← Book details Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 40

Sashe 34

Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Jikin Nasreen ya yi sauƙi domin ba karamin kula Ahmad ya ke ba ta ba. Duk abin da take so shi take ci. Hatta yaranta yana kula da su. Ta samu sauki ta warke sosai. Tana jin daɗin zaman gidan, duk da cewar samuwar halin da ta sanya halin Marwana yana damunta.

Rikici sosai suke yi da Baba da Ahmad, amma ya rantse ba zata koma ba. Shi kansa Faruk ɗin ko aikinsa don yana can yana cin amarcinsa. Rashin zuwa ya ƙara ƙular da Ahmad, ganin bai damu da ita ba. Yana nan yana shirin tafiyar da za su yi. Ya sanya ran da dawo zai maka shi kotu ya yi masa hulɗi ya sake ta.

Ganin ta samu sauƙi ta shirya ta je makaranta. Haushinta ɗaya Faruk ya ƙi yarda a kwaso mata kayanta. Tun da ta doshi get ɗin makarantar zuciyarta ke bugu. Sam ba ta son ta ƙara ganin Marwana, domin har yanzu tana jin ba ta saka mata da alkhairi ba, amma ya za ta yi? Ya zamar mata dole ta ƙara da karatunta musamman da ta kusa gamawa.

Da ta shiga cikin makarantar idanunta na ƙasa har ta ƙarasa kan kujerar ta zauna. A gida ta bar Musaddik don Mama ta ce ta barwa Zainab. Tana zaune tana sauraren darasin har lecturer ya gama suka fita, kafin wani darasin. Zama ta yi a cikin gerden.

Marwana ta ƙara so, cikin sanyi ta zauna a gefenta bayan ta yi mata sallama. Da sauri ta ɗaga kanta tana kallonta jin muryarta.

Hawaye share suka zubo mata. Miƙewa ta yi za ta bar gurin cikin jin kunya. Hannunta ta kamo ta tsaya tana kallonta. Sai kawai ta fashe da kuka. Idan akwai wanda take jin kunya a duniya, bai wuce ita da ƴaƴanta ba.

"Ki yafe mini na ruguza miki farincikin ahalinki. A lokacin idona ya rufe. Tsananin azaba ya sanya na kira ki. Na kira Ya Ahmad..."

"Is ok, ban zo nan don na ji uzurin ki ba. Komai za ki gaya mini ba zai canza komai. Anty Batula ta rasu addu'a kawai za ki yi mata."

"Allah ya jiƙanta kuma zan kasance har ƙarshen rayuwata ina mata addu'a." Ta ce tana share hawaye.

"Na zo na yi miki sallama za mu bar ƙasar. Akwai yiwuwar dawowarmu da wuri ko akasin haka. Tun bayan rasuwar Anty Batula ya canza ya zama tamkar mahaukaci kuma masifaffe. Sam ba ya shiga cikin mutane. Gabakiɗaya rayuwarsa ta susuce."Tsayawa ta yi ko za ta ce wani abu, amma sai ta ga ta share hawaye kawai ta gyara zama. Ganin haka ya sa ta ja numfashi ta ɗora da cewa,"Wannan dalilin ya sanya Mommy ta ce mu bar ƙasar na wani lokaci. Na zo na dakatar da karatuna inna dawo to, in kuma na ci gaba a can shikenan. Ina ta tunanin yadda zan yi miki sallama, cikin ikon Allah sai ga shi mun haɗu."

"Eh, yau na fara zuwa. Ya Faruk ya hana ni komawa. So yake ya yi tafiya ya tara kuɗi akai shi kotu, ayi masa hulɗi."

"Da kyau Ya Ahmad ya cike gurbinsa na Yaya har masa na mahaifinki. Sam bai kamata ki ci gaba da zama da Faruk ba, domin in har kika ci gaba rayuwarki za ta tagayyara. Faruk ba ya ƙaunarki. "

Kanta ta ɗaga ba tare da ta ce komai ba. Hannu ta sanya a jakarta ta ciro maƙudan kuɗi."Ga shi ki kula da kanka. Za ki iya kai shi kotu da waɗannan kuɗin."

Girgiza kanta ta yi cikin hawaye."Ki yi hakuri ba zan karɓa ba, na yi wa kaina alƙawarin ba zan ƙara amsar taimako da ga gare ki ba."

"Haba Nasreen, wallahi ko kaɗan ban zarge ki kan abin da ya faru ba."

"Haka ne na sani amma ki yi hakuri. Ina muku fatan kyakkyawa ra rayuwa, kuma ina neman alfarmarki. Don Allah ki yi ta rokon mini yayanki ya yafe mini. Ki gaya masa akwai wata gangar jiki da jininsa yake yawo a cikinta. Ita gagar jikin ta ba shi wani matsayi mai girma, duk da tsanar da ya yi mata."

