← Book details Amfanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 46

Sashe 1

Amfanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ji[9/19, 5:52 AM] .‪+234 806 165 0187‬: *AMFANIN SOYAYYA*
______________________________________

*NA*

_____________________________________

*BATUL ADAM JATTKO*
_____________________________________

*3*........

Shiru Nura Yayi yana tunanin idan fa yayi sake hamrah zata gane manufan sa tunkafin cikan burinsa
Kuma shi akaran kansa da yayi tunani haduwan Hamrah Da Sahal ba alkairi bane tunda dan zamani ne kuma wata kila ai son gaskiya zai mata bawai yayi amfani da ita ya Bari bane idan ko son gaskiya zai mata daidai yake da tonan asirin shi dan Sahal bazai taba k'ele shiba gaban sa ne ya fad'e da yatuna da shirmen Hamrah jiya mafa daga haduwa da MA aji tas ta gaya masa waye shi hamdalah yayi da bata tsayaba

"ya Nura ka gaya min Ka dena sona NE?
Kake cewa naje acinyeni."
Jawota yayi jikinsa
Hamratu ina sonki shikenan tunda bak'eso nima banaso."
Da sauri ta d'ago kai tace "da gaske.?
Dan batayi tsammanin zai hakura ba."
"Da gaske mana MA aji ya kirani muyin magana dashi zai nema min makaranta a Abuja na kai masa takadduna gidansa anjima amma yace muje tare bayan Sun tashi a aiki."
zamewa tayi jin kukan dan autansu Habibullah
Dan shekara 5 fita tayi,
A kan cinyan Innan taganshi yana kukan

Tace"kai Habib kukan me kakeyi.?
"Koko zansha."
"Zoka karba." tace
Ta tsowa yayi Itako Inna saida ya taso yayi inda Hamrah take tukun ta juya taga inda Hamrah take tabe baki tayi ta na mata yatsina irin na kurame idan suka tsani mutum
hannun Habib tari ke suka shiga
Nura yace kekuma me zaki shiko minda wannan kod'ed'en fuska duk majina."
Yayi maganan yana jefawa Habibullah wani mugun kallo
Hamra tace "Allah yaya tausayin sa naji yana zaune akan cinyanta yana ta kuka amma da yake ba kukan nasa take jiba bai dameta ba."

Yace"lalle Hamrah kina daukan al amarin kurma da wasa dashi dafa haukaci d"aya suke shifa idan zai samu yaci ba ruwan sa ko yayi kud'i ko karyayi bai san nema ba yayi dariya yace koda yake ai idan zai yi cini kaiya ma akwai matsala ki duba kiga yanda Baba Kabiru baya cini ki duk yan uwansa Sun fishi cini ki ita ma Innar taki ai duk matan gidan nan suna da Sana a amma ita ko tayi wazai siya kawai ana ta d'awaniya da sune kawai da barin su akayi suna fita bara kamar sauran na kasassu yan uwan su ."
B'ata fuska tayi tace
"amma ya Nura ai Babana yafi kowa iya k'ira acikin su dan de shi baya iya siyarwa ne su baba Habu su sara da araha su saida Wllh da suna saya yanda ya kamata da Sai yafi kowa kud'i amma yanzu sun maidashi ma haukacin dole....
Da sauri Nura ya Kalli Hamrah har tana da wayon haka dafa tare ake haduwa da ita a zagesu lalle dole ya iya takunsa,
Amma afili
yace" kina nufin ba amasa adalci hakan ma kenan ya ka sa mana ya saida."
Itako zuciyar ta daya bata san gatse yayi ba
tace "eh Wllh ai waslem yana da wayo sai yana saida masa."
Ajiyan zuciya Nura ya sauk'e
Yace"yanzu me zaki bashi da kika shigo mana dashi."

"Wai abincin zan d'an raga masa nasan yunwa yake ji."

"Bade abincina ba."
"Dan Allah ya Nur kayi hakuri na bashi ko arabo na."

gani yanda ta marairai ne yasa
yace" shikenan."

Ta zuba masa a plate yafita da shi."
Aiko Saiga Juwa tazo

"ya Hamrah nima ki zubamin.

Nura yace "dauki abincin nan ki kaimin Gida
tun kafin wadan nan masu nunan gwandan su cinye mayinwata."

Kallon Nuran tayi tasan bazai yarda ta zuba musu ba dan haka tayi da bara tace amma ya Nura zan iba Wllh yunwa nake ji.
Ta dauki wani kwano ta cika da abinci Taf
YA kalleta yace
"yanzu har kedin ce zaki ci duk wannan abincin."
"ya Nura naga kaima zakaci."
Yace "no no ina da kudi na naci shikafa."
Tace "nide zanci har dare dan idan muka Kai gidan umma bazan samu ba
Basu bita kan Juwairiya ba suka wuce
Bayan sun Kai gidan su Nura UMMA tana ta faman musu albarka ta zame ta fito ta dauki abincin da tabari a d'aki tabawa Juwa

tace "ungo kikai kuci ina Waslim.?
"yana zauren k'ira
"to ki kirashi kuci har Innan."
Tajuya ta fita a tsorace Dan tasan Nura zai iya biyo bayanta

Da yamma suka je gidan ma aji bayan ya gama gurzan Hamra sukayi magana na fashimta da Nura zai nema masa makaranta yakarbi takaddun Nura ya d'aga Kai yana karewa falon kallo yace "yallabai amma gidan ya hadu ba"
Ma aji yace "ai Sabone kwananan zan tare da matana aciki."
"amma yayi kyu ya dace da my sugar amma ni wanda yafi wannan zan mana"
Dariya Hamra tayi tana jin dadi dan Nura yariga yacusa mata akidan son Hutu

