← Book details Amfanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 46

Sashe 29

Amfanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Wallashi batun gamsar da namiji ta baki ya hudanci ne abin da ake nufi da matar ku gonakin ku a na nufin kuje busu a sanda kuke so ko dare ko Rana inde ba tana cikin ibada na farillah ba ko jinin al ada ko na biki haka ake nufi*

*Baki da yake da daraja zaka ambaci sunan Allah ka karanta Qur ani meyakai kazanta cikin sa al aura kazan tane dan idan kayi al wala ka tabashi da hannu ko ba da niya ba alwala ya karyi shiko baki Kai tsaye ake budeshi a gaban Allah al aura fa rufeshi ake da yana da ts'arki ai baza ace arufe ba*

*Meyasa Annabi yace idan kana cikin tsiraici kar ka bari al auran ka ya Kalli al k'iblah idan ya zama dole to ka Kare ko da tafin hannu ne sabo al aura k'azantane*
*Shiyasa muke gamuwa* *da sababbin cutuka wanda basu bai yana a daba*

*Akwai wasanni na mutsa sha awa tsakanin miji da mata ya kamata kubi ta hanyan da yadace*

*Ina fatan kun fashimta dan bani da network ne masu bina private shiyasa nayi wannan jawanin anan*

*NAGODE*

*16*

Ummi rumguman Umma tayi ta fara kuka
da sauri Mall ya bude fridge ya dauko ruwa yana yayyafa mata taja numfashi hawaye ne yake ta fitowa amma idon arufe magana ta fara kamar haka

"ba lefin Ruwaida bane dan tayi karuwanci Wllh mune da lefi mungazawa tarbiyar tane
Muk'addam kacuce ni Ruwaida ki yafemin ba lefina bane malama da Mudda ne suka cucemu Wllh in har da gaske Ruwa ta samu wannan na kasun a dalilin zina bazan taba yafewa Malama da Mudda ba.....

Abdallah dan shekara 6 da tunda Mall yayi maganan Ruwa ba zatayi wata 2 aduniya ba yafara kuka sosai

Mall ne yajashi yace "me ya faru please mana Big Boy."

cikin kuka yace "ba kaine ba kace Auntyna zata mutu shikenan bani da kowa mom Ayya da Barrat da mom Hamrah ba sanan."

jan yaron gefe can yayi a hankali yanda su Umma baza su jiba

yace "rabu dasu dama baka san suba barayi ne sato ka sukayi kadena son su daga yau nine Baban ka zan maka duk abinda kake so baka ga na canza maka school ba."

Haka de yayi ta yaudaran yaron har ya ware dashi

Ummi hakuri ta shiga bawa Umma
"haba Kharajina bakya ga halinda kike ciki ba ason masu Ciki suna sa irin wannan damuwan a rai
ba wani karuwanci da Ruwaida tayi sharrin doctor ne kawai
ai jinya bata inda baya shigan mutum nawane suke gamuwa da ciwon Cancer din ta hanyan abinci da abinsha musamman awannan zamanin kiyi hakuri zan bincika kinji yar uwata".

Ummi jan Mall tayi d'aki ta masa fada sosai kuma tace ban da dan uwansa Khalifa bata yarda ko Anas yaji meye dalilin ciwon Ruwa ba shima Khalifa dan Doctor ne tasan zai samo musu mafitane kawai

agidan ance de ciwon cancer ne amma ba wanda yasan dalilin ciwon

duk me imani awannan lokacin idan yaga Ruwaida sai ya zubar bata kwallah dan gaba daya kamanin tama can zawa yayi

Prof Wakili ya Kalli doc yace yanzu ka naga bawani matakin gaggawa da za a iya d'auka.?

"Sir akwai wani hospital a India sun kware wajen aikin cancer din amma fa suna rike mutum har sawon 6months

Sai sun tabbatar aikin su yayi suke bada sallama amma akwai kashe kudi."

