Sashe 9
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Za ta ji." Ta ce tana ƙoƙarin goya Musaddik tare da kallon Ahmad da ya miƙe.
"Bari na taka miki har ki samu mashin."
"Yauwa ɗan'uwa rabin jiki." Ta ce tana dariya.
Fitowa suka yi a tare suka jera duk da cewar ba magana suke yi ba.
Sai da suka fita daga gidan sannan ta kalle shi ta ce,"Ina son na je gidan Yaya Sha'awa na ƙara duba mijinta."
"Ni ma ina so na ƙara zuwa ciwon Mama ya sanya ban je ba, saboda ya kamata na kai mata wani abu."
"Allah dai ya biya ka ƙoƙarin da kake yi."
"Amin,"
"Bari na ɗan yi cefane dubu uku sai na ije dubu biyu."
"Ok, ki sayi abu a shagon Habu." Ya ce mata tare da yin shagon.
Biskit ta siyasa Raihan na ɗari biyar, sai ta sayi indomie na dubu da ɗari biyar. Dubu ɗaya ta tsinci ashana, suga da gishiri. Sai ƙaramin makilin da ta saya musu don na su ya ƙare.
Bayan sun fito da ga shagon, ya tsayar mata da adaidaita ta shiga tana ɗaya masa hannu.
Da ta isa daidai unguwarsu ta sauka sannan ta biya kudin.
Gidan Maman Muwadda ta nufa don ta ɗauki Raihan.
Da sallama ta shiga cikin gidan, ganin babu kowa a tsakar gidan sai ƙarar tibi, da kuma surutun da take ji a falon ya sa ta tura ta shiga.
"Yar Halas! Da ma yanzu Raihan take mini ƙorafin yau Ummanta ta daɗe a makaranta." Ta ƙarashe maganar daidai lokacin da Raihan ta miƙe, tare da rugawa ta isa gareta tana faɗin,"Oyoyo Umma."
Rungume ta yi ta ce,"Ke dai bari kawai. Ciwon Mama ya tashi na biya na dubata."
"Allah Sarki ya jikin?"
"Da sauƙi."
Zama ta yi gefen kujerar da Maman Muwadda take tana kallonta.
"Bari na kawo miki abinci dama yanzu na sauke."
"Da kin barshi Rainah ta ci kuma sai na ci?" Ta ce mata tana murmushi.
"Haba dai! Kin fi ƙarfin abinci a gidan nan, domin mun zama 'yan'uwa.
"Allah dai ya saka miki da abin da kike mini, domin shi kawai zai iya biyanki."
Murmushi ta yi, ba tare da ta ce komai ba, sai ta miƙe ta shiga kicin ta ɗauki kula ta zuba mata abincin.
"Yau rigimar oga ta tashi. Sai da rana ta yi ya aiko mini da kayan ciki wai waina da miya zan yi mishi. Kin ga yadda na ji haushi kuwa? Don ma Allah ya so ni, lokacin tashin Baba Talatu bai yi ba."
Dariya ta yi cikin tsananin sha'awarta. Duk da cewar Faruk ya fishi matsayi a gurin aiki, amma yana matuƙar ƙoƙarin kula da iyalinsa, don ko kayan da suke sakawa sun bambanta da nasu. Ga shi mutum ne mai tsananin kula da abincin da iyalinsa za su ci. Sam ba ya muguwar cima, wannan ya sa ya kullum kicin ɗinta, shaƙe da kayan abinci. Tana matuƙar sha'awar rayuwarsu, musamman yadda yake mata magana cikin taushi da soyayya. Ko ita da take maƙociyarta da mutunci yake kallonta. Saɓanin Faruk da rashin mutunci da ba ya tashi sai in ya ga ta yi baki.
"Bari na wuce dare ya fara yi."
"To shi ke nan Allah ya kaimu gobe. Ya kamata in za ki koma duba Mama na biki."
"Ai da kin barshi duka yaushe kika je?"
"Haba kar ki damu. Allah ya ba ta lafiya."
Amsawa ta yi sannan ta fita daga gidan.
"Umma kin yi mini tsaraba?"
"Eh, na yi miki kuma Mama ta ba da ayabar da lemu na kawo miki."
"Yauwa Ummata." Ta ce tana tsallen murna.
Addu'ar shiga gida suka yi, sannan ta buɗe musu get suka shiga ciki.
Hutawa ta yi, ta ɗan ƙara gyara gidan, ganin kafin ya fita sai da ya ƙara ɓata gidan.
