← Book details Amfanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 46

Sashe 20

Amfanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tabawa tace" haba Ruwa dubi yanda jini yake bin jikin ki kice ba ke kika haifu ba idan so kike ki halatta d'an da kika haifa ga uban ki mu amintattun ku zamu iya fashin tar da Hajiya karaji ta rufawa Kai asiri ta karbi dan a matsayin ita ta haifa amma ban da wannan renin hankalin naki ba agaban mu kika haifu gajini yana bin ki kice w.....

Kasa karasawa tayi ganin Umma ta yanke jiki ta fadi
Duk sukayi kanta cilak Tabawa da Harira suka dauki Umma suka fita asbiti

Tabawa tacewa sauran ma aikatan su shiga part din Karaji su gyarani na haifu haka suka zo suka taru duka suna mamaki Tsohuwar cikin su Baba Ladi ita ta yankewa Abdallah cibiya wai nima zata min wanka wani irin tsawa na daka musu duk suka fice akan gado na daura Abdallah na lulubesa da zani Sai sandara kuka yake ni kam na rasa inda kuka yake balle nayi sa ina tunanin abinda yasamu Umma na

Ashe duk wannan abin da akayi Kamal dauka yake a waya yayi video din komai wai sheda

Acan asbiti ma jikin Umma yariki ce tacewa Kamal yakira mata Abba nemi yafiyar sa ita mutuwa zatayi aiko yakira
A handfree yasa wayan

Shima Abba lokacin suna tare da Malama da Hajja shima a handfree yasa dan yaka video call ne yana ganin Karajina kwance a gadon asbiti Sai Tabawa da Harira a gefe suna kuka shima rikicewa yayi

Abba Yana dauka Umma ta fara magana
"Alhaji kayafe min mutuwa zanyi kirjina ciwo kai na zai fashe idona yadena gani."

Tana maganan daya hannun ta dafe da kanta daya da kirjinta

Arikice duk kansu ukku suka ce "lafiya!!!
Dan yanda muryan Umman yake kadai YA isa a gane tana wani Halin

Umma tasake cewa "Ruwaida ta ci amanan tarbiyan malama Ayau Ruwaida ta haifi cikin shege kuma ta danganta d'an Dani tace nice na haifa dan Allah Alhaji kayi hakuri na kawo maka annoba gidan ka da ban haifi ruwaida ba da hakan bai faruba nace su Bari na kasheta zan samu sauki sun hanani na.....

Maganan ya makale tunfashinta duf ya dauke
Dan na mata kinji doc yashiga Yi arikice

Mama Tabawa ta daga hannun ta taji yakoma ta Kai hannuta wajen kunnen Umma Sai ko ta dago tana rusa kuka yanzu shikenan Hajiya Karaji halinki na gari yabiki hakuri ya kwanta dama wayyo ni Hafsatu."

Abba arikice yake cewa "Habibu kada ka kuskura na rasa Khadija kubarta ta kashe Aisha inde zata huce."

Hajja ta karbi wayan ta kashe ta ita kanta Hajja kuka take tana cewa " " Wllh na yarda Ruwaida ce ta haifu naga alamun ciki ajikinta malama ta samin shakku."

malama kam harda suman karya Hajja tazuba mata ruwa ta tashi tana ta kuka da addu oi

Malama ta sake kiran Kamal alokacin shima kukan karyan yake "Kamal da gaske ta rasu?."

"Malama ayi hakuri ta amsa kiran ubangiji kuyi hakuri zam....

Ai bata karasa jiba ta fashe da wani irin kuka

Shiko Abba shiga yayi ya sako riga yace" kutashi mutafi".

AI malama fadawa jikin sa tayi ta Saki kuka
"Wllh Alhaji baza kaje kaga gawan Khadija ba dan hankalin ka zai tashi har Sai ayi mata sutura tunda Allah yacireka aciki kar kakai kanka nasan kafin zuwa gobe anyi sutura kai ma zuciyar ka yadanyi sanyi hukuncin da zakayiwa Ruwaida zaiyi sanyi."

