← Book details Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 40

Sashe 31

Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da daddare sun kasa bacci sai tunanin lamarin suke yi, musamman ita da take ganin duk abin da ta faru a sanadinta ne. Ahmad kuwa tunanin hayar da zai ɓullo wa Faruk ya sake ta yake yi. Ya san cewar baƙaramin daru za a yi ba, kafin Baba ya amince ta zauna a gidan, amma a wannan karon duk abin da zai faru sai dai ya faru. Ya shirya don ya shanye duk wani wulaƙanci. Ko da ace Faruk zai nace sai ya biya shi, zai je ya samu ko bashi ne ya biya shi, don ya saketa.

Da safe Baba ya shigo ɗakin. Tun daren Faruk ya kira shi ya sanar masa da duk abin da ke faruwa. Ya kuma yi masa barazana da ya biya shi kuɗinsa kaf. Hankalinsa ya tashi tunawa da ko wata ba a yi ba, da ya aro naira dubu talatin, kafin ya bashi kuɗin ba kalar tozarta da bai yi masa ba, amma ya haɗiye. Ya je ofis ɗin da ya fi a ƙirga kafin ya ba shi kuɗin. Babu babu irin tozarta da bai yi masa ba, amma ya jure har sai da ya ba shi. A yanzu cikin kuɗin ba ya tunanin ko dubu uku za a iya samu. Barazanar da ya yi masa kan ya dawo da kudin ya tayar da hankalinsa. Fuskarsa babu rahma ya shigo. Mama tana zaune tana ba Musaddik koko da ta gama damawa.

"Mai Nasreen take yi a gidan nan?" Ya furta cikin ɗauke fuska ba tare da ya amsa gaisuwar da ta yi masa ba.

WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme.

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg

*WASU MAZAN*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan

08144072423

PAGE 18

"Mai Nasreen take yi a gidan nan?" Ya furta cikin ɗauke fuska, ba tare da ya amsa gaisuwar da ta yi masa ba.

"Maganar mai tsawo ne zama ya kamata ka yi." Ta ce masa cikin tashin murya.

"Na zauna saboda me? Abu ɗaya na sani kishi ya sanya ta dawo, kuma wallahi kin ji na rantse, ba za ta zauna a gidan nan ba. Ai na gaya miki duk yarinyar da na aurar, babu ita babu zawarci a gidana. Ke kishiya nawa aka yi miki? Amma kin mutu ne? Saboda baƙin kishi har ta ɓarar da cikinta."

Ba ta yi mamakin abin da yake faɗi ba, don ta san Faruk ya gaya masa ƙarya da gaskiya.

"Lamarin nan da kake gani ya wuce wasa. Inda ka san abin da ya haifar da sai ka yi mamaki."

"Ta ya ya zan sani tun da ba kwa shawara da ni? Kin mayar da ni mara amfani, saboda ba na ciyar daku."

Shiru kawai ta yi, tana girgiza kanta don ba ta san inda za ta fara ba, amma kuma sai ta daure ta ce,"Faruk ba ya kyautawa, a sanadin rashin ƙular da yake ma ta ya janyo matsalo..."

"Kin ga ko kai mai za ki ce babu ruwana, abu ɗaya na sani ba za ta zauna mini a gida ba."

"Baba, wallahi ka ji na rantse Nasreen ba za ta koma gidan Faruk ba, a wannan karon na fito na shirya zan ja da koma waye, don ya ba ta takaddarta. Ko da ace ba shi zan ciyo sai na biya shi sadakinsa."

"Au iyye lailai wuyanka ya isa yanka. Fito na fito za ka yi da ubanka, anya Ahmadu kai ɗan kirki ne?" Ya yi masa tambayar cikin tsanannin mamaki yana kallonsa.

"Ka yi hakuri da abin da zai faru, amma bana tunanin akwai abin da zai sanya na janye ƙudirina."

"Haka kace? To shikenan mu zuba shege ka fasa." Ya faɗa tare da zabga tsaki ya juya ya fita.

Cikin takaici ya ƙaraso gurinta da take kuka kamar ranta zai fita."Ki yi shiru ki daina zubar hawayenki. Da yanzu in sha Allahu in har ina raye, na yi miki alƙawarin babu wanda zai ƙara sanya ki zubar hawaye." Ya ce mata tare da kama gefen hijabinta yana share mata hawaye.

