Sashe 25
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babu musu ta yi masa sallama.Cikin izza ya amsa don ya ɗauki muryar.
"Lafiya?" Ya ce mata a gimtse yana mamakin kiran
Daurewa ta yi ta kawar da muguwar shawarar da zuciyarta take ba ta tana zugata kan ta danna masa ashar, a maimakon hakan sallama ta yi masa, wanda ya amsa kamar mai ciwon baki.
"Na san ka gane ni matarka ce ba lafiya tana asibiti."
"Ya za a yi na kasa gane ki uwar shishshigi." Ya ce mata yana girgiza ƙafafunsa.
Ranta ya ɓace amma sai ta daure za ta yi magana ya riga ta."Ba ta da lafiya sai ta kasa kiran kowa, sai ke dangin dagiro?"
"Faruk, don't provoke me. Nasreen tana cikin halin rashin lafiya ɓari ta..."
"Ɓari me? A gidan uban wa ta yi cikin?"
Tambayar ya yi matuƙar ba su mamaki da haushi, har bai san lokacin da zuciya ta cika shi ba ya gushe wayar ya ce,"Kai wane irin mara mutunci ne? Kana rayuwa da matarka kake tambayar ina ta samu ciki?"
Jin muryarsa ya yi ta doki kunnensa "To ɗan iya! Kai kuma a dangin wa? Kuma ba zan tambaye ta ba, tun da ban san da cikin ba?" Ya yi dauriyar faɗin haka duk da cewar muryarsa ta firgita shi.
"Kana tsoron Allah kuwa?Anya ka ɗauki aure a matsayin bauta, kana da sanin cewar Allah zai tambaye ka yadda ka riƙeta a ranar alkiyama"
"A'a ba na tsoron Allah sai na ka. Kuma da kake mini tambayoyin nan kai a zuwa? Ban san matata na da ciki ba, laifi ne na tambaya?"
"Ban yi mamaki ba saboda ba ka da hankali, har za ka iya sanya ƙwanka ba tare da ka sani ba."
Zuciyarsa ta tunzura jin bin da ya ce. Zaginsa ya fara yi, amma sai ya dakatar da shi ta hanyar cewa,"Ni ba jahili bane kamar ka. Matarka tana kwance a asibiti kuma jini ake so, don haka sai ka yi sauri ka zo ka bada jinin, saboda an nema babu kalar nata."
"Kutumar uba! " Ya ji ya danna ashar. Yana mamakin abin da ya ce, sai kuma ya ɗora da cewa,"Wallahi ko mutuwa za ta yi ba zan bayar ba. Ina tsaka da cin amarci sai a iban mini jini?Wallahi uban kuturu ya yi kaɗan."
Ƙit ya kashe wayar yana zagi. Kallon wayar suka yi cikin mamaki.
"Marwana irin mijin da take aure kuma take zama da shi kenan?"
"Ya za ta yi? Rayuwarta rana zafi inuwa ƙuna. Mahaifinta shi ma rayuwar sa babu dama. Ƴaƴanta daya shine kawai haskenta."
"Kira shi ki sanar masa." Ya ce cikin ɓacin rai yana jin kamar ya zama hukuma ya hukunta shi.
Cikin sanyin jiki ta danna kira. Ringing biyu ya ɗauka."Hello, ƙanwata, yanzu na karɓo cajin na ke shirin kiran ki."
Gyaran murya ta yi ta ce,"Ba ita ba ce ƙawarta ce. Muna asibiti ta yi ɓari."
Salati ya sanya jin abin da ta ce,"Don Allah wane asibitin?"
Kwatance ta yi masa ya kashe wayar.
"Ƴaƴanta yana so ta shi ne gatanta." Shiru kawai ya yi ba tare da ya tanka ba.
Bai ɗauki tsawon lokaci ba ya ƙara so. Hankalinsa a tashe ya shigo cikin asibitin. Mamakin kyaunsa asibitin ya kama shi, domin ya dai san asibitin, amma bai taɓa shiga ba.
Kallonsu ya yi yana mamakin kyawunsu da haɗuwarsu. A ransa yake godiya ga Allah da ya haɗa ta dasu.
"Tun jiya take asibitin nan ta kira wayarka a kashe, sai ta kira ni. Ta yi ɓari jini ake so kuma ba su da jini. Shi ne suke son a samu wanda za a ɗiba. Ta gaya mini Faruk kalar jininsu ɗaya."
Kansa ya ɗage domin kalar jininsu ba ɗaya ba."Yanzu mai Faruk ɗin ya ce?" Ya yi mata tambayar duk da ya san ba zai yarda ba.