Hajja tayi naam da shawara malama dan haka dakyar suka samu Mukaddam ya yarda ayi suturan Umma da safe tunda chana akwai nisa sai sunsake kwana idan ahaka hada kwananin zasu zama 2 kenan

Awanke aka sace gawan matar da tarasu na mutanen kauye aka basu cin hanci suka bar zancen dan asbitin na Habib ne private ne

Ita kuma Umma Aminu ya dauketa ya fita da ita tafiya yake ba kakkkautawa har jahar yobe ajejin gaidam ya ajiyeta awani kauye ya juyo

Ina zaune aka shigo da gawanda aka kira na Umma ne a gabana ina son budewa na gani amma su Mama Tabawa suka hana da safe akayi sutura tashin hankalin da nashiga ba magana madara nasa aka sayo min nake bawa Abdallah kowa yazo Sai Mama Tabawa ta karanta masa yanda akayi har zuciyar Umma ta tabuga ta mutu

Ahaka har aka sake kwana su ABBA suka sauka inda gidan yasake gwacibewa dan Abba binduga ya fitar zai harbeni Kamal ya kwace

"Kamal kunci amanana Kai da Tarawa da Habib da Aminu kuna gani a gaban ku na rasa Karajina yar amana meyasa baku Bari ta kashe wannan tsineniyar ba Wllh ko kubari na gashe ta ko nima ku rasani in ba haka ba to tafita bana fatan nasake hada ido da ita."

Cikin kuma ina rungume da Abdallah
nace "Abba kar ka yanke hukunci cikin rashin bincike Wllh wannan d'an Umma ce ta haifa k'ani ne agareni ba d'aba Wllh Abba ko hannuna wani namiji bai taba rikewa ba,

ban san yanda akayi d'an da uwata ta haifa ya juya ni na haifu ba amma nayiwa UMMA uzuri bata da lafiya ne

Abba kaduba d'anan dakai yake kama na sosai."

"Ruwaida fita min agida to dan yayi kama Dani abin mamaki ne AI ni Ubanki ne."

"Abba babu inda zanj.....

Ba Ankara ba yakarbi bindugan ya setting dai dai kirjina inda nan ne rungume da Abdallah jikake tasss

*To fa masoya Sai Naji comment din ku bani da network ne amma ina kallon duk yanda kuke comment kuma na ngd sosai*

*B JATTKO*

*TEAM RUWAIDA*
[9/12, 10:15 AM] ‪+234 803 970 1225‬: *AMFANIN SOYAYYA*
( aure)

*NA*

*BATUL ADAM JATTKO*

*Godiya me tarin yawa ga masoya Wllh bazan* *iya zai yana yanda nima nake jin kuba🤝🏻*

_Masu nema daga farko 🤦🏼‍♀ Wllh ina wahaluwa wajen turawa amma ga number sis dina zasu baku Insha Allah_
08064472038
07086499428

*Garkuwa wannan shafin de naki ne ki rabawa duk fans naki ko da kalma 1 1 1 ne nide naba da* 🤷🏼‍♀🤣

Kainuwa asso

*11....*

"INNALILLAHI!!! sir yanzu ya za ayi kenan?"

"ni ma ban sani ba amma wlllh Allah Ya d'auramin son abinda yake cikinta Kai har mahaukaciyar ma gashi auta yace ko shikara nawa zan iya yi da ita ni de nake ganin Bari zanyi Sai bayan zabe kaga komai yawuce Sai na ganta inda hali ma na kaita sacatry dan nasan mahaukaciyar yar baiwa ce irin Kharajina dan doctor ci daya Sun tabbatar min ba da kowace macce zan haifu ba acikin mata Dari da wuya asamu guda daya da zata dauki kwan haifuwata amma gashi mahaukacir nan ta samu
Kuma Wllh nasan za arina hakan dan komai nata na Kharaji nake ji
Dan haka ina son cikin nan bazan iya zubar dashi ba."

