← Book details Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 40

Sashe 2

Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ya ke yi har da buga ƙafa. Murmushi da yake yi zai tabbatar maka da mata yake chatting ɗin, duk da cewar ba sabon abu bane a gareta, amma sai da ta ji wani irin ƙunci ya mamaye ta, yayin da wutar kishinsa da ƙaunarsa suka yi matu rubdugu.

"Kina gidan uban wa na yi ta kiran ki ba ki ɗaya ba?"

Tambayar da ya yi mata ya dawo da ita cikin hayyacinta.

"Wallahi babu inda na je, bayan na dawo makaranta, sai dai in wayar ta mutu ka san ɗauke wa take yi."

"It didn't concern me.'" Ya ce tare da make kafaɗa sai kuma ya ɗora dacewa,"Shegen son gasa da goga kafaɗa da 'ya'yan masu hannu da shuni. Kina 'yar gidan Malam Shehu ko uban me ya sanya kika na ce sai kin yi makaranta? Na gaya miki ɓacin Mommy wallahi da ke da makarantar nan har abada!"

Shiru ta yi ta yi tare da mayar da kanta ƙasa ba tare da ta tanka ba, don ta saba. Neman hanyar da zai gabata abinci ya ke yi.

"Ma za ki tashi ki dafa mana abinci." Ya ce ba tare da ya kalleta ba.

Kallonsa ta yi da sauri tana hawaye, amma ganin baya kallonta ya sa ta miƙa cikin galabaita tana haɗa hanya.

Binta da idanu ya yi tare da sakin wani wasan tsaki. Ƙazamiya ji shigar da kika yi da daddare kina zaune da wata banzar doguwar riga. Ni na ƙara auran mata Bahaushiya an yi an gama yare zan ɗauki don sun fi ku sanin darajar mijinta iya tattalinsa, saboda na san da ace ita ne, yanzu ta yi shigar da zai ɗauki hankalina. Ko da yake ina abin da za a nuna ƙirji kamar silifas?" Ya faɗa hankalinsa na kan wayarsa.

Idan da sabo ta riga ta saba da cin mutuncin da yake mata, ko da a gaban kowa ne, amma duk lokacin da ya gaya mata, sai ta ji kamar ta kashe kanta don baƙinciki.

Da ta shiga kicin ɗin, sai da ta yi kuka mai idan ta sannan ta kunna gawayi da ƙurar tana kallon gas ɗin ta da ya daina repelling tun da suka gama amarcinsu.

Da ƙyar ta samu gawayin ya kama kasancewar jiƙakke ne. Bayan ta hura wutan sannan ta zuba ruwa ta koma don ta gyara waken ganin akwai gyara.

Tana girki tana hawaye har ruwan ya tafasa ta sanya waken.

"Ke! ma za ki zo ki ɗauki wannan ɗan banzan yaron na ki ya tashi zai hana ni kallo." Ya ƙwala mata kira yana faɗin haka.

"Abba Hairan, kai fa uba ne a gurinsu bai kamata ace kana kiransu da munanan kalamai ba."

"Ƙarya na yi? Yabon ne kuke yi mini ke da shi a cikin gidan nan in ban da kuci ku yi kashi?"

Shiru ta yi ta kasa ce masa komai sai zuciyarta da take mata rukunin ɓaci rai.

"Wuce ki bani guri tun kafin ƙi ƙara ɓata mini rai na sanya ki kashe girkin nan." Da sauri ta shige kicin ɗin domin ta san cewa ba ƙaramin aikinsa bane.

Goya shi ta yi da yake kuka yana ƙunnai ta cigaba da girkin da shi. Ganin ta ɗora girkin ya san mya shi daina kuka yana kiran ta gama. Tausayin yaron ya cika mata zuciya har sai da ta ji kamar ta yi kuka.

Tana kicin ɗin ba ta gama girkin ba har sha biyu ta buga. Sannan ta ga shinkafar ta tsotse sannan ta zuba masa fulas ta kai mishi bayan ta sanya wa Musadik.
Kallon wulakanci ya yi mata tare da bude fulas ɗin fuskarsa a yatsine kamar ya ga kashi.

"Na gaya miki ki daina sanya mini spicy da yawa ko?"

"Wallahi curry powder da ganyen na'ana'a na sa." Ta ce mishi a tsorace.

Ba tare da ya kalleta ba ya ɗauki cokalin ya fara cakala yana ci wanda zuwa can ya ture abincin.

Cikin wahala take cusa abincin sakamakon ƙirjinsa da ya riƙe mata. Sam ba ta jin ɗandanonsa saboda yunwar da ta ƙwaƙwuleta.

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K

*WASU MAZAN*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan

08144072423

PAGE 2

BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
Cikin wahala take cusa abincin, sakamakon ƙirjinsa da ya riƙe mata. Sam ba ta jin ɗanɗanonsa, saboda yunwar da ta ƙwaƙwuleta. Da ƙyar ta samu ta yi loma biyar, sannan ta mayar ta rufe, don ta san ƙila wannan abincin har gobe shine abincin da za su ci.

Ɗaukar Musadik ta yi, da ya gama cin abinci ta yi ta wanke masa hannu, sannan ta kai shi ɗaki ta kwantar. Gyara yaron ta yi, tare da ɓingirewa sai bacci. Da kyar da siɗin goshi ta samu ta tashi Hairan, kasancewar ta mai nauyin bacci.

Littafan karatunta ta ɗauka, ta shiga ɗakin cikin murna ganin jefa sun kawo wuta, za ta yi karatun test ɗin da za su yi gobe.

