Sashe 37
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin abin da ya faɗa ya sanya gabanta ya faɗi, don ba ta ƙi su zauna daga ita sai shi ba.Ɓata rai ta yi tana kallonsa cikin kissa."Yanzu baby, dawowa da ita za ka yi mu rinƙa sharing ɗinka."
Kallonta ya yi tare da jawota jikinsa."Ƙarki damu dawowarta ba zai hana mu jin daɗin rayuwarmu ba. Don ban damu da ita ba, in ta ga dama ta zauna, in ta ce za ta ɓata miki rai jikinta zai gaya mata, don yanzu kin fi mini kowa a duniyar nan."
Murmushinta saki tana kallonsa."Lallai aikin Malam yana ci, na samu kansa sosai, sai kuma ayi mini maganin maƙonsa." Ta furta hakan a cikin ranta.
"Shikenan ta dawo ka ga dama ni kaɗai nake aikin gidan nan."
"Ƙarki damu babyna, da zarar ta dawo ita za ta rinƙa aikin gidan, tun da ita ce take da yara."Daɗi sosai ta ji jin abin da yace.
Baba da ya koma gida ya sameta tana zaune a ɗaki ta zabga tagumi.Ganinsa ya sanya ta janye tagumin. "Sannu da shigowa Baba."
"Yauwa,"Ya amsa tare da zama kan kujerar.
"Gurinki na zo."
Jin abin da ya ce gabanta ya faɗi, har ta kasa amsa masa sai kallonsa da ta yi. Zama ya yi yana kallon ta.
"Nasreen, ki daina yaudarar kanki ki koma gidan aurenki, domin kin san dai wanɗanda suka ɗaure miki gindi duk sun gudu sun barki?"
"Ya Ahmad ba guduwa ya yi ba, Ya Ahmad ba zai taba guduwa ya bar ni da gangan ba."
"Ko ma dai mene ne ke kike tunanin haka. Don haka ya zama dole ki koma gidanki tun da babu shi."
"To don babu su dai na kasa ƙwatar 'yancina, wallahi na gwammce na fuskanci ko wace irin rayuwa da na zauna a gidansa, domin Faruk azzalumi ne macuci, a dalilin ayi masa hulɗi Ya Ahmad ya ƙarfafa tafiyarsa. Na tsane sa bana ƙaunarsa, kuma ba zan koma gidansa ba."
"Wallahi ba ki isa ba, in har ni na haife ki sai kin koma." Ya ce cikin tsawa yana kallonta.
Kasa amsa masa ta yi tana kallonsa cikin zubar hawaye, ganin haka ya ɗora da cewa,"Yadda Faruk, ya watsar da ke ya ishi ya nuna miki zai iya rayuwa babu ke, saboda kina nan kina shan wahala, amma shi yana morewa da amaryarsa. So na ke na wa 'ya'yanki da ke kanki gata, saboda wallahi in har ba ki hakura kin koma ba, sai kin zama abin tausayi. Kina gani dai yadda abinci yake nema ya gagareki, don haka na je na ba shi haƙuri, sai ki tattara ki koma gidanku."
Ta kasa magana sai kawai ta fashe da kuka."Yanzu Baba, duk wulaƙancin da Faruk ya yi mini, amma har ka iya zuwa gidansa ka ba shi haƙuri?"
"Taimakon ki na yi, kuma da kike wannan maganar mata nawa suke zaman ƙunci a rayuwar aurensu kuma suke haƙuri? Wasu matan babu abinci babu sutura, amma hakanan suke zama a gidajensu."
"Ka yi haƙuri Baba, ba zan iya komawa gidansa ba."
"Ni kuma wallahi ba za ki zauna mini a gida ba, sai dai ki nemi wani gidan uban, sannan in har kika faɗi haka yarannan a yau za ki mayar masa da 'ya'yansa."
Sharhi game da Ahmad.
Jiya da na saki post na ji ƙorafinmu mutane da dama cewar kar na kashe Ahmad masu biyo ni pc da kuma masu comments a group. Duk na fahimce ku kuma na gane abin da kuke nufi. Ku kwantar da hankalinki Ahmad ba zai mutu ba, amma ku sani dole na kauda Ahmad na wani lokaci, saboda Nasreen ta zama jaruma ta ƙwaci yancin kanta. Ahmad so yake a yi wa Faruk hulɗi, kuna ganin hakan mafita ne a gareta? In har aka yi masa hulɗi suka rabu Nasreen ta yi experiencing rayuwa kuwa? Karfa ku manta wanda za ta kuma haɗu da shi wato Damir a dalilin ta matarsa ta mutu har ya tsane ta. Kuna ganin a haka har za ta iya fuskartar ƙalubalen da zai faru, kafin soyayyarsu ta ƙullu? Dole tana buƙatar ta tsaya ta zama jaruma don ta iya fuskantar ko wace irin rayuwa ta tsinci kanta a ciki. Na gode da yadda ku ke kuke bibiyar WASU MAZAN haƙiƙa comments ɗinku yana sanya ni cikin duniyar nishaɗi. Fatana na faranta muku ta hanyar tsara muku labarin domin farincikinku.❤️❤️❤️❤️❤️💃💃💃💃💃💃💃💃👏👏👏👏
*WASU MAZAN*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 21

"Ni kuma wallahi ba za ki zauna mini a gida ba, sai dai ki nemi wani gidan uban, sannan in har kika faɗi haka, yarannan a yau za ki mayar masa da 'ya'yansa."
Sosai take kuka jin abin da ya ce. Kallon yaran ta yi tana jin duk wuya, duk rintsi ba za ta rabu da su ba. Ahmad ya faɗo mata a rai, ta san cewar da yana nan, Baba bai isa ya yi mata dole ba."
