← Book details Amfanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 46

Sashe 32

Amfanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ita ma komawa ciki tayi

Sosai Nura yake kuma agaban Hamrah

"YaNura ba nace na yafe maka ba."

"nagode Hamrah amma kisani Wllh nima bansan na ginu da sonki da yawa ba saida narasa ki ashe kudi basa maganin so."

Sadiya tace "Hamrah jin abinda Abban Khairat yamiki naso fita a gidan sa sai de yanda muka tara zuria nasan fitan ba mafita bane dan Allah ki yafe masa ko dan yaruwan yaran mu yayi kyau."

"nayafe fa Sadiya."

Nura yace "maganan kudin bank fa."

Hamrah tace
"kudin yana wajen accounter OK dina yake jira yashigar da kudin da sa hannun ka."

washe baki yayi yace nagode yar uwa".

to maganan aikina da kud'in na cikin account fa."

"kallon sa Hamrah tayi tace babu su kud'i na zuba a abubun barayu aikin ka kuma tunda ba kada takardu baza ka samu ba."

atsoroce yace "kina nufin document dina bazasu dawo ba dan Allah Hamrah ki temakeni kibani takadduna."

"Wllh Ya Nura babu su muna kar bosu Ruwaida ta cilla masa wuta yayi kurmu ."

.wani irin kuka Nura yasa

Mamar sa tace "Kai ka godewa Allah mana da baza a kai ka gidan yari ba."

Hamrah tace "kuma zanci gaba da daukan duk nauyin gidan kowa yayi list din abinda yake kashewa a wata yaran duk zan canza musu makaranta sannan wanda suka gama sukawo takardun su nace gaba zasu cigaba na aiki zan sa anemo musu."

duk godiya suka shiga yi mata

shide Nuraddin kuka kawai yake dan yasan bashida wani amfani dunta ko messenger bazai yuwu abashi ba a wannan zamanin bashida ko shidan primary school

bayan kwana biyu Nura yasake zuwa har da kukansa Hamrah ta fasa auren Sahal ta aure sa

"dan Allah Hamrah ki sani ke nafara so arayuwa wllh bazan kuma mai maita lefina ba."

Murmurshi tayi tafara masa wak'a

_na aminta da Kaii Nurah na yarda zaka rik'eni amana in angano wata za aga zahra AISHA Humaira ce ta Nura_

katuno wannan Film din shima yace amana ai inaga abin masu irin sunan ku yabi

Kuka ya fara" nasan kinfi ajina Hamrah amma kisani Wllh duk abinda ya sameni kece tsila arasin kine

Kuma Wllh Wllh inde ni Nura ina numbashi bazan taba barinki ki zauna lafiya ba ko agidan majalisan d'inkin duniya ne balle wani d'an gidan tsohon matemakin shugaban k'asan Nigeria Sa adun banza."

Hamrah tace
"haka kace."

"haka nace kuma zan aikata."

"Bissmillah."

juyawa yayi yafita

Bayan wata ukku anyi auren Ayya da grema bawani biki da akayi saboda mutuwar Duno amarya ta tare sai kuma koya tsarin zaman zai kasance."

Egypt

a Egypt kuwa Ummusulem ta haifu d'anta namiji Mukddam yasa sunan shugaman kasa babban aminin sa Zahkar

Mudda zaune cikin yaran sa dama idan yana gari dauke yaran Kharajina ake sai yatafi a kawosu

"haba yusura ni ayau nake son tafiya da matata nanunawa duniya
da dangina nafito nanuna Ahlan da Sahlan ma yaranane zan fito na fadi gaskiya abin da yafuru tsakani na da Ummusulem nasan Hajja da malama zasu fashimceni kuma na gaya mata tayi sa ar abokiyar zama bazata mata muguntan da wancen kishiyar ta mata ta haukata ta ba

tana da sani sosai ga shikkimar malinta
akwai wani aure da nayi
Wllh ita malama ita tasani nayi."

Yusura tace "haba kataba aure Kennan. "?
"

"Eh amma matar ta rasu."