"Zan gaya gaya mishi don Allah ki karɓi kuɗin nan."

Girgiza kanta ta yi sai ta juya da gudu ta shige ciki.

Marwana ta daɗe, a tsaye tana kallon ta cikin tausayawa. Har ga Allah ta yi kunyar ta taimaka mata. Burunta su gama karatu ta sanya Ya Damir, ya ba ta aiki, amma ƙaddara ta canza komai.

Bayan sun gama lecture ta koma gida. Tana kwance a ɗaki suna hira cikin nishaɗi. Ahmad ne ya kalle su ya ce,"In sha Allahu, ina ga cikin sati nan za mu wuce Inugu. Ogana ya ce na kasance cikin shiri a kodayaushe zai iya kirana mu wuce."

"Allah ya kaimu kuma ya kaika lafiya ya tsare mana kai." Cewar Mama tana kallonsa.

"Amin." Ya amsa tare da ɓallar raken da yake sha.

Nasreen ta ƙura masa ido ya cikin tsananin so. Ta san cewa abin da yake mata Allah ne kawai sai biya shi. Inda ace babu shi a rayuwarta, Allah kaɗai ya san halin da za ta shiga.

"Ubangiji ya kai ka lafiya ya dawo mana da kai lafiya." Ta ce tana kallonsa.

A maimakon su tafi kamar yadda ya ce, sai ba su tafi ba har suka ƙara sati biyu. A lokacin. Nasreen ta kwantar da hankalinta, ba kamar da ba tana ta zuwa makaranta.

A daren da za su wuce Nasreen da ka ta ta yi masa wanki. Bayan ta gama ta shanya, da suka bushe ta goge masa, sannan ta shirya masa a jaka. Duk wani abin da ya kamata ya ɗauka ita ta shirya masa.

Da ya zo zai yi musu sallama. Ta tsaya yana kallonsu cikin tsananin ƙauna."Mama, Nasreen zan wuce ku yi mini fatan sauka lafiya. Ga wannan kuɗin ku rinƙa amfani da shi kuma cin abinci. Ni ma ba a bani kuɗi sosai ba, in sha Allahu da zarar na fara aiki zan turi muku."

"Ubangiji ya kai ka lafiya ya dawo mana da kai lafiya." Ta ce tana share hawaye sai kuma ta kalle shi ta fashe da kuka."Ka yafe mini na ɗora maka nauyin da ba naka ba."

Murmushi ya yi jin abin da Mama ta ce."In sha Allahu Mama zan kula da rayuwarki da ƙannina sai baba ya yi nadamar rashin bamu kulawa da bai yi ba."

"Allah ya ba ka iko." Cewar Mama.

Nasreen kuwa ƙarasawa kusa da shi ta yi ta riƙe hannunsa."Ya Ahmad amma ba za mu daɗe ba ko?"

"Eh wata ɗaya kawai za mu yi. Duk abin da Bana zai yi miki kar ki koma gidansa. Da zarar na dawo in sha Allahu zan biyasa duk abin da ya kashe ba."

"Faruk ba zai zo gare ni ba, saboda ya samu wacce ta fini. Ina sha Allahu ba zan koma ba." Ta ƙarshe maganar maganarta tana kama hannunsa tana ji kamar karya tafi.

"To in zauna mu je mu zauna mu ci ƙasa kenan?" Ya yi mata tambayar cikin tsokana yana harararta cikin wasa.

"A'a, Ubangiji ya dawo kai lafiya."

"Amin," Ya amsa bayan ya karɓi Musaddik ya riƙe hannun Raihan.

Har ƙofar gida suka raka shi. Har ya hau mashin ta ƙwala masa kira."Ya Ahmad, sai ka dawo Allah ya tsare." Ta furta tana ɗaga masa hannu.

Shi ma hannu yake ɗaga musu har ya ɓule. Da suka dawo cikin gida. Zama suka yi suna ta hirarsa har aka kira sallar azahar, sannan suka tashi suka yi sallah.

A ranar da ya tafi Nasreen cikin dare kasa bacci ta yi. Tana ta tausayinsa yadda ya zaɓi ya wahala don ta kula da ita. Addu'a ta yi masa sannan ta kwanta. Cikin dare ta yi wani mugun mafarki. Mafarkin da ya sa ta tun da ta farka ba ta koma ba. Ta yi karatun Alkur'ani sannan ta yi ta tasbihi tana roƙon Allah ya musanya mata mafarkin ya zama alkhairi. Duk da cewar ba za ta gane abin da yake cikin sa ba, amma tun da ta yi ta nemi natsuwarta ta rasa. A haka ta wuni sukuku da ita, don ko makaranta cewa ta yi ba za ta ce ba.

Tana kwance Mama ta shigo, Da shinkafa da mai da ya ji ta da girka."Nasreen, lafiyarki yau kuwa?"
Chapter 34 · 0% Book details