← Book details Amfanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 46

Sashe 30

Amfanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ummi tafiya kuma ina.?

"au ba kama san da tafiyan ba sabar baka damu ba to zaku fita da Ruwaida ne india."

"Ummi kuma aka bar Khalifa ya koma ba shine likita ba ai shi ya dace ya kaita."

"Kai da maka dace ba Kai zaka Kai ta dan Khalifa an masa kiran gaggawa yakoma amma zai sameku a can zai Kai wani abokin sa doctor zai duba mahaifan nata."

"gaskiya Ummi bani da Time kawai su tafi ko da Anas."

"Ismail ni kake cewa baka da lokacin aikin da na saka?

"sorry Ummi zanje."

Ismail baya son bacin ran Ummin sa yana son farin cikinta dan haka ya amince badan zai iya tafiya da wanda yafi tsana a duniya ba

daga Ruwaida sai Kharajina sai Ismail suka tafi
( *INDIA* )

Ismail tunda ya kai su asbiti bai kara bita kan suba yariga yagama da biyan komai nasu

yasamu hotel yayi zaman sa dan shi jiran yaji ance Ruwa ta mutu kawai yake ayanda yaga tana jin jiki

Ummi kullum sai sun kira Idan ta tambayi Ismail suce yafita haka idan shi tafara kira yace yabar wajen su yanzu

An duba bakin Ruwaida sai da aka bata magani na sati tukun aka shiga aiki da ita ana zatawa aikin yayi kyu amma tayi rashin hak'oran gaba guda biyu saboda cire dadashin kasan hakorin da akayi dan yagama lalacewa sai gefen harsheta da aka dan yanke saboda rubewan wajen

Hamrah da Ayya ma sunzo
Amma sun koma

Mahaifa kuma shima wani kwararren Doc ne Khalifa yazo dashi a Germany amma magani kawai ya daura ta akai yace aiki bazai yuwu ba sai ta gama warkewa da cancer din za amata aiki amma magani zai hana ciwon cigaba

Affan da mommy da suka zo a lokacin jikin Ruwaida ya matsa sosai dan magani ya fara aiki kunsa ance ciwo shi yake fitar da ciwo wani irin ruwa ne me wari yake fitowa a gabanta ka kurajen bakin sun kara fursowa sai wari yake
Affan kuka sosai yake ya fara cewa

"mommy kiga yanda Ruwaida ta takoma mommy idan na rasa Ruwaida nima mutuwa zanyi."

Ruwaida da harshen ta yake nade ba daman tayi magana sai bin Affan da mommy sa taken da kallo hawayen bakin ciki Yana bin kumatunta

Affan da Mommy sa masu sonta ne sakani da Allah ta tsaya jiran wani Mall da bai san darajan ta ba inama zata warke ta samu dama bazata taba bari Affan ya wuce taba dubi yanda take cikin wannan halin amma basu gujeta ba duk da ba yau ta fara mamakin yanda Affan yake sonta ba amma yanzu ta gane Affan Ruwaida yake so ba kyanta ko wani abunta ba
Allah kasake bani dama zanyi amfani dashi ina ma zan warke na auri Affan na nuna masa so

Jikin mommy ta fad'a tafara kuka ita ma mommy kukan ta fara
Tana lallashinta da zata warke kuma koda ancire mata mahaifa Affan zai zauna da ita

Affan da mommy ba karamin temako suka bawa su Ruwaida ba dan tattali da kulawa har aka cire mata bandage harshen ta

ta fara magana amma kadan kadan

Ummi ko sam hankalin bai kwanta da yanda Ismail yake tsula mata k'arya ba dan a k'allla zata kira su Ruwaida so 4 a rana amma kowane lokaci zancen dayane Yamall yafita

shima haka yace yanzu na barsu shiko nan ko awaya sai yayi kwana biyu bai kira Kharajina ba

Akwai ranan da yakira Kharajina tafita wayan yana kusa da Ruwaida dauka tayi cikin tsarkeken muryar tayi sallama

"what!! da kazamin bakin ki kika daumin waya"

kafin ta ce wani Abu har yakashe

Ruwaida kuka ta fara dan duk wannan abin son Mall yana nan agefin zuciyar ta kawai Affan dan yana kyutata matane

Ummi takira Mall

tace "Ismail inason ka hadani da Ruwaida awayan ka yanzu hankalina ya kasa kwanciya da yanda kake kula dasu ni kuma ga Khareji ta shiga watan haifuwa ba daman na barta."

