← Book details Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 40

Sashe 39

Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin abin da ya ce ya yi masa kallon wulaƙanci ta juya kawai ta shiga cikin zauren gidan su. Kuka ta fashe shi, duk da cewar ta yi alƙawarin ta daina yi masa kika, amma maganar da ya gaya mata yi mata ciwo. Yana goranta mata talauci kamar ita ta ke ba da arziki.. Muryarta ya shaƙe yi kamar ta ta sha guba ta mutu. Ji take yi rayuwa ba ta mata adalci. Anya za ta kurɓi ruwan daɗi a cikinta, yaushe za ta yi farincikin da mata suke yi a gidan mazajensu.? Yaushe za ta zamo ɗaya daga cikin matan da WASU MAZAN suke nuna wa ƙauna, suke shayar da su madarar ƙauna da tafi zuma daɗi. Anya hakan zai faru? Tarin tambayoyin da suka cika ƙwaƙwalwarta kenan har suka sanya ba ta ganin abin da ke gabanta.

Da gudu ta shige cikin gida tana kuka. Tsaki ya ja tare da shiga cikin motar da ya tafi. Mama ta yi turus! Cikin damuwa tana kallonta."Na ɗauka ya zo tafiya da ke ne? Amma sai kuka na ga kina kuka."

Hawaye ta share tana kallonta."Mama Faruk ba zai canza halinsa ba, a yanzu rayuwata sai ta fi muni a gidansa, domin ya gaya mini cewar ko na zauna ko ya sake ni. Zaɓi ya ba ni, saboda ya ce yanzu ya samu kalar macen da yake so."

"Haƙuri za ki yi, kina gaya wa Allah kukan ki, saboda yanzu kamar yadda ya ce ba ke kaɗai ba ne, kuma sai kin yi hakuri saboda yawa WASU MAZAN in suka yi sabon aure suna juya wa matansu baya."

"Faruk, bai ƙara aure ba yana wulaƙanta ni, ina ga ya samu matar da yake so. Na san cewa rayuwar da zan yi a gidansa, Ubangiji ne kawai gatana, amma ki sani Mama a wannan karon ba zan yi masa biyayya ba, saboda na gaji da cin kashin da yake mini. Ni ma fa mutum ce mai daraja. A rayuwar aure sai a yi ta cewa mace ta yi haƙuri, bayan an san miji yana cutar ta. Shi ya sa asibiti muka yi yawa mama. Ciwon depression ya yi yawa a cikin mata. Mata suna wani irin rayuwa sai kaga mace tana tafiya tana magana kamar zarrariya. Namiji ya ƙunsa mata baƙin ciki in ta zo gida iyayenta ba za su ƙwato mata haƙƙinta ba, sai a ce ta yi haƙuri. A aure mata kawai ya kamata su rinƙa haƙuri? Mama ba zan yarda ciwon depression ya kamanni ba, na haukace a banza su Raihan suna bukata. ."

"Ki mai da lamuranki ga Allah, duk wanda ya yi haƙuri ba zai taɓe ba."

Kuka ta fashe da shi,"Allah Sarki Ya Ahmad! Ubangiji ya bayyana ka haƙiƙa na yi rashin jigo, amma na yi maka alƙawarin ba zan ƙara zama Faruk ya wulaƙanta rayuwata ba, zan ƙwaci 'yancina, domin tun da na rasa ka bana tunanin a yanzu, akwai abin da ba zan iya rabuwa da shi ba. A yadda nake ji ko ni kaɗai ne a cikin duniya, zan rayu kuma na sanyawa kaina farinciki. "

"To ya za mu yi? Ubangijin kawai ya san yana raye ko ya mutu, fatanmu Allah ya bayyana shi." Cewar Mama tana share hawaye.

