Sashe 30
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nasreen da ta lallaɓo ta zo gurin da suke faɗan. Rushewa da kuka ta yi tana kallonsa."Laifin me na yi maka Faruk? Ka zaɓi ka cutar da zuciyata? Ka san a rashin ƙular da ka kasa bani halin ƙuncin da na jefa kaina kuma na sanya wadanda suka taimake ni? Saboda me ba za ka iya ba ni jininka ba? Alhalin akwai wani can wanda babu dangantaka zai iya. Yayan Marwana ya ba ni jininsa wanda hakan ya sanya matarsa ta mutu. Mai na yi maka da ba ka sona? Don Allah ka sake ni Faruk. Na gwammce na fuskanci ko wace irin rayuwa, da na zauna da kai ba ka san daraja ta ba."
Kallonta ya yi cikin tsananin kishi jin wani ya ba ta jininsa. Hannunsa ya sanya ya shaƙeta ba tare da ya kula da halin da take ciki ba."Kika bari aka sanya miki jinin maƙiyina? Na gaya miki na tsani family ɗin su, a dalilin ƙanwarsu da take son ta ɓata miki tarbiya. Tun ranar da kika hadu da ita na rasa gane kanki. Wallahi kin ji na rantse miki sai na je na ji dalilin da ya sanya ya ba ki jininsa, kuma sai na sanya hukuma ta hukunta shi. Daga yau zan sanya ayi miki tsakani da su, domin na lura in har kina tare da su. Kwaɗayinki ba zai bari mu zauna lafiya ba."
Mamaki, takaici, da haushi suka kama su jin abin da ya ce. Ahmad ya kalle shi ya ce,"Kai dabban ina ne ne? Taimakon da suka yi mata sai ka ɗauke shi da mummunar manufa. Idan ka kasa kula da matarka ka ba ta jini, sai aka gaya maka kowa zuciyarsa mara imani ne kamar kai?"
"Wallahi ban yarda ba, ai dama tuntini na fahimci tana kula wasu mazan, saboda innba kuka shi take yi ba, babu yadda za a ya rinƙa ba ta kyauta."
"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Na shiga uku Faruk ka san babu kyau zargi a aure ko?"
"Ke zan gaya ma haka don ki san darajar aurenki." Ya ce mata yana zare mata ido.
"Faruk ka sake ni na gaji da zama da kai. Wallahi ka ji na rantse maka ko kai ne autan maza na gama zama da kai. Am done in this hell that you call marriage."
Wata 'yar iskar dariya ya saki."Ok, na sake ki don ki je ki auri ɗan iskan nan ko? To da na yi ninyar sakin ki, amma kin ji na rantse miki ba zan sake ki ba, sai na tabbatar da babu abin mora a jikinki. Sai na wulanƙa ta rayuwarki, ta yadda babu namijin da zai iya kallon ki har ya yi sha'awarki..."
"Wallahi ba ka isa ba sai ka sake ta yau." Ahmad ya ce yana gyara hannun rigarsa.
"To uban da yake iko dani sai ya yi mini dole. In har kuma son na sake ta, sai ku biya ni tas bashin mahaifinku da yake karɓa sannan kuma ku biya ni duk abin da na kashe, domin tun da na aure ta ban mori komai ba, sai uban yara da ta tara mini."
Tsananin mamaki ya kama su, ganin tozarcin da yake musu ya sanya suka kasa ce masa komai, har ya fice yana takun taƙama.
"Ya Allah ka ɗauki raina don rayuwata babu amfani."
"Kar ki ce haka Nasreen ki yi addu'a." Mama ta ce mata Ahmad kuwa ya kasa cewa komai zama ya yi cikin tashin hankali.
Jikin Mama ta faɗa ta rinƙa kuka tana jin kamar zuciyarta za ta fito waje. Ƙirjinta wani irin zafi take mata sam ba ta da amfani a cikin duniyar.
Faruk na fita kai tsaye ya fara neman gidan su Damir. Saboda tsananin kishi ƙirjinsa har tafasa take masa. Ya san cewa yana sonta tun da ya ganta soyayyarta ta hana shi sukuni, amma mugun halinta da ta kasa bin duk abin da yake so, ya sanya shi wulaƙanta rayuwarta.
Kasancewar gidan na su ba ɓoyayye bane, sam bai sha wahala ba. Ɗaya daga cikin ɗan sandar da ya ɗauko ya kalle shi cikin tsananin razana. "Dama wannan gidan ka ce mu zo mu kama mai gidan?"
"Eh matata yake bibiya ku kama mini shi, sannan ku yi masa warning na yi alkawarin biyan ku ko nawa ne."
Shiru ya yi yana tunani amma jin ya ce zai biya su, sai ya ɗan samu ƙarfin gwiya. Parking suka yi a ƙofar gidan. Ganin taron mutane sai jikinsu ya yi sanyi. Kamar rasuwa aka yi a gidan?"
"Ban damu ba ko uwarsa ce ta mutu. Don ayi rasuwa sai ku kasa kama mai laifi? In ɗan kidnapping ne uwarsa ta mutu ba za ku kama shi ba?" Ya yi musu tambayar a fusace yana zare idanu.
"No ba haka na ke nufi ba." Ya furta cikin sanyin murya yana kallon da.
"To kamar haka ne ka san dai hukuncin wanda yake bin mace da aure?"
Ɗaga masa kansa ya yi ba tare da ya ce komai ba, suka nufi ƙofar gidan jikinsu a sanyaye.
