Sashe 32
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Shit! Kar ki faɗi haka." Ta katse ta tana faɗin haka. Ganin ta yi shiru sai hawaye suke ga zuba daga ƙuncinta ya sanya ta ɗora da cewa,"Kin taɓa ganin wanda ya kashe wani? Anty Batula, lokacin ta ya yi, kuma dama can ba lafiyayya bace, tun kafin ta auri Ya Damir Allah ya ƙaddara sanadin haka za ta mutu. Family ɗina sun yi fushi. Zafin rashinta ya sanya sun ɗauki laifin mutuwarta sun ɗora miki."
"Wannan dalilin, yansa ya na ce ba zan zo gaisuwa ba. Ina jin tsoron haɗuwa da Yayanki. Na san cewa ya tsane ni babu wacce ya tsana kamar ni."
"Haka ne Nasreen, musamman da Faruk ya zo har gida da 'yan sanda ayi masa kashedin ya daina kula matarsa, amma zuwan ya fi rashin zuwan."
Jin abin da ta ce ya sanya ta zare idanunta."Anya Faruk na da imani kuwa? Duk da abin da ya faru kan rashin kula da ni ne?" Ta yi mata tambayar cikin muryar kuka.
"To ya za mu yi? Lamarin ya riga ya faru."
Shiru ta yi tana kallonta ta kasa cewa komai. Yadda Marwana ta dawo kawai zai tabbatar maka da tashin hankalin da suke ciki. Ganin ta kasa cewa komai sai ta kama hannunta.
"Ku zo mu shiga ciki ku yi musu gaisuwa." Tamkar waɗanda aka zare musu lakka haka suka shiga ciki.
Damir yana zaune da hoton Batula ya riƙe yana hawaye. Hannunsa ɗaya kuma Little Marwana da take ta yi masa kuka tana kiran Mommy. Hawaye yake yi sosai. Ya kasa cewa komai, domin shi kansa da ace akwai wanda zai kwanta a jikinsa ya yi ta kuka yana rarrashinsa hakan zai yi, don ya samu sauƙin zafin da zuciyarsa ta ke yi. Ya san cewa lokacinsa shi ma ya yi, domin ba zai iya rayuwa babu Batula ba. Yarinyar da ya so kamar ransa. Tun tana ƙaramar Allah ya sanya masa tausayinta saboda wahalar da take sha na ciwo. Daga baya ta riƙe ta koma soyayya. Yau ga shi ta yi masa nisa. A sanadin taimakon wata can ya rasa masoyiyarsa. In ya tuna hakan sai ya ji ba zai taɓa yafewa kansa ba. Ya yi kuka har ya ji babu daɗi, in ya tuna cewar da shi da Little Marwana sun zama marayu, sai ya ji duniya da abin da ke cikinta sun gimshe shi. Haka nan rayuwar sa za ta ƙare, domin ya yi mata alkawarin ba zai taɓa aure ba. Zai yi ta zama haka har Allah ya ɗauki rayuwarsa ya koma ga Allah.
Jin sallama ya sa shi da Mommy suka ɗago kansu. Zubbur ya miƙe yana nuna ta da hannu.
"Mai ya kawo ki gidan nan? Ki kin zo ki kashe ni ne?" Jin abin da ya ce yana nuna ta ya sanya ta tsaya cak, tare da ɓoyewa a bayan Marwana.
"Ya Dam...."
"Please shut up!" Ya daka mata tsawa yana faɗin haka sannan ya ɗora da cewa,"Kina tunanin akwai malaman da zai sa ya na ƙara kallonta da tausayi? Marwana a sanadinta na rasa matata wacce na ke so fiye da komai. Mai kike so ki gaya mini?"
Shiru ta yi tana hawaye ganin yadda yake magana cikin tsawa tana zare idanu.
"Fita da ita kuma ki gaya mata kar ta ƙara shigowa gidan nan, don ko a lahira bana fatar Allah ya haɗa fuskokinmu."
Duƙawa ta yi cikin kuka ta ce,"Ka yafe mini na san ce...."
"Kar ki ce mini komai! Bana son jin muryarki na tsane ki kar ƙi ƙara fatan ki haɗu da ni, domin kin ji na rantse miki haɗuwarmu ba za ta yi kyau ba."
Jin abin da ya ce ta fisge hannunta cikin na Marwana ta juya za ta fita. Mama ta gyara murya ta ce,"Mun san cewa haƙuri da malamai ba za su taɓa goge abin da ya faru ba, amma don Allah mu zama musulmai masu yarda da ƙaddara, Allah ya riga ya ƙudurta a za ta mutu, kuma babu makawa sai ya faru."
"Don Allah ku fita daga gidan nan don bamu buƙatar ganinku. Marwana ta haɗa zumunci kuma na yi mata gargaɗi in har ta ƙara zuwa inda take sai na yi mata baki."
"Subuhanallahi! Haka ba zai faru ba. In sha Allahu Nasreen za ta yi nesa da ku. Mun gode da abin..."
Maganarta ta katse sakamakon jifa da ƙaton gilas ɗin ɗakin da Damir ya yi. Kallonsa suka yi cikin damuwa. Kukan da Little take masa ya isa ya mai da shi ƙaramin mahaukaci. Ga kuma jaririn da ta bar masa yana ta tsotsan hannu.