Aminu yace "
hakan yayi daidai amma ya zamu yi da ita da ciki ga hauka ga kuma ita kad'ai agida."?

Wannan ba matsala bane zansa a dauko min wata doctor Yusura a kasan Egypt zata zauna ta ita har ta haifu."

"OK sir."

"Aminu na dauki wannan abin a masayin kaddara ka duba y'ata Ruwaida ta haifi shege na koreta amma gashi ni da girmana nayi abinda banyi a kuruciya taba
Zina harda riban sa
Amma nadauki abin na dan gantashi da hakkin Ruwaida ne."

Aminu yace "to yallabai anemo Ruwaida mana ai neman ta ba zai yi wahala ba gaskiya lefin Ruwaida bai kai ace an yanke mata wannan shukuncin ba"

Mudda ya numfasa yace"hakane Aminu nasani wlllh Ruwaida ba dan lefinta na koreta ba kawai jinayi duk duniya
Bana kaunan ganin Ruwaida ne ita da abin da ta haifa amma acan cikin zuciyata Wllh kullum son Ruwaida da tausayanta karuwa yake amma wani bangaren baya ko son jin sunanta."

Aminu da yasan komai amma ba shida ikon magana dan bai Isa Ya fara tunkaran Mudda da zancen wai malama ce take musu assiri ba

yace "Sir a gani na ya kamata ace kana yawan ziyar tan malaman gaskiya suna baka addu oin kariya kana amfani dashi."

"Aminu AI malama tana iya kokarin a kai na da kyuta da sadakan da takeyi duk akan kariya ta da
cigaba na takeyi tace maganin masifa sadaka."

Nufasawa Aminu yayi dan abune da bashida iko Sai Allah

Sosai doctor Yusura take kula da kharajina duk da har lokacin a haukan take har Allah yasauke ta lafiya ta haifi fararin yara araf irinta a sanda Mudda ya dauki jariran kuka ya dingayi Yana kallon su

Yace "Aminu na yarda Kharajina da Ruwaida Sun zama jinin jikina Kharajina bata duniya amma gashi na haifi yara masu kama da ita Wllh Aminu fuskan Kareji nake gani a tare da jariran nan."

Nace "sosai kamar Ruwa tana karama AI shi jini baya bata sun bi jinin yayar su Ruwaida ne kawai."

"Aminu badan sharadin Auta bai cika ba ba ayi zabe ba da zanso ganin mahaukaciyar nan."

Nace "hakane
Amma Sir me ka yanke game da mahaukaciyar da jariran."

Yace "Eh dama so nake mukaita Gida na dankawa malama ita da sunan sintar ta mukayi akan titi naji tausayinta kaga zata zauna a gidana sannan yarana suna hannun malama zasu tashi cikin ingantaccen tarbiya."

Aminu ya numfasa yace "haka ne Sir amma anawa ganin hakan bai yiba sabo da malama tana da ilimi da saurin fashimta tabbas zata zargi wani abu musamman yanda yaran sukayi kama da Ruwaida."

"gaskiya kam koni badan akan idona Kareji ta rasu ba kuma ina zuwa kabarinta ziyara kullum indan ina kasan ina ganin tudun kabarin nata ta na kwance ciki ba da zance wannan jininta ne
amma Kai kana ga awai wani mafitan."?

Aminu yace "ni aganina kafito kagayawa doctor Yusura komai sannan ka dan k'a mata amanan Mahaukaciyar ka ga ita likita ce zata san hospital da zata kai ta a can Egypt sannan ita tasan yanda zata kula da jariran."

"amma kakawo shawara amma fa ni hankalina bazai ta ba kwanciya ba idan yarana ba ahannu malama suke ba."

"Eh idan aka yaye su Sai akawo mata amma zaka ce agidan marayu na kasan Egypt kaje aka baka saboda kana son samun ladan rike mayara kaga malama zatayi farin ciki
da hakan."

"to amma Aminu meyasa bazan ce agidan marayu na nan Nigeria na dauko suba."
Chapter 20 · 0% Book details