"Alhamdulilah inde za asamu nasara ko shekara zata zauna ai kayi mana shirin tafi Ismail da Khalifa da Kharajina."

Sahal ne suna waya da Hamrah yake gaya mata Ruwaida tana asbiti
Aiko gigicewa tayi tana tambayan sa me ya same.?

"wllh dan cancer ne ya taba ta amma bai zama chronic ba ina ga zuwa jibi za afita da ita ma."

kuka Hamrah ta fara
"haba YaSall jinyar da za afita waje ne ba Chronic ba
haba nifa yawanci idan nakirata a waya bata dauka ko Kharajina ta dauka ko akashe
ashe rufata sukayi."

bata jira amsan saba ta Kashe wayan

Juwairiya ta samu tace" dan Allah sis ki gayawa Innan da Baba zamuje Kano yanzu Ruwaida ta ba lafiya."

cikin kuka Hamrah tayi maganan
Juwa tace "wai Aunty meyasa bakya son koyan kurmanci ko kinfi karfin koyane haba komai Sai kice a gaya musu mutum da iyayen sa ba zaiyi magana dasu ba."

"zan koya mana yanzu de jekiyi abinda nace."

tayi maganan tana dialling number Ayya

Ayya tana picking tafara

cewa "mutanen nan kum fa samu lafiya tun dazu ina miki magana har kika sauka baki min Ripley ba
damma kwara ke akan shegiyar yarinyar nan Yau kwana 2 banji ta ba idan nakira ace wai tana bacci wato ta samu danginta ko idan kin sameta ki mata maganan an fitar anko amma nace Sai Kunzo kunga tunkun Abu yana karatowa fa kuyi shiru."

"Aunty Ayya Ruwaida ba lafiya yanzu YaSall yake gayamin amma ni yanzu zan fita zuwa kanon."

afirgice Ayya tace "me meya sameta."

"ban sani ba mude hadu akanon."
ta kashe wayan
ai atake ita ma Ayya ta gayawa Mama da yake jirgi suka biyo har suka riga su Hamrah zuwa

sai dare bayan iyayen sun koma gida daga Ruwaida sa Hamrah da Ayya da Kharajina dan su Nafi ma cewa akayi su tafi sunyi yawa

har yanzu Hamrah kuka take

Ruwaida "cikin karfin hali ta fara magana

"yanzu jinyan da na kwaso na kawowa iyayena kenan da tun ina bariki ya sameni Wllh da ko gawata ba zan yarda su sani ba
Ashe Cabaliya tana da gaskiya da take rashin lafiya taki fadan inda danginta suke."

Kharajina tace "wacece kuma Cabaliya."

Ruwaida tace "Cabaliya me aikin muce wanda ita muka barwa gidan muna hotoro munyi zaman shekara 4 amma har muka rabu bata gaya mana inda danginta suke ba

Haduwar muda
*Gaballiya*

wata rana munje anguwan takwayen ruwa akwai wani GIdan karuwai awajen ja ama an da muka gani ankewaye wata mata kudaje Sai binta yasuke da gani tana cikin mawuyacin hali na rashin lafiya dan gaba daya a rame take kamar skeleton matan sai masifa suke mata su sun gaji da ita tana musu wari a gida ba irin wulakancen da basu mata ba har da tona rami idan bazata fadi inda danginta suke sun Kai taba sai sun binneta amma tayi dariya

tace ita su binne ta yafi mata sauki ba zata taba komawa gida ba

Muda muke cikin mota muna ganin duk abinda sukeyi

kuka Ayya tasa tace yanzu sis wata rana muma idan maza suka dena yayinmu haka zamu koma ko na tsani bariki Allah Yana gani ba nida mafita ne da wajen zuwa."

