← Book details Amfanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 46

Sashe 35

Amfanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mudda yace "wannan sanin ki amma bazan kyale abokan yinki ba."

ya kalli Kamal
yace
Kamal tun kana yaro katashi a gidan nan kasamu limi da duk abin bukata na rayuwa amma kacutar dani bayan nayar da dakai ayanzu zaka bar gidan nan idan ka kara koda Kallon kofan get dina asan nan zaka fuskanci hukunci

Sai ke yanuna Tabawa da take ta faman naso ita kadai tayi jakaf sai wani mannuwa take jikin kujera

Yace "kema bani da zabin da yawuce nace kibar min gidana dan bawani fansan da zan dauka akan ku na sadaukar dashi ga rayuwan yarana musamman Ruwaida da take wani hali Allah ya albarkaci zuri ana dalilin wannan cutan da kuka musu

Sai kai doctor Habib katuna kana almajiri na daukeka na kaika k'asan Germany kayi karatu duk da Hajara tasa ka amma dukiyata ce amma nima kaci amana na balle wasu

Dan haka baka can canci zama likita ba me kula da lafiyan dan adam zaka samu an rufe hospital din ka kuma kayi hakuri nasa an lalata takardunka tun ajiyan gudun kar kaje wani wajen ka cutar da sauran al umma."

Kamal da Habib kuka suka fara amma Mudda ya daga musu hannu

Suma Mall yasa aka fita dasu

Malama rarrafawa tayi ta kama kafan Hajja tace Dan Allah Hajja kuyafe min banida Kalma da zan kalli idon Khadija ayanzu na nemi yafiyar ta dan almarman Muhammad rasulillashi Hajja ki wuce min gaba."

Hajja tace "malama ko nace Hajara bazan taba yarda ki zauna acikin matan Mudda da yaran sa ki cucemu ba
amma tunda yace shi bazai sakeki ba yanema miki waje."

Da ky'ar su Baba Haruna suka bada hakuri abinka da manya aka sa santa
Amma da sharadin...................

*Borno*

Anwanki Mama an shiryata aka koma kan Ayya matar da take wankan cikin mamaki take k'ara Shafa tuyan Ayya tace ikon Allah nikam Fanta taba jijiyar wuyan yarinyar nan kamar Yana dan har bawa nakeji."

wanda aka kira da Fanta tace" Aisa nima abin yabani makaki tunda nake taba gawa bantaba jin jikin gawa me zafi irin wannan ba kiji kamar me zazzabi bayan gawa sanyi gareshi."

"ai take matan suka fara cewa Anya tarasu kuwa kowa ya taba sai yace shima yaji jijiya yana harbawa zance har yaje wajen maza

Grema yanaji ya sunkuceta sai asbiti

Tunda Ayya da Mama suka kwanta jinya Grema yake da ayar tambaya akan jinyar su dayake lawyer ne yafara zarjin mutuwan da iftilain da yafada family daya acinkin wata 2 kacal

amma dayake hankalin sa ba akwance yake ba yabar case din da kula a abubuwan a hannun Hassan babban a minin sa security s s ne

Hassan yana gudanar da binciken sa yafi bibiyar kanin Mama Bura dan yafi zargin sa haka asanda aka zo aka ce ana zaton Ayya da sauran nunfashinta yayi mugun firgita dan haka Hassan yasake sa ido akan sa

Ana tafiya da Ayya Bura ya tashi yashiga motan sada yake can bayan wasu motoci yajima sannan yafito yazauna acikin jama an duk da alamun bacin rai attare dashi
So biyu yana tashi yashiga motan yafito
.dan haka Hassan yatashi yazaga ta baya ya lallaba yashiga cikin motan da Bura yake shiga dan yana sa rai ko zai kara shigowa

Baya ya shiga kasan kujeru ya kwanta ya setting camera sa yayi lub ya kwata yana Allah Allah yakara shugowa
aiko bai jima da kwankiya ba yasake jin anbude anshigo

Buran ne

magana yafara a wayan sa a handsfree wayan take dan haka Hassan yanajin duk amsan da wancen yake badawa

haba doctor ya zaka bata min aiki Wllh inaga da gaskene bata mutu ba baka san nafi son mutuwar yarinyar fiye dana uwar ba."

Daga jan doc yace "Sir nasa Alluran ne a gaggauce kasan sai da na kashe na'uran d'akin kuma idan na'uran yayi
1minute a kashe za iya gano ni shine ban sa aluran duka cikin Drip din ba kuma ruwan bai shiga jikin ta sosai bane dan ban samu time din da zan k'ara gudun ruwan ba shiyasa ina ganin dogon suma tayi
amma kaga drip na uwar dayake na k'ara gudun ruwan ita yashiga jikinta
Amma sir Kai ka bata min aiki ai sai da nace kabari a yiwa mutum daya daka baya sai ayiwa dayan kace kaide sai dukan su 2 sun mutu atake

Kaga ko dole asamu matsala kayi addua ma kar asirin mu yatonu dan idan an mai data india asirin ne zai tonu dan za ayi kwaji sosai akan abinda yasata dogon suma har na kwana 2

"doctor me mafita."

"ai ni bani da wani mafita Kai ka bata abin taya zaka ce mutum biyu makusan tan juna sun mutu rana daya lokaci daya a hospital daya wani zargi bai biyo baya ba
Hakan ma wai ni nayi gaggawan sallaman ku dan kar ayi bincike akan gawan kuma Wllh idan aka kawota nan zaka min sana din aiki da hukuncin kisa dan nan ba Nigeria bane."

"zansan yanda zanyi ba za akawota nan ba."