Yusura tace
Ayya Allah yajikanta ya sunanta?

da sauri Ummusulem tace Kharajina."

Atsorace ya kalketa yace "waya gaya miki."?

Murmurshi tayi tace "kamanta kullum kana cewa itan muka rufe ido Kharajina nake komawa ."

Shima murmurshi yayi yace "haka nefa."

yanzu de goben tafiyan Yana nan ko."

Ummusulem tace "eh amma akano wajen dangina zan fara sauka tukun".

"OK nima nafi son nafara ganawa da dangin naki tukun

washe gari suka tattara suka dawo

Agidan su Mall suka sauka
Cikin mamaki Mukaddam yace "ai wannan GIda Haruna walwalane .?

Ummusule tace "eh ai yayata ce take auren Wakili walwalah

*Tofa wannan babban magana ne dan nesa tazo kusa abinda kuke jira yazo amma kafin nan bari nalek'a wajen Ruwaida*

jiki yayi sauki har ansa ranan aikin mahaifan ta

Hamrah ce takai mata ziyara ita da Juwa da Wassileem

Suna zaune suna fira da ita da Kharajina da Ruwaida Juwa da Wasileem sun fita da Affan

Mommy Affan ta koma amma yanda taken kiran Ruwaida da kula da ita ko su ummi ba sayi

Ruwaida "tace sis yana ga duk kin rame ne."

Kuka Hamrah ta fashe dashi tace "sis dole na rame Wllh ina gani mu kuma a duniya irin k'addaran mu Kennan inaga bazamu taba samun jin dadi ba."

wawulun bakin ta Ruwaida ta bude tace "sis zaki sa zuciyata ta buga meyake faruwa ki gaya min."

Hamrah tace da Aunty Ayya tace kar mu gaya miki agani na rashin gaya mikin bashi da wani amfani

Ruwaida muncuci kanmu ba muyiwa kan mu adalciba gashi mundena zina zina bata dena bin muba

Ayya da zasuyi aure ita ta Grema sunje kwaji akace tana da ciwon hanta wanda ana daukan sa sai da ta gaya min natuno mata ajikin Alhaji Bala Oliya ta iba kin san ana daukan sa ta hanya hada numfashi ko yayu tatta a saduwa ana dauka amma dayake Grema Yana sonta ya rufe abin akayi auren amma tunda akayi aure ko hannun ta bai rike ba yanzu haka ita nazo dubawa tana nan india tana karban magani."

wani irin kuka Ruwaida tasa tamek'e tace "ki kai ni wajenta dan Allah."

Hannu ta Hamrah ta kama tace "sis nima ina da nawa
matsala Ruwaida a yanzu ina shirin fasa auren Sahal

"dan me meyafaru?

share hawayenta Hamrah tayi tace tunda aka yanke auren mu Yasall bai bari na zauna lafiya ba akullum cikin zargina yake Abu k'adan zai hau gaya min maganganu yana min masifa
bayan ya kwace wayan hannun na
sabon da yabani
yaje yayi setting number nada nasa idan aka kirani shiyake rigani jin me za acemin shine muna waya da khaleel Dan gidan Baba Haruna yake gaya min yanda Nura yake haukan shi yadawo shi zai aureni

A ranan baki ga cin mutumcin da yamin ba
Aure da zargi matsalane kuma
anyi anyi ayi auren idan nashiga daga gidan sai na rufe duk wani hanyan da zai zargeni idan muna kusa da juna

amma yan gidan su sunce da auren Ya mall za ahad'a
Ita kuma Ummi ta kafe Mall bazaiyi aure ba sai kin tare da ganan ayi na wanda yake so din".

arazane Ruwaida tace ban gane sai na tare?

cikin mamaki Hamrah ta kalleta

Amma kafin tayi magana
Kharajina tace "ah ah tana nufin sai kin warke kintare gida ne ai ."