A daren ranar ta gama shirye-shirye ta. Kasa bacci ta yi sai juye-juye take yi. Tana tunanin yadda zamansu zai kasance, don ba zata yarda ta ƙara wulakanta ba. Sallah ta yi ta roƙi Allah ya ba ta haƙurin jure duk abin da za ta gani, sannan ya ƙara cire mata tsoron Faruk ta ƙwaci 'yancinta.

Washegari da safe duk yadda Mama ta yi da ita don ta yi kitso da lalli, amma ta ƙi don ba da ninyar zaman auren za ta koma ba, ballanatana ta yi abin da zai burge shi. Kallon kanta ta yi yadda ta rame, duk da cewar ta ciki ba kamar lokacin da ɓacewar Ahmad take sabo ba. Da dadddare Baba ya tsareta sai da ta shirya. Shi da kansa ya kaita har ƙofar gida, sannan ya buga ƙofar."In kin ga dama ki yi hakuri ki zauna da mijin ki, in kuma kin sanya kishi ya sake ki, wallahi kin ji na rantse miki sai dai ki samu wani uban, domin kin san Faruk ba zai karɓi 'ya'yansa ba, ni kuma ba zan riƙe ɗan uban kowa ba, musamman shi da ba shi da ta ido. Kina dai ganin zawaran layinmu sun yi yawa, saboda yanzu maza sun yi ƙaranci. 'Yan matan ma, da yaya suke samun maza, ballanatana zawarawa, kuma in..." Maganar ta maƙale masa sakamakon jin ya buɗe get ɗin.

Ganinsu ya sanya shi canza fuska, ya tokare get ɗin yana kallonsu. Dariya Baba ya yi."Ga shi na dawo da ita a rinƙa haƙuri, na ɗauka da ka zo tafiya da ita za ka yi?"

"Saboda ni na kaita ko? Sharuɗɗa na kafa mata, don wallahi yanzu ba zan ɗauki rashin mutunci ba, ina da matar kirki da take faranta mini tana mini duk abin da na ke so."

Ɗago idanunta ta yi cikin tsana tana kallonsa."Eh ki ji da kyau ɗin haka ki san zaman da za ki yi." Ya ce mata ganin shi take kallonta.

"Ayi dai haƙuri komai ya wuce. Ke Nasreen shiga ciki." Ya ce mata.

Jin hakan ya sa ta fara tafiya za ta shiga. Ganin haka ya matsa ya ba ta hanya yana harararta.

Da ta dumfari gidan gabanta ya fara wani irin sauti. Tana zaune a falo mace ƙatuwar mai jiki sosai. A yadda fuskarta ta nuna ta girmi Nasreen sosai. Tana da ƙiba da kuma ƙirji, sannan ko ina na ta a cike yake. Fuskarta fara ce sosai, domin an dade ana mai. Sanye take cikin wando skin tie ya matse ta dosai, domin kusan yana bayyana surarta, sai riga iya cibi. Kanta babu ɗankwali sai uban attach da aka yi mata kitso ƙanana da su. Tana riƙe da remote a hannunta tana kallon Nigeria film.Tsoro firgici da tashin hankali ya kama ta har sai da ta ji kamar za ta yi hauka. Wani juwa ya kamata har ba ta gani abin da ke gabanta, sai kuma ta dake don ta sanya a ranta daga yanzu ba lokacin da wani a duniya zai tsorata ta bane, ballanatana wata jibgegiyar matarsa ta tsorata ta. Ta riga ta kama yankewa ko zai kasheta ba za ta yi zaman wahala a gidansa ba, don a yanzu ko a mutu ko a yi rai. Za ta nemi farinciki a duk inda take. Ba za ta ƙara yarda wani ɗa namiji ya sanya ta kuka ba. Ita ma mace ce, kuma mace mutum ce da take da daraja.