"OK Ummi."

Awaje mall ya tsaya yakira Kharajina
yace "kisa meni a waje."

rai ab'ace ya Kalli Kharajina yace" Ummi tana son cusa min wannan k'azantan Wllh wai fa yanzu kirana tayi wai na dauki waya ta nabawa wannan k'azaman zasuyi magana Wllh da nabata wayana kwara na bawa kuturwa tayi waya dashi

dan haka yanzu zankira Ummi ki karbi wayan kuyi magana a matsayin kece Ruwaida nake ga bazata gane ba ai muryar ku iri daya ne kika kuskura kika bani failure zaki rena kanki."
Yace tare da meka mata

"Hello Ummi ."

.tace cikin nok'e harshe kamar yanda Ruwaida take magana

"yawwa Ruwaida yayan naku yana kula daku yanda ya kamata ko."

"Eh Ummi."

"Masha Allah amma yanzu naji muryar naki Ya fara fitowa sosai ba kaman d'azu ba harshe ya bushe ne.?

"Eh Ummi da sauki."

"Alhamdulilah naji dadi Wllh inda danna min video call nasake gani."

"um um."

tace dan ta gigice sosai
Ismail Karban wayan yayi ya kashe kaba d'aya

yace
"naje duba kudin da akayi charging namu this week
Amma aka ce anbiya harda ragowan canji ma muke binsu waye
AFFAN SULEMAN TABAR.?

Kharajina tace "saurayin tane suka zoda mommy sa suna da kirki suna son Ruwaida irin son mamakin nan baka ga yanda suke kula damu ba."

Murmurshi yayi yace "Good yayi kyu ai dama irin su da suka san darajan ta suya kamata suyi zaman jinyanta ni gobe ina son zan wuce amma kar ki gayawa Ummi zata iya hanawa."

Ismail a Nigeria

duk kan su zaune a parlour Ummi

Ummi tace "ni har yanzu baka gaya min dalilin ka na barin Marar lafiya kazo ba."

"Ummi me amfanin zamana naga *kwarton* ta yabita har da uwar sa ni kuma zaman me zanyi bayan ga abinyi agabana."

Ummi da haushin Ismail Ya kaita wuya
tace "in ma daduron tane me yasa kazo baka sanar dani ba."

"Ummi yan gidan su Halima ne suka matsa na turo."

"katuro ayi me"

Yace "maganan aure mana za a tsayar."

Ummi tace "OK amma iyayen ku maza sunyi shawaran Kai da Sa adu tunda kune manya acikin gidan nan zaku zauna har anfara ginin daga acan filin bayan gidan Daddyn ku Idiris amma ina tsammanin bazai wuce part din Mace daya ba sai de idan karawa zakayi."

washe baki yayi yace nima nafi son zaman gida ba wani k'arawan da zanyi Mace daya ta isheni ai."

Murmurshin mugunta Ummi tayi
tace "kenan baka bukatan HALIMA ko."

"bangane ba Ummi."

"Ai kai yanzu kana da aure tarewa kawai yarage wa matar ka
bayan tafinyan ku da kwana daya nasa an daura maka aure kai da Ruwaida dan maganan kana ba lalle ta rayu ba ya girgizani ina tsoron kar ta mutu ba aure a kanta shine na matsa aka daura auren."

bai yarda ba dan haka fuskan sa dauke da murmurshi ya juta ya Kalli Umman Ruwaida

yace "Ummatee wai ana irin wannan auren dama ko ba namiji kawai sai adaura masa aure."