"Yaya, dole na koma saboda Faruk, ba zai sake ki ba sai an yi masa hulɗi, kuma ka ga bamu da kuɗi."

"Kar ki damu da wannan duk inda kuɗi yake zan nemo. Akwai aikin da oganmu yake sanya ran samu a kudi. In sha Allahu zan bi shi don na samo kuɗin."

Kallonsa ta cikin tsananin ƙauna."Na gode Ya Ahmad, Ubangiji ne kawai zai biya ka."

Murmushi ya yi jin abin da ta ce."Ki samu kisha ruwan koko, sai ki shirya mu je musu gaisuwa."

Girgiza kanta ta shiga yi cikin zubar hawaye."Ba zan iya ƙara haɗa idanun da wadannan mutanen ba, domin sun yi mini alkhairi na saka musu da tsiya. Ku je kawai zan kasance ina yi wa matarsa addu'a har tsawon rayuwata."

"Nasreen, ki taɓa ganin wanda ya kashe wani ba tare da lokacinsa ya yi ba? Allah kawai yake da ikon ɗaukan ran bayinsa, domin shi ne ya halicce su. Lokacin mutuwar bawa Ubangiji ya riga ya tsara ta tun kafin zuwan mu cikin duniya. Ko wace mutuwa da sanadinta a rayuwa."

"Na sani Yaya, amma sam ba za su fahimta hakan ba. Ni ce na yi sanadin mutuwar matarsa. Na san cewa a yanzu ba shi da abin da ya tsana sama da ni. Na zama baƙar daga na sanya rayuwarsu cikin damuwa. Marwana kullum burinta ta sanya ni farinciki, sai ga shi na sanya su a cikin ƙuncin da za su dauwama a cikinsa." Ta ƙarashe maganar tana kuka sosai.

Miƙewa ya yi, yana kallon ta ganin rarrashinsa bambaki ba za su yi mata ba."Ko mai za ki ce dole mu je musu gaisuwa, don haka ki gama karyarwa ki shirya bari na yi wanka."

Idanun ta bi shi da shi, ta kasa cewa komai har ya fita. Tun da ya gaya mata zuwa gaisuwar gabanta yake faɗi. Kunya sosai take yi, tana tunanin tarbar da za su musu. A ranta ta yi dana sanin haduwa da Marwana ya fi kwando masaki.

Cikin mutuwar jiki ta gama shiryawa. Tana cikin uwar ɗakar Mama ta yi zugum hawaye yana bin ƙuncinta.

Ahmad ya je ya samu tashar napep suka hau. Tun da suka shiga suka yi shiru. Babu wanda ya yi ko tari, kowa da abin da yake saƙawa a cikin ransa.

A lokacin da suka isa ƙofar gidan wani irin faɗuwar gaba ta ji, har sai da ta kama hannun Ahmad ta riƙe.

"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! 😭 Ta tabbata matarsa ta mutu saboda ni." Ta furta tana kallon get ɗin gidan da ya cika da motoci da mutane.

Ganin ta kasa fita daga cikin napep.Ahmad ya sa ya hannu ya kamo ta. Da ƙyar ta ƙoƙarta ta fara taku tamkar 'yar koyo. A haka suka rasa ƙofar gidan cikin tsananin damuwa. Tun daga ƙofar gidan Nasreen ta tsinke da dukiyar da suke da shi. Tsananin mamakin ƙawance su take yi, domin ta san ruwa ba a san kwando bane. Duk da cewar jikin Marwana, kawai mutum zai kalla ya tabbatar da hutu da jin daɗi, amma ko kaɗan ba ta taɓa tunanin suna da kuɗi haka ba.

Saboda babu wanda suka sani a gidan, sai suka tsaya a harabar gidan suna raba idanu.

Marwana da ta fito, za ta raka ƙawayenta da suka zo mata gaisuwa. Cak ta tsaya tana kallon Nasreen da take tsaye kamar gunki. A hankali ta ƙarasa gunta.

"Nasreen," Ta furta cikin sanyin murya. Da sauri ta juyo ta kalle ta. A tunaninta kamar yadda danginta, suke kallon ita ta yi sanadin Batula haka za ta yi, amma sai ta ga ta share hawaye ta rungume ta.

"Ya jikin ki?" Tambayar da ta yi mata ya sanya ta fashe da kuka.

"Marwana ashe za ki ƙara mini magana? Na ɗauka ke ma kina kallona a matsayin ni na...."
Chapter 31 · 0% Book details