Tana wannan tunani, Faruk ya ƙaraso cikin falon yana ƙoƙarin cire jallabiyar da ya zura. Da ya cire sai ya rage da ga shi sai gajeren wando. Zama ya yi kusa da ita yana watsa wa Nasreen mugun kallo. Peck ya ba ta gashi tare da sakin mata murmushi, ita kuma ta kamo hannunsa. Zan iya hakuri na zauna kuwa?" Ta furta hakan cikin tsanannin tashin hankali tana ƙaranto duk addu'ar da ta fito bakinta. Basarwa ta yi kamar ba ta gani ba.

Rashida ta mike zuɓbur tana kallonta. Lokaci ɗaya suka ƙara kallon juna. Tun kafin ya aure ta ta so ya nuna mata hoton Nasreen, amma ya yi mata rantsuwar babu hotonta a wayarsa. Da fari ba ta yarda ba, amma da ta karɓi wayar sai ta yarda da maganarsa cewar ba zai sa ya hotonta ba, abokansa su ga ni su yi masa dariyar matarsa mai kama da taɓarya, amma duk da cewar ba ta da ƙiba kyakkyawar gaske ce na nunawa tsara. Tana da haske amma ba irin sosai ɗin nan ba, doguwa ba sosai ba, sannan jikinta mai kyau, irin wanda yake nunawa in ta samu hutu za ta yi hibs. Idanunta dara-dara, sannan fuskarta doguwa ce da hancinta mai tsawo sosai. Tsananin kyawunta ya ruɗar da ita, musamman ƙuruciyarta, domin ita a tunaninta matarsa babba ce. Ta yadda ta ga ta ta san za ta girme mata sosai. Hankalinta ya tashi, amma kuka da ta tuna duk kyawunta ba ta a idanunsa sai hankalinta ya kwanta.

Kallo-kallon juna suka yi, wa junansu kowacce da abin da take tsaƙawa a cikin ranta.

Hanyar ƙofar ɗakinta ta yi, zuciyarta a dake ba tare da tanka musu ba za ta shiga.

Wata uwar tsawa ya daka mata mai ƙarfi. Tsawar da in ya yi mata a da, sai ta ji hatta hantar cikinta ya kaɗa jikinta ya kama rawa, hawaye ya fara zuba a ƙuncinta, amma a yanzu sai kawai ta juya tana masa wani kallo kamar kashi. Idanunta ta ware sosai ta ɗora a cikin nasa fuskarta babu alamun tsoro. Kallon banza ta watsa masa da shi da Rashida, ta take cikin jikinsa kamar za ta shiga cikin jikinsa, tana shafa sajensa. Ta kama hannun Raihan za ta shiga.

Faruk sai ya tsaya sororo, yana kallon ta cikin tsananin mamaki. Goge idanunsa ya yi yana kallon ta da take taku cikin isa za ta shiga ciki.

Ya kalli Rashida ta take kallonsa cikin tuhuma. Ya gaya mata cewar ko muryarsa ta ji, sai ta rikice in ya sanya kara ba ta iya tsallake wa, amma sai ta yi mamakin kallon wulaƙanci da rainin da ta ke masa. Ganin ganin haka ya kira sunanta da ƙarfi.

"Nasreen!"

Ba tare da ta amsa ba, ballantana ya yi tunanin za ta juyi, sai ya ji ta saki tsuka mai ƙarfi ta ci gaba da tafiya.

"Kutumar uba!" Faruk ya furta tare da dumfarota tamkar kububuwa. Sai dai, ya cika da mamakin ba ta gudu ba, kuma ba ta jirga daga inda take ba. A zuciyarta ta riga ta rantse ba za ta ƙara yarda ya taɓa jikinta ba, in kuwa ya yi sai ta yi masa abin da ba zai ƙara gigin dukanta ba. Za ta ƙwatarwa kanta 'yanci ba za ta yarda su wulaƙanta ta ba. Lokaci ya yi da za ta zama mace mai 'yanci kuma ta samu walwala a gidan cikin rayuwarta. A shirye take da duk wani hukunci da zai ɗauka. Lokaci ya yi da zai daina dukanta kamar jaka a gaban yaranta.
Chapter 39 · 0% Book details