"Mommy ki ce musu su fita daga gidannan, in ba haka ba zan iya aikata abin da zai zama dana sani. Zuciyata zafi take yi mini in na ganta. Bana son ganinta na tsane ta."Ya furta hakan yana dage ƙirjinsa, sai kuma ya ruga da gudu kamar zautacce ya ƙara sa gurunta da dake tsaye tana kuka tamkar ranta zai fita.
"I hate you whatever you name. Ki fice daga gidan nan, tun kafin na yi ajalinki. I hate you kar ƙi ƙara fatan ki zo inda na ke, domin duk ranar da kika bari muka hadu sai na yi ajalinki."
Cikin tsawa yake maganar yana zare idanu, wanda a dalilin haka ya sanya duk idanu suka koma kansu.
Ganin haka Ahmad da sauri ya kama hannunta suka fita zuciyarsa na zafi. Faɗawa jikinsa ta yi tana kuka. So take yi ta yi magana, amma ta kasa sai kallonsa take yi, tana haki tamkar ranta zai fita. Shiga cikin napep suka yi ya kwantar da ita a abaya. Ganin yadda ta jiƙe da zufa sai ya cire mata hijabi. "Don Allah ja napep ɗin mu bar ƙofar gidan nan." Ya ce masa cikin dana sanin zuwa. Da ya sani da ya ji maganar ta, amma ga shi zuwan ya haifar da wata damuwar.
Sai da suka yi nisa sannan ya umurce sa da ya tsaya. Ruwa mai sanyi ya siya ya ba ta. Babu musu ta karba sai da tasha leda biyu.
Da suka koma gida sun yi jugum-jugum suna kallonta da ta kwanta. Idanunta rufe amma ba bacci take yi ba. A ranar ta ita kawai ta san zafin da zuciyarta take yi. Ta yi fatan ace ita mutuwa ta ɗauka ba Batula ba, domin mijinta yana so ta haka dangin mijinta. Sannan duniya ta yi maraba da zuwanta, har ta sanya take kurɓar ruwan daɗi a cikinta, amma ita fa sam babu wanda yake kaunarta. Bayan Yaya Ahmad shi ne ya damu da ita sai mahaifiyarta. Tana kwance cikin damuwa. Ta yi kuka har ta ji babu daɗi. In ta tuna rashin mutuncin da Faruk yake mata, sai ta ji tamkar ta haɗiye kanta ta huta. Tana kwance ta ji sanyi na ratsa jikinta. Ganin ta fara kyarmar sanyi Ahmad ya lulluɓeta. Idanunsa sun ciko da hawaye. A ransa ya ƙudiri ko nawa zai nemo sai ya yi wa Faruk hulɗi ya sake ta.
Faruk
Ango kasha kanshi kenan. Tun lokacin da ya je gidan su Damir ya yi musu kashedi. Ya wuce hotel kai tsaye. Amarya tana kwance kamar ruwa tana shan baccin gajiya. Da ya shiga ɗakin ya zauna ya kalleta da take jan rago. A hankali ya zauna a gefenta. Bubbuga filon ya yi kamar wanda zai ta shi jariri."Baby na dawo." Ya ce mata yana kashe mata idanu.
"Oh darling sannu da zuwa." Ta ce masa tare da miƙa masa hannunta da nufin ya zo su kwanta.
Amaimakon ya kwanta sai ya kalleta ya ce,"Ki tashi mu tafi gidanmu."
Miƙewa ta yi ta zauna tana kallonsa."Ba ka ce Mahaifiyaarka ta ce sai ka yi mata kayan faɗan kishiya ba?"
"Ai ba ta gidan tana gidansu. Bakin shi ya sa ya ta zubar da cikin da take da shi. Ni wallahi murna sosai na yi da cikin ya fita, don ban san tana da shi ba."
Jin abin da tace sai ta kalle shi kawai. A ranta mamakin halinsa take yi. Duk yadda take tunaninsa ya wuce haka.
Haɗa kayanta ta yi sannan suka bar hotel ɗin.
Da suka isa gidan kallon gidan take yi sosai tana ƙara kallonsa. Ta gaya mata Nasreen ƙazamiya ce, amma sam ba ta ga ƙazanta a cikin gidan ba, duk da ya yi gyara. Da ace ƙazamiya ce a gidan dole a ga zahiri. Komai tsaf-tsaf hatta kayan kicin ɗin ta sai da ta yi mamakin tsaftarsu.
Abinci ta shirya musu lafiyayyen suka ci cikin farin ciki.
Ganin jikin Nasreen ya yi zafi Ahmad ya kaita kyamis. Ƙarin ruwa ya zo ya sanya mata har gida. Ƙarin ruwan da aka yi mata ya samya ta samu sauƙin ciwon da kanta yake yi. Tana zaune bayan an cire drip ɗin tasha magani. Ruwan koko Mama ta dama mata ta samu ta sha. Raihan take ta kallonta cikin tausaawa. Ja yota ta yi ta rungume tana hawaye.
"Umma, ki bar kuka za ki samu sauki." Jin abin da ta ce sai ta yi ƙoƙarin tsaida ruwan hawaye dake zuba kamar famfo. Duk bala'in da Baba yake yi, Ahmad ya tsaya kan kaifi ɗaya ba za ta koma gidan Faruk ba. Mamaki ya ke ba shi. Ganin ba ta da lafiya, amma ko sau daya bai leƙo ya gaishe ta ba. Yana mamakin mugun halinsa da ya haife su ya kasa sanin darajar su.