban kwana ...

Suka kai ziyara agirjuje yasmin tana da 7month old baby girl so tunda suka je babyn ta manne wa suhan ita kuwa suhan ta dauke ta a cinya tana mata wasa sai dai ita babyn ta hana ta sakewa tayi magana saboda qamshin baby lotion din tuni taji yana neman cahkuda mata ciki sai yanayin ta ya sauya gaba daya taji cikin ta na hautsinewa...

Wasa wasa har suka bar gidan qamshin baby lotion din bai daina damun ta ba suna isa dakin su sai da ta kwanta na dan lokaci tana kokarin saita kanta don amai take ji sosai mai dauke da azabbaben tashin zuciya gaba daya sai take jin kanta a dagwale....

Hakan ta cize suka kama hanya da zimman take off zuwa nigeria bai san halin da take ciki ba..

*?????????? toh meke damun suhanah baby kuma _??_ argure with ur ancesstors??????*
Chapter 46 · 0% Book details