Umma tace "Eh d'ana nide ba abinda Zance sai Allah yasan Ya albarka dan nayi murnan wannan had'in."

awani irin razane Mall ya mek'e yace "wai dama da gaske ne?

wllh da a aura min ita kwara an auramin Iya Ramatu"

Iya Ramata wata tsohuwar me aikin sune da ta tsufa aka hanata aiki amma tana gidan tazama kamar kakar su

dariya Ummi tayi tace "haba Samaila Iya Ramatu da nima tayi jika dani AI.....

da sauri ya katse Ummin

"Wllh kwara ita ni da ace wannan k'azantan Wllh kwara ku auramin gurguwa makahuwa kurma kuturwa
Ai koda mutuwan zatayi Wllh karuwa ba zata mutu min da aure ba gwara kuturwa wllh bat.......

"Ismail shiru yayi dalilin ganin yanda Umman Ruwaida ta dafe cikin ta da daya hannun ta daya kuma tana yarfashi

Ummi ko cewa tayi "Ismail kana son kashenin yar uwa ko nashiga ukku ni Aishatu mezan ga Khareji jine nefa ya tsunko miki...............

*Tofa yaya Affan da mommy zasuji batun auren nan*

*Mall fa*

*Wllh nikam yanzu Team* *AFFAN* 😭

*B Jattko**AMFANIN SOYAYYA*
( aure)

*NA*

*BATUL ADAM JATTKO*
*ASHBAT*

*Atemaka min da*
*Cigaban Wani novel daga* pg 17

*Na manta sunan sa*

*Wanda wani mutum yake auran mata biyu amma bai san biyu Ya aura ba*
*Yana zaune da matan biyu a gida daya amma bai sani ba shi a daukan sa da daya yake zaune* *kuma dukan su biyun suna haifuwa*
*amma Bai sani ba dan shi d'aya ya aura*

*Sunan mutumin Mukaddam*
*please*
*AMIN TEMAKO*
😭😭

*Sis*
*sunan sa*
*amfanin soyayya*

*shikiman Jattko*

🤣🤣
*Kai sis ina jin dadin irin wannan comment din naku* 🤝🏻
*Jattkon ku*

*Please wanda suka min magana ta private suka ga banyi Ripley ba Wllh network ne yahana yazo amma ni naga tsakon ku*

KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

*17*

Umma rik'e Ummi tayi gam tana wani irin nishi sai ka sunkucecen Yaro yafado sai kuka yake Ummi tsabar murna gigicewa tayi

ta kalli Mall da sai raba ido yake tace "ai sai kaje ka kira min Umman Nafi

Umman Sall ce ta shigo tana tafa hannu
"kai kai "HAJIYA Ruwaiya ya haka kin bar yaro yana yawo a katsan style baza ki yanke cibiya ki dauke shiba da sanyin nan."

"Wllh yaya Turai rasa abin yi nayi duk na gigice memo reza."

cikin k'an kanin lokaci aka wanki Hjy Kharaji da san talelen dan ta mekama da Muk'adda sak

Mall ne ya dauki yaron sai addua yake masa Maman Farida ce tace "Mall ka makale yaro kawoshi nagashi

Murmurshi yayi yace "Mama hudduba fa na masa sunann sa ABDULRAHMAN amma Imran za ace masa ina son sunan ."

yayi maganan Yana mekawa Mama yaron

Ummi tace jiwani iko sai kace d'an sa."

dariya Mama tayi tace" ai ni Mall mamaki yake bani yanda yake jida Ummatin nan tashi yakoma kamar ba sojan da yake mana muzurai ba har yazauna a parlourn da mutane suke ana fira da shi ai abune dako a kuruciyar bai yiba."

Murmurshi Mall yayi yamek'e ya taka har inda Umma take yace" Hajiya Ummatee mekike bukata."

murmurshi Umman Ruwaida tayi tace Kai nake son kani d'ana."

tameke sukayi kanyan bedroom din Ummi

sai da tajira yashiga ta rufe kofan har da key

suka zauna abakin gado
Chapter 30 · 0% Book details