Cikin takaici ta ware hannunta ta ce,"Ya ce ba zai bayar ba, ko mutuwa za ta yi."
"Hhmmmm!" Ya ce dama ya san za a rina, an saci zanin mahaukaciya.
Ɗakin da take ya shiga. Ganin haka suke bishi har da Damir. Damir ya shiga don ya ɗauki Little Marwana su koma gida. Don in bai bar asibitin ya yi baz zuciyarsa za ta iya harzuƙa ya sanya a ɗaure sa.
Yana ƙarasawa kan gadon ya hau ya kama hannun ta."Ƙanwata ashe ba ki da lafiya."
Kuka ta saka tare da kama hannunsa."Yanzu ina za a samu jinin?" Jin bin da Marwana ta ce sai ta kalle ta.
"Faruk ya ce ba zai bayar ba ko?"
Shurin da ta yi ya tabbatar mata da hakan. Kuka take yi sosai.
Damir ya ɗauki Marwana zai fita saboda kukan damunsa yake yi. A rayuwar sa ya tsani kukan mace, wannan dalilin ya sanya Batula ta gane lagonshi take masa kuka a duk lokacin da take son ya amince da wata buƙata da take da shi.
Hannunsa Marwana ta kamo tana kallonsa. Juyowa ya yi yana kallonta ba tare da ya ce mata komai ba.
"Jininku iri ɗaya ne, don Allah ka taimaka a ibi naka.."
"What?" Ya ce yana zare idanunsa yana kallonta, sai kuma ya ɗora idanunsa kan nata da ta yi ƙasa jin abin da ta ce.
Fita kawai ya yi yana girgiza kansa, ba tare da ya ce komai ba. Shi kansa ya rasa gane dalilin da ya sanya shi ƙin amincewa.
"Zan je na nemo jinin ko kuma wanda yake da kalar jinin. Mun gode da ƙaunarku gareta." Ahmad ya ce tare da miƙewa.
Wai readers kun san me? Labarin WASU MAZAN kamar yanzu aka fara it is just beyond predictable. This part that we are is just like the introduction part. Ku ci gaba da bibiyarsa kuna rikirkitani da zafafan comments akwai ƙura a cikin labarin.
WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme.
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242
Follow the 𝑊𝐴𝑆𝑈 𝑀𝐴𝑍𝐴𝑁 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xqsd72WTrg772JU2P
*WASU MAZAN*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
Na buɗe wani group wancan ya cika mai son shiga ya bi link ɗin nan👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg
PAGE 15
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM

"Zan je na nemo jinin ko kuma wanda yake da kalar jinin. Mun gode da ƙaunarku gareta." Ya ce tare da miƙewa.
Damir da ya shiga cikin mota sai ya kasa tuƙawa. Rintse idanunsa ya yi. Yana jin wani iri saboda hana jinin da ya yi, amma ya zai yi ya ba da jininsa a sanya wa matar wani? Bayan shi mijin da yake morarta ya ƙi ba da na sa? Sakarcin Marwana ya gani da ta yi masa tambayar. Ta san yadda yake matuƙar shan wahala in har aka ibi jininsa. Baya manta wahalar da ya sha a lokacin da aka sanya wa mahaifinsa jininsa. Sai da ya suma har sau uku. Yana da wadataccen jinin, amma duk lokacin da aka ina ba ya sha ta daɗi.
Kunna motar ya yi, yana jin ba zai iya wannan taimakon ba, amma kuma sai ya ji ya kasa fara tuƙa motar. Cak ya tsaya yana tunani. Tsintar kansa ya yi, da buɗe motar ya koma cikin asibiti.
Saura kaɗan su ci karo da Ahmad da ya fito cikin tashin hankali. Yana tunanin inda zai samu jini. Naira dubu biyu ya tashi da ita, kuma ya ba su Mama su yi girki da shi.
Matsawa ya yi yana kallonsa. Marwana ganin ya dawo sai ta ƙarasa gurinsa."Na yarda a ibi jinin." Ya ce mata cikin murya mai sanyi. Faɗawa jikinsa ta yi cikin farin ciki.
"Mun gode Yaya Allah ya biya ka."
Ba tare da ya amsa ba ya nufi inda ake iban jinin.
Ita da Ahmad sun kasa magana, sai kallonsu suke yi cikin mamaki.
A lokacin da aka sanya masa allura aka caka masa inda jinin zai rinka zuba. Rintse idanunsa ya yi. Yana jin yadda zafin ke shiga ƙwaƙwalwarsa.