Yana zaune a gurin yana chatting da 'yan matansa, har agogo ya buga daya daidai, sannan ya miƙe ya kashe kayan kallon ya shiga ɗakinsa. Wanka ya yi ya fito zuwa ɗakinta .

A lokacin ta dakata da karatunta ba don ta so ba, sai dai bacci ɓarawo da ya yi nasarar sace ta.

"Ke Nasreen," Ya ce yana dukan bayanta wanda ya sanya ta farka da sauri tana zare ido.

Harararta ya yi bayan ya kwanta." Ba na gargaɗiki da ki daina sa yaron nan a gadon nan ba?" Ya ce mata cikin ɓacin rai.

"Abban Hairan, akwai sanyi ka tausaya musu."

Banza da ita ya yi tare da jan Musadik can gefe da karfi.

Shiru ta yi ba ta da bakin magana. Ta san cewa in aka kawo agola a gidansa, tsaf zai iya kashewa, tun da ɗan cikinsa ma bai tausaya masa ba.

Babu kunya ya kwanta tare da rungume ta yana sauke ajiyar numfashi a fuskanta.

Hawaye ne ke zuba a ƙuncinta wanda take gogewa ba tare da ta bari ya gane ba.

"Ni shikenan ba ni da daraja da ƙima, sai in dare ya yi nake mace a gurinsa, amma da safe baiwa?"

Jin ya yi shiru ya sa ya ta yi laƙwas, a jikinta saboda tana so shi ya kai sunan da za a kira shi namiji, amma kwata-kwata ba shi da hali, munanan halinsa da suke sanya tana jin kamar ba ta yi dace miji ba.

Ture ta da ƙarfi ya yi har ta bugu da gado. Ta rintse idanunta tana shafa gurin daidai lokacin da ta ji ya ce,"Kin wani shiga jikinta kamar mage? Nufin ki ni zan yi aikin? Ke ma kin san yau ba ni a wannan mood. Yanzu na hakan taimaka miki zan yi don kar ki je kina kwaɗayin mazan jami'a, saboda ba wani tarbiyyar ƙwarai kika samu ba?"

Gabanta ne ya yi mummunar faɗi jin abin da ya ce. Hankalinta ya tashi sanin cewar sam babu kyau miji ya rinƙa zargin matarsa.

"Zargina kake Abba Hairan? Duk tsawon shekarun da mun ayi ban yi zina ba sai yanxu?"

"Ko wa na iya canzawa lokaci guda. Yadda rayuwa ta canza, babu wa da zan iya yadda da shi a wannan duniyar, kuma yadda kike cuɗanya da waɗannan mazan jami'an masu kama da buntsura, ai ba zan yi shedar ki ba. Na yi karatun na san yadda mazan jami'a suke." Ya ce cikin zafi.

"Na shiga uku kaicona! Sai na yi tur da rayuwa matuƙar mijina bai yarda da ni yi ba." Ta ƙarashe maganar tare da sakin razanannen kuka sai kuma ta ɗora da cewa," Sau nawa kake chatting da 'yan mata, a kan gadona kuma magana ta batsa? Wane namiji ka ga na taɓa yin waya da shi ko na kawo shi gidanka?"

"Ke kina ke jina? In ga za ki yi aiki kiyi in kuma ba ki so, sai na ce huta rororo." Ya faɗa tare da jan filo ya rungume.

Kuka sosai ya kubce mata har da sheshsheka.

"Ke wallahi in kika tayar da maƙota sai na yi mugun saɓa miki, domin duk wanda ya tsare ni yana tambayata jikin ki zai gaya miki."Ya faɗa tare da zama a kan gadon wanda ya sa ta yi tsit sai na zuci da take yi.

Kwanciya ta yi nesa da shi tana hawaye. Ganin haka ya ja bargo yana faɗin,"Aikin banza, tura agwagwa a ruwa. Ki riƙe jikinki uban me zan ji."

Banza da shi ta yi ta kwanta tana jan majina.

Kasa haƙura ya yi don ya san ba za ta kawo kanta ba. A hankali ya ja jikinsa ya shiga jikinta tare da rungumota.

Da sauri ta mike zaune, tana kallonsa duk da babu wadataccen haske a cikin ɗakin.

"Na sha gaya maka ka daina irin wannan domin ba ɗabi'a nace na musulmi. Annabi ya horar da mu kafin aikata sunna mijinta gabatar da abin taɓi. Ko ba ka gabatar ba ya kamata ka tashe ni. Faruk, kuma ni ma mutum ce ina buƙatar mu gabatar da soyayya ba wai ka yi gaba gaɗi ba."

"Saboda ba ki da abin da zan shafa a jikinki ne. Ki zauna kina nan za ki ga na auro mace yar duma-duma wacce zan more sadakina."

"Ni ma ba haka ka auro ni ba. Ta zo wane dare ne jemage bai gani ba. Matuƙar za ka yi mata irin rayuwar da kake mini wallahi yadda za ta koma sai ya fi nawa. Kai fa ma'aikacin gwamnati ne, amma sai an yo cefane a gidanka. Hatta man shafewa watarana sai na roƙo. Duk sana'ar da na fara sai ta karye saboda ci da gida. Ba ka da mu da karatun yaranka ba. Ni nake ɗawainiya da su. Wallahi Abban Raihan, ina tausayawa rayuwarka, saboda haƙkin iyalinka da kake ɗauka."
Chapter 2 · 0% Book details