Ruwaida tace "hakane dama ai kudin bariki ba shida albarka kuma duk karshe bariki haka ne

Ayya ceta nace sai mun temaki matar ko muma wata rana zamu samu wanda zaiji k'an mu

dakyar na yarda sabo da banason talaka a ganina macutane tunda kashi malama talakace a ka aurota taci amanan Babana haka Tabawa talakace taci amana

Amma Ayya da Hamrah suka lallasheni akan muje mu temaka mata

Muka sauka muka karasa inda suke nikam toshe hanci nayi sabida wani wari kurajen jikin matar yake

matan wajen muka tambaya Meya faru

daya daga cikin matan ne tace "wannan da kuka gani tafito cin kasuwa kuma ta gama ci amma lokacin komawa gida yayi taki ta koma kanjamau ne da ita ta fadi garinsu mukaita taki har kudi muka ajiye Har dubu dari 500 dan kar ta tafi a tsiya amma taki ta fadi garin su mukai ta metake son mumata taci ka mana gida da wari shine zamu binneta."

amma marar lafiyar bakinta bai mutu ba sai cewa tayi
"bazan fadi ba abinda ya koroni a garinmu yafi halin da nake ciki ko gawata insha Allah dangina ba zasu gani ba."

Ayya da kuka ta cicibi matar ta sata amota

niko na dinga masifa akan me tasa mana ita a mota ko motan ban hau ba nakira Sani yakawo min mota

su kuma suka kai Cabal asbiti

Sun biya kudin komai har dana nurse din da zasu kula da ita
.haka duk bayan kwana 2 sai sunje dubota aka daurata akan magani da yake tana samun kulawa ras ta tashi har aka bata tsallama da haradin zata na karban magani idan ta kula zatayi rayuwa kamar kowa

Ba irin lallamin da basuyiwa Cabaliya ba akan ta fadi danginta mukai ta
taki
har labarin mu suka bata amma dariya tayi tace Wllh naku me sauki ne nawa bazai fadu ba sai lashira

haka suka Hakura suka kawo mana ida gidan

da suka shigo da ita ba irin masifan da banyi ba amma basu kula ni ba

Ashe nima zan shiga irin wannan halin Wllh inda abariki nake bazan zo iyayena suga halin da nake ciki ba ahe Cabaliya tana da gaskiya."

Kuka tasa sosai

Kharajina
tace "toke sister in banda abinki kina tunanin zaki ci bulus ne ai ba ayiwa Allah dabara gashi Virginity din naki da kije tattali bai miki amfani ba wata kila ma kinyi loosing nasa tunda ance sai an miki aiki a mahaifa."

"Kharajina idan bazaki fadi abinda zai kwantar mata hankaliba ki mana shiru kawai."

Inji Hamrah da taji ciwon maganan Kharajina

Kwance yake ruf da ciki kafafuwan sa a sama sai kad'asu yake akan makeken gadon sa
chatting yake sai faman murmurshi yake yana mamakin yanda ustaziya Halima ta iya tsara kalaman soyayya lalle zatayi dai dai da rayuwan sa

Ummi ceta turo kofan juyowa yayi yaga wane isheshen ne ya shigo masa bako Knocking

yana ganin Ummi ce yasaki murmurshi yace "Hajiya Ummi yanzu fa nake cewa zanje part din ku saboda Matawalle yace zai zo gaida Ummati na dan duk abokaina wanda bai zo yaga uwata ba bani bashi. "

zama Ummi tayi abakin gadon tace "AI son nata abaki ne inda da gaske kake son nata meya hana kaso jininta."

"haba Ummi ina son su mana yanzu nan fa muka gama chatting da Aunty Yusura ta bani Hajara da Ameer muka gaisa."

"meyasa baka son Ruwaida yanzu kwananta nawa a asibiti amma tunran daka kai ta kabar ta kazo baka koma ba gashi har gobe tafiyan ku ni banga kana wani shiri ba duk kabarwa daddyn ku aikin."
Chapter 29 · 0% Book details