Damir da yake ƙofar gida yana karɓar gaisuwa. Tun lokacin da aka yi rasuwar ya zama kamar mutum-mutumi. Kallon mutane kawai yake yi ya kasa ce musu komai. Idanunsa sun canza sun yi jajur.
Ganin motar 'yan sandar gabansa ya faɗi. Kasancewar bai taɓa ganin Faruk ba. Wannan dalilin ya sanya shi tunanin dalilin da ya kawo su.
Da fari ya ɗauka gaisuwa suka zo, amma bayan sun yi masa gaisuwar sai suka kalle shi." Don Allah nuna son yin magana da kai, saboda wancan ya turo mu don ka zo ayi maka tsaka Ni da matarsa Nasreen. Ya ce yana zarginka da bibiyar matar..."
"What!" Ya ce yana zare idanu."Am sorry ba wani babbar magana ba ce. Cewa ya yi so yake kawai a ja maka kunni kar ka ƙara shiga lamarin matarsa."
Ransa ya ɓaci idanunsa suka firfito. Hawaye kawai yake yi yana mamakin da ga taimako ya sa ya rayuwarsa cikin tashin hankali. Matarsa ta rasu ranta a dalilin haka, kuka yanzu mijin ta yana zargin sa da bibiyar matarsa. Jiri ne ya ibe shi ya dafe mota da sauri yana karanto duk addu'ar da ta fito bakinsa. Ganin yadda ya birkice. "Please Yaya Damir, take easy bari na je na yi musu magana." Ƙaninsa Fadil ya ce yana ƙoƙarin kama shi.
"No, kar ka damu." Ya ce masa tare da ture hannunsa ya nufi inda Faruk yake yana aika masa da mugun kallo. Kallo kallon suka yi wa juna. Kowa tsana ce ƙarara a fuskarsa. Kallo ɗaya suka yi suka tsani juna. Ji suke yi da za a basu takubba don kare kai, ko wane zai iya kaiwa abokin gabarsa farmaka da ninyar kai sa kushewa.
Faruk ya bi shi da kallon tsana. Mamaki yake yi har ya kula Nasreen kuma ya ba ta kyautar jininsa. Wani irin kishi ya lulluɓe shi. Sai ya bi shi da wuƙa yana jin tamkar ya sassare shi da wuƙa.
Damir kuwa mamaki ya kama shi ganinsa wayayye. Saboda halin da yake ciki sai kawai ya kalle shi tare da ɗauke kansa.
"Ba zan iya zuwa ofis ba ina karɓar gaisuwar matata." Ya furta cikin karayar zuciya.
"Eh, ku yi masa tsakani da matata." Faruk ya ce yana zare idanu da kumfar baki.
"Shi kenan in sha Allahu ba zai ƙara ganina ba, kuma matarsa ba zan ƙara shiga lamarinta ba." Ya ce tare da juyawa.
Harara Faruk ya bi shi da shi har ya shige cikin gidan.
Damir yana shiga cikin ɗaki kai tsaye ɗakinsa ya wuce. Gilas ya ɗauka ya yi jifa da shi. "Mai ya sa kika shigo rayuwata don ki tarwatsa mini farincikina? Ashe taimakon ki zai zame mini rashin alkhairi? Haƙiƙa kin cancanci a kira ki tauraruwa mai wutsiya. Na tsane ki Nasreen ko a mafarki bana fatan Allah ya haɗani dake." Sai ya fashe da kuka cikin tsananin tashin hankali.
Mommy ta kama shi ta riƙe ganin ya ji wa kansa ciwo."Haba Damir ka zama mai imani da hakuri."
"Mommy taimako yana zama laifi? Mijin ta ya kawo 'yan sanda ayi mana tsakaninsa ita, wai ina bibiyar matarsa!"
"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Wannan wane irin musiba ce? Yarinyar nan wallahi in har Marwana ta ƙara hurɗa da ita sai dai ta nemi wata uwar. Yarinya ta zamar mana baƙar daga tauraruwa mai baƙar wutsiya!"
Marwana da take bakin ƙafa tana jin abin da Mommy nta ce, sai ta fashe da kuka. Kuka take yi sosai tana tunanin halin da take ciki.
Mommy da ƙyar ta rarrashe shi sannan ta fito. Marwana ta gani a tsaye a bakin ƙofar tana ta kuka. Wucewa ta yi ba tare da ta ce mata komai ba. Zama ta yi ta ɗauki Little Marwana da ta samu bacci ya ɗauke ta.
Nasreen da aka ba ta sallama Ahmad gida ya wuce da ita. Kuka sosai take yi har suka isa gida. Da suka isa gida ɗaki ta shige ta kwanta. Kanta ke ciwo ga cikinta da har yanzu yana mata ciwo.
"Rayuwata ba ta da amfani Allah ka ɗauki rayuwata na huta." Ta ce tana share hawaye. Kafin wani lokaci kanta ya ɗauki zafi sosai, tamkar tukubar mai tsire.
"Nasreen, ki sha magani ki samu ki ji sauki, gobe mu je mu yi musu gaisuwa."
"Mama, ku je kawai ba zan iya ƙara ƙara hada idanu da su ba. Sun yi mini alkhairi na zamar musu tauraruwa mai baƙar wutsiya."
"Duk abin da kika ga ya faru haka. Allah ya ƙaddara. Duk abin da za su ce, ai ya zama dole mu je mu yi musu ta'aziya."
"Kai innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Ta ce tana rintde idanunta.