Ma aji yace " to zaku iya tafiya dan nima zan wuce."
Nura Sosa Kai yayi yace "yallabai amma da kadan bar mana mun dan more saboda Sai dare zamu tafi."
Badawa Nura kana sha aninka."
Ma aji yana fita Nura d'aga ta sama yayi bedroom da ita akan tabkeken Bed suka fad'a Nura kamar bazai bar gidan ba Sai wajen 9 na dare suka tafi

Haka washe gari ma Nura ya sa ta tafi da abinci Dan yanason su samu number sentor Zazaje ahannu

Chairman da ta wundo ya ke hango Hamrah cak
Ya meke dan tun ranan yake kwadayinta dan de bazai iya nunawa a gaban ubangidan sa kuma abokin sa senator ba
Ai take ya kira messenger shi yanuna masa ita yace yashigo da ita

Bayan yagama chairman ba karamin dadi yaji ba shima daukan katin sa yayi yabada yace ta bashi number ta Kai tseye ta bashi na Nura
Har tazo fita ta tuno da gar gadin Nura na lalle ta san duk yanda zatayi tasamo masa number Zazaje ne yasa
tace" ina wannan na shekaran jiyan.?
Sai asannan ma yatuno da ashe zazaje ya dameshi akan maganan yarinyar
Yace "ah ba yabaki no ba yace baki kirasa ba meyasa.?

"katin yafadi ne?
"OK ga wani ya dauko yabata
Tana fita ta dauki abincin tayi gaba,
yan wajen sai gulman ta suke suna nunata gatanan
azuciyar tace daga Yau idan kuka ganni ku dukeni

Sai dare Nura yakira zzje yabawa Hamrah yawan ya jima yana ringing akayi picking tun kafin yayi magana tayi ai take Zzje yagane muryan ta
yace "ah ah yan mata nayi ta jiran kiranki shiru."

gaisheshi tayi bata San mezata ce masama Dan haka tace" ga yayana zakuyi magana."
Nura hannu na rawa yakarba yace yallabai menasaran Adamawa kayi gomna munyaba gana majalesa muna kan yabawa Allah ya temaki ME temako;"
"Ameen yace
Ni Susana Nura Hamza Sank'ira Yayan Hamrah Kabir Sank'ira."
"OK Ko kuna anguwan sarkin k'ira ne?
"eh mu jikokin Samaila sarkin k"ira ne Hamrah ta gayamin komai Wllh mu abin tausayine yallabai shekarana 15 da gama secondary amma har yanzu ban ci gama ba bana nema na zana jamb kuma nasamu making sosai zan iya zuwa duk makaran tanda nake so Amma ba dama shine mukayi *AMFANI* da wannan daman dan nasamu nayi karatu Wllh dole ne yajefamu Dan ni ne zan Auri Hamrah kaga dole ne Zai sa muyi haka ko."
"eh hakane kayi dabara amma yanzu ni yazanyi na kasan ce da ita a kullum dan bazan iya zuwa Adamawa akai akai ba ina da aiki."

Shisu Nura yayi can wani da bara ya dado masa
Yace "dama wanda suka gama junior tare yawanci na anguwan boarding school a ka kaisu kawai zan iya cewa zan kaita boarding school din Sai na kawota da ganan ma mayi maganan makaranta na."
Sen ya gamsu da shawaran Nura
Yace "Wllh ko waje kake son fita zan fitar ka cikin satin nan kaide ayi kokarin kawota kawai."
Ahaka suka gama tattaunawa da ga karshe Nura yatura basa number account zai turo masa kud"i

Nura yana Kashe wayan yaje yatara iyayen sa maza harda baban Hamrah yace zai kaita boarding aiko Sun nuna bakin ciki sosai baban Nura harda cewa
"amma ga Harira nan baza ka kai ta ba ita cefa kanwar ka uwa da uba."
Nura yace" Baba duk idan sunaso har su barakan Baba Haruna zan kaisu amma ba irin na Hamrah ba godiya iyayen suka masa
A ranan Umman Nura kwana tayi tana fad'a
Ashe dama ita suke nemawa kud'in makarantan yake cewa shi take nemawa ban taba ganin asarere irin Nura ba.
Allah sarki ita ko Inna Dumba kurma dadi taji sosai har taji kunyar abinda tayiwa Nura dan Tana son yaranta suyi karatu dan itama Sai da tayi secondary na kurame a garin hadeja aka mata aure

Cikin sati Nura ya kama duk wani sayayyan karya na abinda d'an makaranta zai bukata hopping ba Wanda baiyi ba ya tattara ta,
Da sunan zaikaita Government Girls secondary school
Na Bauchi
Sun sauka a Abuja suka Kira senator zazaje saiga su Nura anzaba
Yan kauye a gidan da aka sauke su yace "Wow sugar kinga inda ake rayuwa ko Wllh Sai na gina irin wannan gidan
Suna shiga palon yasake rikicewa
Ganin har yamma sen bai shigo ba ya masa waya yace zai koma kar ya Kwana yan gida su zargi wani abu
Fad'a masa tayi ajikin sa tana kuka "Noory yanzu tafiya zakayi ka barni ni daya ba kajin tausayina a irin wannan Gida yanzu idan ya saidani fa.?

"Haba Hamrah ya zaki ce haka taya zai sai daki Nima baki ji na matsu ya nema min makarantan anan ba ai tare zamu zauna yanzu ma Dan kar agane ne zan goma ke ma kinsan bazan iya rayuwa bake ba ban tabayin tafiyan wuni na barki ba sai yau Wllh bazanyi ko sati ba zan tattara nace nasamu makaranta na taho amma Sai na gamawa su Baraka ciku cikun makarantan su ko da a adamawan ne."
"kuma yaya su makarantan gaske zaka kaisu.?
Chapter 1 · 0% Book details