Tayi maganan tanayiwa Hamrah kallon zakiyi tabar gaza

Ita ma Hamrah sai asan nan ta tuno ashefa Ruwaida bata san ita matar Mall bace

"Ruwaida tace ni tashi ki kai ni naga Aunty Ayya
Inban da abin Ummi ni me gamina da wani auren Mall yayi mana ko ina garin ma bazan je wajen bikin ba

*Tofa ya ruwaida zata yi idan tasan ita matar mall ce*
*affan fa😭*

*YA Mukaddam zaiyi idan yashiga yaga Khajina Ya malama zataji idan taga mukaddam da tarin yara da mata buyu*

*Wannan rikicin babbane Anzu wajen cakwaciyar fa*

*Ya batun nura na sai yaga bayan auren Hamrah*

*Kar ku damu da yawan post ingantacen labari sai da nazari dan sanu sanu bata hana zuwa ina jin dadin comment dinku*

*Amfanin soyayya yanzu aka fara* 👍🏻🤸🏼‍♀

*B JATTKO**AMFANIN SOYAYYA*
aure

*NA*

*BATUL ADAM JATTKO*
*ASHBAT*

*Sis dan Allah kuyi hakuri da rashin amsa muku comment Wllh bani da network ne amma ni ina ganin duk comment din ku kuma duk group dinda nake ciki idan basu ga posting dina ba Wllh network ne ya hana yashigo amma ni hadawa nake nayi make duka Nagode*

*Musamman wanda suka min magana ta private Wllh na muku Ripley bai zoba ne kumin hakuri dan naga kunfusata sosai*

kainuwa asso

*18*

Ayya nannun Ruwaida da Hamrah ta kama cikin mawuyacin hali
tace "Hamrah banace kar ki gayawa Ruwaida halin da nake ciki ba ita da bata da lafiya

Sis kuyafe min lefin da nayi muku azaman mu
sis na baku amanan Barrat duk da ba kwaina bace ni na kyankyasheta na haifeta da cikina shari a ta bani ita dan haka y'ata ce
na baku amanan ta

Ruwaida kiyi hakuri a duk halinda kika tsinci kanki a gidan auren ki da ya Mall wataran zai soki

dan Allah sis kudin ga sani cikin addua ku bani da wanda ya fiku ga Mamata zuciyarta ta buga bata san wanda yake kanta ba nasan Mama bazata yaru ba ko mata rasu aka boyemin dan nafi sati ban ganta ba bayan tare aka kawomu

Na raba dukiya na gida 5 daya nakune daya na Barrat daya akai gidan marayu daya dangin su Mama daya Grema

Barrat amanan ku Ruwaida
Kumin addua bani da gowa sai ku......

cikin kuka Ruwaida tace "dama haka jikin ki yake ba agaya min ba

Aunty Ayya insha Allah bazaki mutu ba zaki tashi kamar yanda nima nasamu lafiya......

wani irin tari Ayya tafara saiga aman jini ta hanci ta baki

Da gudu doctor suka shigo dan naura yanuna musu komai shima Grema da gudu yashigo amma a bakin kofan ya kafe kamar wanda aka dasa shi baki kawai yabude yake ganin yanda ran Ayya ke son fita duk da danna mata kirji da agajin da doctor suke badawa
Ayya tana rike da hannun Ruwaida anyi anyi ankasa kwacewa har saida rai yayi halinsa

Allahukbar

atare Ruwaida da Hamrah suka zube a sume

dau kansu akayi aka fita dasu

Grema a hankani yake takawa har inda gawan Ayya yake

ahankali yaja ya bude ta "dagaske AISHA kintafi ki tashi mu rayu tare matata
Aisha haka zakimin dafe kirjin sa yayi yaja wani irin numfashi yazube sumeme
to yaza ayi da abinda yake
(RUBUTACCI AL AMARI
GARKUWA TA )

ahankali take bude ido har ta sauke idon ta akan Affan kanta taji ya mata nauyi bin d'akin tayi da kallo tabbas ba d'akin ta bane wani k'ara ta kwala tare da mekewa tsaye

Affan yarik'e mata Hannu yana "please my love ki nayin addua."
Chapter 32 · 0% Book details