Tana wanke filet ɗin da ya ci abinci aka kira sallah. Gama wanke wa ta yi, sannan ta shiga bayi, ta ɗauro alwala bayan ta taimaka ma Raihan ta yi.
Da suka idar da sallar, suka zauna a falo, suka ci abincin da Maman Muwadda ta ba su.
"Na ga kamar an kawo wuta a maƙota, amma babu a gidan nan. Raihan, zo ki haska mini na duba mita ko ya ƙare."
WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme.
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43
GE 6
*WASU MAZAN*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 6
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
Miƙewa ta yi, tare da karɓar wayar ta nufi inda take zuwa don ta haska mata.
"Ikon Allah ɗage wutan ya yi kenan?" Ta tambayi kanta cikin tsanani mamaki.
Ba ta kunna wutar ba, don ta san mai zai haifar. Komawa ta yi ta zauna tana mamakin mugun halinsa.
Kasancewar sun ci sun ƙoshi, sai ba ta jira shi ba.
Suka yi isha'i ta yi kwanciyarta tana karatu har bacci ya kwashe ta.
Ba ta san lokacin da ya dawo ba. Cikin bacci ta ji an ɗauka mata duka mai ƙarfi.
Da sauri ta tashi tana salati tare da sosai wurin.
"Mai na yi maka za ka duke ni ina baccina?" Cikin muryar kuka ta yi masa tambayar.
"Ok, tambayata kike ko? To bari na yi miki wanda ya fishi sai ki yi tambayar mai dalili." Ya ce tare da ƙara kai hannunsa wanda ya sa ta miƙe da sauri.
"Uban wa ya ce ki ƙi tashi kina jin ina ta hon?"
"Bacci ne mai ƙarfi ya kwashe ni, saboda na gaji sosai." Ta ba shi amsa cikin muryar kuka.
"Sai aka ce miki hakan ya dame ni, ko ni na ce dole ki nace sai kin yi boko? Kamata ya yi ki zauna a cikin gidanki, ki nemi lada ki zama full house wife, kamar yadda kowa ce mace ƙwarai take yi."
Ba ta ce masa komai ba ta tsaya tana mazurai.
"Oya, ma za wuce ki buɗe mini get don ban shigo da mota ta ba, a waje na ije ta, don ga ki ba zan wahalar da kaina ba."
Miƙewa ta yi, jin abin da ya ce ta sanya hijabi bayan ta ɗaura zani. Get ɗin ta buɗe masa, bayan ya shigo ya kashe motar, ta buɗe bayan motar ta kwashi kayan da ya shigo da shi.
Wucewa ya yi gurin motar ya kunna wutar sannan ya shigo cikin falon.
"Abban Raihan, saboda me ka kashe wutar?"
"Akwai uban da ke biya mini ne?"
"A'a, mamaki dai na yi da ka kashe, saboda matarka da yaranka za su ga haske. Raihan tana ta damuna na kunna mata kallo."
"Shi ma kallon daga yau na daina bari kuyi, domin matuƙar ba za ki zama mace mai tarbiyya ba, ni kuma ƙwandalata ba za ta yi ciwo ba."
"Mai na ke maka Abban Raihan? Iya kokari ina yi na ga cewar ban shiga haƙƙinka ba, amma kullum maganarka ni ba mace ƙwarai ba ce."
"Ok, da ma kina yaudarar kanki kenan? To bari ki ji matuƙar ni zan ɗaga ƙafarsa ki shiga aljanna, babu ke babu samunta, domin ba ki da kirki sam ba kya jin maganata Nasreen."
Ranta ne ya ɓace, ba tare da ta ce masa komai ba, ta juya za ta koma ɗakinta.
"Nasreen!" Ya kira sunata da ƙarfi yana huci.
"Har kin isa ina magana ki tafi?"
"Bacci zan yi na gaji yau."
"Bacci?"Ya maimaita yana mata kallon ƙaskanci.
"Bacci saboda kina hauka ba ki yi girki ba?"
"Na gaji ba zan iya girki ba."
"Ki dai gaya mini kin yi rokon da kika saba, don na san a gidanku babu abincin da za ki samu. In ma kin samu ba ci za ki iya ba."
"Saboda ba a gidan na girma na rayu ba? Wallahi babu rayuwar da ba zan iya fuskanta a cikin gidan ba."
"Bana tunanin za ki iya, saboda shi kanshi maigidan da ya aje ku, ya kasa ci daku, ba iya haƙura yake yi ba. Na tabbata ƙila ya tambaye ki ko kin kai masa kuɗin da ya tambaye ni?"
Ba ta ce komai ba, sai ta fara hawaye tana baƙincinkin halinsa da yake ja mata tozarci.