Doctor yace"OK Sir nasan tunda aluran nan ya taba jikin dayuwa ta iya rayuwa sai de idan tana da rabo me yawa zata mutu ma."

"OK doc zan sake kiran ka duk abinda ake ciki'

Da harshe turanci suke maganan

ya kashe wayan ya sake fita

Jinjina kai Hassan yayi yace ko ahaka aka tsaya ansamu sheda

Ahankali ya zame yafito yakira yan sanda suka zo suka tafi da Bura da sai hauka yake yana
cewa "menayi to koma me nayi ai zaku bari ayi suturan yar uwata dani haka suka hankada k'yar sa

suka ce idan munje kaji

da ky'ar likitoci suka samu suka gano Ayya tana da sauran numfashi amma tana cikin mawuyacen hali ansa mata alluran guba ne

Sahal yace Girema tunda akwai jet a hannu nake ga su bamu doctor cin da zasu na kula da ita ahanya mukaita Germany wajen kanina Khalifa abin da yakaranta kenan fitar da guba dan ya kware wajen aikin sa shiyasa ma turawan suka rikeshi."

Grema yace "nagode abokina."

Hassan yakira Grema yagata masa yanda abin ya kasan ce

yace "to a kula dashi mu yanzu zamu wuce da Ayya amma kada ayi suturan ita mamar ma akawo asake kwada ta."

atake aka wuce da Ayya

Ita muka mama an tabbatar da tamutu akayi suturan ta

Affan yace "my love mu koma ko kinga Daddy Idiris fada yakeyi meyasa kika zo."

Ruwaida da muryar ya dashe dan kuka ba ataba jin abinda take fada
ta jawo pepper
tayi rubutu akai kamar haka

_my dear nagode da kulawan ka dan Allah ka koma wajen aikin ka kar karasa aikin ka zamu koma nida Kharajina yazanyi Ayya na rasata na hakura_

Yace "Eh my love zan dawo ina kaiku dan nafi son na dank'a ki hannu doctor din da nayarda dashi kinga abinda yafaru da Ayya Ina tsoron duniyar nan my love kar acutar min ke

Murmurshi tayi ta rubuta
_ku dena yaudaran mu akan cewa Anty Ayya bata mutu ba saboda mun damu wato mudena damuwa ko acikin tafin hannu na numfashin ta ya dauke_

"Wllh bata mutu ba yanzu haka ankaita Germany wajen yayan ku doctor

Ruwaida wani murmurshi me ciwo tayi dan tasan mutuwa 1 ce

Bura ya doku iya dokuwa cikin wani waje aka sashi ana gana masa Azaba akan yafadi gaskiya

Zan fada
Ni sunana Ibrashim ni kani ne awajen Kangiram ina jin haushin yanda ta fifita mijinta ta dank'a masa uban dukiya

Shine nayiwa yaran su asiri suka lalace Amina da Muhammad suka auri juna ita kuma Bilkisu nasa mata hauka amma da yake tana shaye shaye sai akace shi ya haukatata dama shaye shayen mani ne sila

AMINA da modu nabisu har kasan da suke da sunan nine kad'ai me sonsu na kawo musu ziyara

Sai da nabari yasha giya yakoshi nace yaje airport ya dauki jirgi suyi yawo da yake dama drivern jigine
Shine nace harda yaran da AMINA shine suka tafi ya dauki jirgi wanda yake dama mallakin shi modun ne

Yana shigowa na fara masa kirari
yayi d'ana yau fa asaman ka kake."

Dariya yayi yace "Baba Bura baka yawa fa."

"Eh mana yau yanda kage hakan nan kyanta ka hau gajimaren gasken yaka mata kahau hugaban matuk'a na duniya."

Yace "Baba Bura bar hawa saman nan banida passenger
kasan ba kowane k'asa nake zuwa ba saboda tsaro."

"haba Modu na kuma dan baka da passenger
ka kasa daukan family ka ku shakata kaida jirgin ka."

"kakawo shawara fa Baba Bura ba uban da ya isa ya hanani jirginane kudin ubana nasato na tsiya yau zamu kwana muna shan iskan sama."

daga nan ya dauki Amina da yaran su biyu suka fita

yana tada jirgin basu wani jima ba yakife shikenan nagama dasu

Sai shima Duno ni nasa aka masa alluran mutuwa asanda ake shirin fita dashi

Sai ita Ayya akan idona suka je asbiti bayan fitan su naje wajen doc da niyar nace yasa mata jinin me HIV dan Greema yafara auren ta bayan natsiyi doc yake gayamin ai jinyar da yake jikin Ayya yafi me HIV hatsari amma bayi karfi ba zata iya warkewa ko akasan nan ma
ciwon hanta ne."

nacewa doctor idan akwai alluran da zai karawa Ciwon karfi dan Allah idan sun sake zuwa ya musu Na fadi kudin da zan biyashi

dariya yayi yace to ai ni ko results din ban masu ba dan bai fito ba nace sai anjima idan suka zo sai na mata akwai alluran da zai k'ara karfin ciwon zanne ma yanzu

Haka ita ma yaya Kangiram aka sa mata wanda zai karawa ciwon ta karfi har mukaje Indian din na siyi wani babba likita yamin aiki akansu

Ina murnan saura Barrat da Bikisu a hankali suma zasu bisu

Banyi dan komai ba sai dan nasan idan babu wadan nan mutanen nine magajin dukiyan su.....

*Tofa duniya juyi juyi ashe akwai wanda yafi Duno taddanci kenan*

*Menene sharadin da Mukaddam yace zai gindayawa malama da kukuncin da yace zai yan kewa Ruwaida*
Chapter 35 · 0% Book details