"Nasreen ba za ta koma gidan Faruk ba, sai dai duk abin da za ka yi ka yi." Ya ji muryar Mama tana faɗin haka.
"Au ke kike ɗauke mata gindi ko?"
"Haba ka tausaya mata mana. Yaron nan ya nuna baya ƙaunarsa, kan dole sai ta yi rayuwa da shi?"
"Ke mai ya sa ba ki rabu da ni ba? Tun da kullum gaya mini kike ba kya son halina? Sai ita ki sanya ta kashe aurenta. Kina ganin yadda maza suka yi wahala.To wallahi gara tun wuri ki farka da ga barin da kike yi. Kar ki yadda ta ɗora ki a kan keken ɓera."
"Sai dai in ka sake ni, amma Nasreen ba za ta koma gida sa ba."
"Mene ne abin tada jijiyar wuya? In har kin shirya biyansa kuɗi sai ki kai shi kotu." Ya ce yana ɗaya kafaɗarsa alamun bai da mu ba.
Gabanta ne ya faɗi tunawa da hakan. Hawaye ta share tare da kama hannunta ta miƙar da ita, wacce take kuka kamar ranta zai fita."Ta shi ki daina kuka ba za ki koma ba."
"Mama, na san cewa ba ji da gata, tun da Yaya Ahmad ya ɓata. Baba so yake ya raba ni da yarana, ba zan iya kai su gidan ubansa ba, saboda na san Faruk ba zai iya riƙe su ba. In har zai sanya dole na mayar da su, zan koma gidansa ne don kawai bamu da kuɗin da zamu biya sa, amma ba don na ci gaba da biyayar aure ba. Ba zan iya jure rashin mutuncin sa, idan ma yana ganin ba zan iya rayuwa babu yarana ba, zan haƙura da su na yi musu addu'a. Ya Ahmad ya ɓata zan tsaya tsayin daka na ƙwaci 'yancina da yake mafarkin samar mini"
"Allah yana tare dake ki yi addu'a, in sha Allah ba za ki rabu da yaranki ba." Mama ta furta mata cikin rashin ƙarin gwiya.
"Au komawa za ki yi don ki gurza masa rashin mutunci?" Dariya ya saki jin abin da ta ce, sai ya ɗora da cewa,"Da yake ta yaro kyau take ba ta ƙarko. Kina sane da halin sa, saboda ban taɓa ganin tijararren irin sa ba, duk jarabata wallahi ya fini. Ɗan banza mara tarbiyya, amma a haka yake kiran 'yata ba ta da tarbiyya."
Kallonsa Mama ta yi cikin takaici jin abin da ya ce."Saboda ba ka riƙe mutuncin ka bane, duk wannan wulaƙancin da yake mata, ai kai ka janyo mata shi, saboda da ace ka riƙe talaucinka ba ka roƙonsa, wallahi babu yadda za a yi ya rinƙa maka rashin mutunci, amma saboda mutuwar zuciya wai suruki kake gaya ma ya taimaka maka, ba ka ci abinci ba. Ai dole ya wulaƙanta ta, tun da ya san uban da ya ubanta, shi ma rokonsa yake abincin da zai ci."
"Au tijara kike son yi mini kenan?" Ya tambaye ta cikin borin kunya yana kumfar baki.
"Gaskiya nake gaya maka wallahi in har ba za ka canza ba, za ka yi nadama saboda abin da kake yi babu kyau."
Banza da ita ya yi domin gaskiya ta faɗa, ba shi da abin da zai ce. Kallon Nasreen ya yi ya ce,"Oho, yanzu dai shawara ta rage wa mai shiga rijiya. Da na ban yi mata dole ba, zaɓi na ba ta." Ya ƙarashe maganar tare da ficewa da ga ɗakin.
Kuka take yi sosai, ta san cewa ba ta da zaɓi da ya wuce ta koma gidansa. Ba ta da kuɗin da za ta biya shi, da kanshi dole ya saketa, saboda a halin yanzu babu wanda ta tsana fiye da shi."
Miƙewa ta yi, bayan ta share hawaye ta zauna tana tunanin rayuwarta. Da dadddare tana zaune ta ranka tagumi ta yi nisa a cikin duniyar tunani. Ƙarar motar Faruk ya dawo da ita hayyacinta. Gabanta ya faɗi sosai har sai da ta dafe gurin. Idanunta suka fito, don ta san zuwansa ba alkhairi zai gaya mata ba. Kafin ta yi wani yunƙuri ya shiga sakin hon ba ƙaukautawa. Da sauri Baba ya fito daga cikin ɗaki yana ƙoƙarin saka takalmi."Ga wancan tijararren ya iso, bari na yi sauri kafin ya kurmantar da mutanen unguwa." Ya ce tare da ficewa.
Raka shi da idanun cikin tsananin takaici ta yi. Ta san cewa da ace Faruk yana da sakin hannu, sujjada ce kawai ba zai yi masa ba, amma yadda yake da mugun son abin duniya, babu abin da ba zai yi masa ba.
Da sauri ya ƙarasa gurin motar nasa. Yana cikin motar ya ƙure waƙa yana ji."Ashe ka zo? Sannu da zuwa bari a kira ta."
"Ita ba ta san ƙarar motana ba, sai na kira ta? Ko rashin tarbiyar za ta nuna mini?"
"Bacci take yi." Ya yi masa ƙaryata hakan yana kallon sa.
Tsaki ya yi, ba tare da ya ce komai ba ya ci gaba da shan waƙarsa.