← Book details Amfanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 46

Sashe 26

Amfanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kowa yayi mamakin wai Ruwaida yar gidan me kwano ce
Kuma matar sa Malama da ta gama shahara a duniya wajen WA azi da temako ce haka

Ummi tace "Ruwaida ni yarana 6 Ismail shine babba sai Anas sai Abida sai Khalifa da
Al amin sai auta Kharajina wanda nake ganin zaku zo sa anni
Alokacin da Wakili ya aureni muna tashi a Niger England muka wuce saboda da ma iyayen sa suna can kuma alokacin bai gama karatun Sa ba yariga Yayan sa Hakuna aure shiyasa Ismail yafi Sa idu da y'ar watanne a London Wakili ya nema min makaranta Sai da na gama secondary dina alokacin shikuma yazama professor har yasa mu aiki a can duk shekara idan muzo Kano Sai naje jejin niger amma Sai tulin k"asa wanda ko gari babu akusa haka zan zube acikin rairayin nayi kukana amma haka wani shekaran ma zan sake zuwa wai ni yau Sai gani da y'ar gidan Kharajina k'anwata da na barta ko shekara 4 batayi ba yar autan mu Allah na gode maka Ismail ayau ba Sai gobe ba nake son ganin Kharaji ta."

Prof. Wakili yayi gyaran murya yaje
ni abinda yafi mani mamaki dama Mudda yaran da ya nuna yace a gidan marayu ya dauko yaran sane sannan faduwar damn yaHakuna yayi a zabe shine sanadi amma takanas yazo mana jaje a lokacin campaign ya Kashe mana dukiya meyawa da sunnan yana bayan mu."

Shiko Ismail cije libe yayi yana tunayin irin azaban da zai bawa boka auta Ya haukata masa k'anwar uwa san nan da sa hannun sa yayan baban shi ya fadi a zabe da sukayi dinbin asara

Baba Idiris yace "a gani na adauko Ita Kharajinan nan yafi sai a hadu da shi Mudda din ayi maganan Ismail kwai Jet amma yana port Harcourt
Kuje da Sa adu da ita Ruwaidan ku daukota mu ganta"

Kharajina tace "Daddy zan bisu Egypt din."

Sau ran yaran ma suka ce nima nima

tSawa Mall ya doka musu yamekawa Anas wayan sa yace "ta gaya maka address din da zamu Sami gidan Doctor Yusura din."

Anas yakarbi wayan zai mek'awa Ruwaida wani irin tsawa Mall ya doka masa yace "cewa nayi ta gaya maka kasa ba kabata ta rike min waya a k'azan taccen hannnun ta ba."
Baba Hakuna yace "haba son ba ahaka kar naji ka kara kiranta k'azanta kowani ya kirata haka zakaji haushi ."

Ummi ko hararan sa tayi

Ruwaida cikin kuka ta fadi address din su da kuma number su

Pro Wakili ne Yace "amma Ruwaida kici gaba da zaman ki anan har agama da case din ku kin ji."

cikin ladabi Ruwaida tace "Abba bani daya bace ina da yan uwa Hamrah da Ayyaram
daga nan ta shashe labarin su Ayya ta gaya musu

sun jinjina abin sosai musam man na Ayya dan Dunoma ba wanda bai san shiba kuma labarin kwace masa dukiya ma ya baza duniya amma ba yanda Ruwaida ta basu labari ba ayanda ake fada da kuma shi kansa Duno da yan jarida sukayi fira dashi cewa yayi dama dukiyar uban gidan sane balaraben saudia kuma yakarbi kayansa

Baba Hakuna yace "na tausayawa labarin ku kuma zan shiga cikin maganan su Ayya din ma suma suzo muzauna tare ita Hamrah da ma ni banki auren ta da. Sa adu ba iyayen sa mata ne suka ki na hakura saboda nasan mata sune gida idan anyi abinda ransu baya so abin baya kyu ita Ayya nasan Barrister Bunima mutumina ne ai zanyi magana akai

San nan kuma na gida kuyi hakuri ayi auren Hamrah da Sa adu wannan alfarma na nema..

da sauri Sahal ya daga ya Kalli Umma yana jiran amsan ta

Umma ta goge kwallan ta tace "shikenan Alhaji Allah yabamu ladan wannan gyara da mukayi na yarda...

tsalle daya Sahal yayi ya rumgume mahaifiyar sa yana murna

Ruwaida tashi tayi ta taka har gaban Umman ta zube ta dafa cinyar ta tana kuka tace "Umma ku yafe min abin da na muku a bank."

Umma tace "ba komai Ruwaida a ya nayin yanda kuka tsinci kanku abinda yafi haka ma zaku iya yi Sai de abinda kikayiwa Baban ki bai yi ba Aishatu."

Ayya Hamrah Barrat da Abdallah ne suka shigo
gaida iyayen sukayi suka sun kuyar da kansu
Daddy Idiris ne yace "munji komai na labarin ku shine muka yanke shawaran zamu nemi Barrister Bunima akan maganan ke Ayya idan zasu Bari dan su ya aureki ayi idan baza su bari ba za mu nema miki wani san nan abinda ki kayiwa Duno baki yi dai dai ba ai ko ba komai ya juya dukiya yana kuma da hakki a kansa kamata yayi ki cire masa hakkin sa"

Ayya "tace Baba dama banyi niyar karba gaba daya ba zan mai da masa tunda ni ba iya juyawa zanyi ba."

"yawwa to Sai maganan ke Hamrah kin yarda zaki tuba bayan kiyi istibrai a daura auren ki da Sa adu."

sunkuyar da kanta Hamrah tayi tana hawayen farin ciki ta kyad'a Kai

Shiko Ismail dora Abdallah yayi kan cinyar sa yana masa tambayayi ko sauraron abinda ake ba yayi

Ummi tace "bani d'an nawa idan ka gama ikon naka."

Ruwaida sunga tattali da kauna zalllah awajen Ummi Kai dama sauran family kowa Yana nan nan dasu

Kharajina ta Kalli Ruwaida tace "sis Wllh fada ake kawai kinfini kyau."

Ruwaida tayi murmurshi tace "ni yanzu ba surutun ba duk naga kowa YA Khalifa da Aunty Abida ban gansu ba."

"Ya Khal yana Germany
Aunty Abeed tana gidan ta a Abuja amma da safe zaki gansu dan Ummi ta musu kiran gaggawa bamu gaya musu a waya ba so muke su ganewa idon su."

Ruwaida tace "to ya maganan auren ki da Sahal.?

"Kharajina tace "caf ai babu ma dama yaya balle yanzu ta aka bashi wannan me iyayin tskiyan ai na hakura ni bana son ganjo ma."

dariya Ruwaida tayi tace "shikenan mun shuta da kishiya."

Kharajina tace "wato kinfi sonta ko nice kishiyar ma ko."

Ruwaida tace "Wllh ina son Hamrah."

Kharajina tace" to shikenan ban janye ba zan aureshin naga ya zakiyi."

Hamrah da fitowan ta Kennan a bathroom taji duk yanda sukayi
da sauri tace "ah ah Wllh sis ni ina son ki nafi sonki ma akan Ruwaida ke zan ba babbar k'awa kice ba Kya son Sahal din nan."
"kaji wayo to sai na soshi
wazai ki guy kaman Yasal

Su Ismail sunje Egypt

basu sha wahalan gano address din ba

Kharajina runmume su Ismail tayi tana kuka
ganin yanda Ummi ta damu suzo ko ta biyosu ne yasa sukayi shirin ta howa a washe garin har da Doc Yusura da Ummusilem da yaran duka

Fadin kuka da farin cikin da Ummi da UMMA sukayi bazai fad'u ba jim kad'a a runmume juna ayi kuka

washe gari aka kira meeting a babban parlour dan asan yanda za a bullowa Mukaddam har da Aminu yana wajen

Amma doctor Yusura ta nemi alfarman dan Allah abari tana da wasu abubuwa da take yi akan yanda komai zai zo da sauki."

Ummi tace "meye abubuwan da kike son kammalewan?

Yusura tace" da farko de abi abun ahankali yanda za asamu nasara dan idan baka iya kama barawo ba shi zai kama ka dan malama ba karaman shukuma bace idan muka bi abin da gagggawa abin bazaiyi ba zata iya bin bokayenta ta juya kwakwalwan Mudda ma amma yanzu nasa wani babban malami ya na karya duk abinda tayi yace Sai a hankali zai karye

sai kuma bana son a tada maganan nan Kharajina da Ummusileem basu haifuba Tunda ciki garesu duk me ciki bata son abin magana idan suka haifu sai ayi komai cikin nusuwa."

Kowa ya yarda da shwaran Yusura

Hashe gari Yusura da Ummusulem suka koma suka bar Umma

Angama maganan auren Ayya da Grema iyayen sa sun amince acewar su dama ya fada musu amma basu yarda ba atuna nin su kodan yana son tane har ansa rana 4

Haka Hamrah ma anje adamawa da k'yar aka shawo kan Kabiru kurma da matar sa suka yafewa Hamrah shima dalilin Sahal da yake suna ganin girman sa sosai
Hamrah ansha kuka da su Ruwaida zasu tafi musammam Abdallah da Barrat mutanenta

Ismail ko gaisuwa ba ya hadasu da Ruwaida ita ma bata isa tun karansa gaisuwa ba dan bata ga wannan fuskan ba

Amma Ummanta kam kamar ita ta haifeshi ko irin sun jima taren nan bini bini Ummati

Yau suna zaune a parlour suna da yawa Sai fira suke ya shigo
wajen Umma yaje yace "Ummati yau fa ki shiryar surukar ki zata zo gaidaki".

washe baki Umma tayi tace "Kai d'ana kace ina da bakuwa Kennan."

Ummi kam ko kallon inda yake batayi ba

da Yamma Sai gashi da wata Wanda za a iya ce mata lah baasa amma de bata dace da shiba
ta fuska bata da lifi dan tana da hanci da magana sosai
amma gajirace gata bak'a k'irin sanye take da zurmemen shijaf dan haka ba me cewa ga yanayi k'iran jikinta kanta asunkuye ta zube ta gaida su Umma ita ko Ummi kyakkyawan kallo daya ta mata ta tabe baki ta juya
Umma ce take ta nan nan da ita har ta tambayeta ya Sunan ta
tace Halima shiko gogan sai dariya yake Yana faman washe baki kamar ba Mall ba

Yace "Umma yar gidan malamai cefa."

Umma tace "ai ko da alaman tarbiya a tare da ita Allah yasan ya alkairi."

" Ameen."
yace

Yamall yana fita Farida kanwar Sahal tace "
wai ni Nafi wai meye ma dam da k'asa ne da sauri Zahra tace "tukuban tsire."

Nafi tace" ah ah ke inuwan kashi yafi kusa da k'asa saboda kajer ta.

wani irin dariya suka sa dukn su
"Kharajina tace "ah ah kujera ne ."

Dariya suka sake yi
Umma da ba gane habai cin nasu tayi ba tace"meye haka ku kuma anya ma kun gaida Auntyn naku."

gaida ita sukayi
Shigowa yayi yace "ke Nafisa rakata part din Umma da Mama ta gaida su."
Jiki na rawa Nafi ta tashi Halima tabi ta
Chapter 26 · 0% Book details