← Book details Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 40

Sashe 8

Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yadda za a yi da kuɗinnan, Ya Ahmad ka karɓe su duka ka ci gaba da nema mata magani, Allah ya ba da lada kana matuƙar ƙoƙari."

"Haka ya kamata ko wane ɗan mai son ya gama da iyayen sa lafiya ya kasance Nasreen. Mama ita ce fatanmu a duniya. Kina ganin Baba bai damu da rayuwarmu ba, kasan kawai ya sani. Sam bai san haƙƙin 'ya'yan da ya haifa ba. In har bamu nema mata lafiya ba wa zai nema mata?"

"Haka ne, Allah ya shirya iyaye masu halinsa ya sanya su gane cewa. Aure da 'ya'ya duk a ranar lahira sai Ubangiji ya tambayeka yadda ka kula da su, kuma Ubangiji ya ce dukkanninku makiyaya ne ranar gobe kiyama zai tambayi kiwon da aka baku. Amma abin takaici da alhini har da zaman makoki WASU MAZAN sun ɗauki rayuwar aure don biyan buƙatunsu sa ba wai ibada ba. Sun mata cewa aure bauta ce ta Ubangiji ne, haka kula da yara duk Allah ya azurtata ya kuma ka ce ka kula da su."

"Haka ne Ya Ahmad, da yawa WASU MAZAN yanxu don buƙatar kansu suke aure ba don bauta ba."

"Allah ya sa su gane, su ɗauki auren a matsayin bauta sai a taru a gudu tare kuma a tsira tare."

"Amin," Ta furta.

"Wallahi tallahi a gidan nan daidai na ke da uban kowa. 'Yan iskan yara matsiyata mara sa mutunci." Suka ji muryar Baba yana faɗin haka daidai lokacin da ya iso ƙofar ɗakin.

Da sauri suka haɗa idanu Nasreen ta kai hannu za ta ɓoye kuɗin da abincin, amma sai dai ba ta yi nasarar ɓoye kuɗin, ban da abincin da fruit ɗin, ya riga ya banko ɗakin babu sallama yana mazurai.

"Haba Baban Ahmad, ya kamata ka daina zagin yaran nan ka san babu kyau haka?"

"Ban yi magana dake ba don haka ki ji da ciwon ki, tun kafin na yi miki tijara. Ba dole na yi magana ba. Ɗan bazan yaron Aminu, na gani ya dawo daga kasuwa ya samu kuɗi, na tare shi ya bani naira dubu na sha shayi, amma ya rantse mini ba zai bayar ba, wai zai biya kuɗin islamiya."

"Haba Baban Ahmad, kai ya kamata ka kula da karatunsa, ba ka biya ba, ya samu kuma zai biya sai ya zama tsiya?"

Harara ya zabga mata jin abin da ta ce,"Ai to laifina za ki gani ko? Ai dama kullum ni mai lafi ne a gurin ki. Yanzu ma na tabbata kun haɗu ne ke da yaranki kuna zagina. Wallahi kin bani mamaki ƙwarai, domin ban san lokacin da kika canza ba. Ace wai da yaran da na haifa za ki zauna kina gulmata?"

"Gaskiya ce ba ka so, amma ba gulman ka muke yi ba. Haƙƙinka da ka kasa saukewa a matsayinka na uba muke magana a kai."

"Ba ni da shi zan yi ma kaina dole ne? Ko sata kike so na je na yi? Ai na riga na gaya muku koya ya yi ta kansa, domin wallahi Allah bai yi ni mai arziki ba, ba zan je na kashe kaina ba."

"Amma ka san ba ka da shi Baba ka rinƙa aure-aure kana tara yara? Duk da yadda rayuwarsu suka zama Allah sai ya tambaye ka."

"To fitsarrare mara kunya! Ai ni na yi mamakin tun da ka na shigo maka yi mini fitsara ba. Ɗan banza wanda ya fitsare ƙafarsa. Sunnar ma'aikin da na ɗanbaƙa, shi ne kake ɓakincikin da ladar da zan samu. Manzon tsira ya ce,"mu yi aure mu hayayyafa ranar gobe kiyama ya yi alfahari da mu."

"Baba, ba irin yaran da kake haifa ba. Kana ganin halin da kake sanya yaranka, saboda ba ka tsaya ka inganta rayuwar mu ba. Jiya fa haka Ashiru ya dawo gidan na yana tangaɗi. Ga Na'ima kwana biyu ba ta kwana a gida ba, kuma ko ajinka hankalinka kwance."

"Au to so kake na mutu? Ai duniya ce duk wanda ya ce lalacewa zai yi ya je duniya ce, ta ishi bagaruwa jima."

"Amma dai kai ka haife su kana da haƙkin ka kula da su." Cewar Nasreen cikin damuwa tana kallonsa.

"Nasreen! Au ke ma fitsarar za ki yi mini? Wai tsaya yaushe kika zo ma cikin gidan nan? Allah ya sa mijinki ya sani, don wallahi ya zo ya yi mini tijara sai na yi mugun saɓa miki, in kuma kika kuskura ya sako ki sai dai ki nemi wani gidan uban. Kin san dai ba za ki yi mini zawarci a gidana ba, domin na gaya muku dama alla-alla na ke na aurar da ku, tun da kuma na samu waɗanda suka ɗibe ku, babu shegiyar da za ta dawo mini gida. Ballantana ta zo mini da 'ya'ya."

Shiru ta yi ta matsa cewa komai, sai hawaye shar suka wanke mata fuska.

"Da ma na san ba ni da gatan da ya fi zaman aurena." Ta furta tana share hawaye.

Ganin babu wanda ya tanka masa, ya ci gaba da kallon da yake yi ma abincin da ayabar.

"Tuni na san cewa ni a gidan nan. Babu mai ƙaunata. Duk ɗan da zai shigo gidan nan sai dai ya kawo wa uwarsa abu, amma ni ba ku da mu da na ci ba ko na mutu oho!"

"Kai ya kamata ka basu, in ba ka basu ba, dole mu nemo ko a wuta mu basu, don kar mu rasa su."

"Ni kuma inna mutu ba ku da damuwa." Ya ce ba tare da ya kalle su ba ya ɗauki ayabar ya ɓare tare da jefawa a baki.

Zama ya yi a gefen gadon yana zare idanu."Wannan abincin na cikin farar robar nan. Tak away ake ce mata ko take way?" Ya ɗauki abincin tare da ɗauke cinyar kazar.

"Ikon Allah masu kuɗi na sha'aninsu." Ya ce tare da kai loma.

"Ke Nasreen, ba dai ke kika kawo wannan abincin ba, domin na san wannan ɗan iskar maƙoƙon mijin na ki ba zai iya ba ki wannan abincin ba. Mara mutunci shekaranjiya na kira shi ya bani bashin dubu goma, amma ƙememe ya ce ba shi da kuɗi. Wallahi bacin bana son ki yi zawarci da saina raba ki da shi na aura mai kuɗi irin mijin Nadiya, saboda shi ina ce ya bani za ki ga ya miƙa mini."

"Ta ya ya zan yi daraja a guri sa Baba, kana zubar mini da mutunci kana cin bashi a gurinsu? Bana haƙuri kawai na ke yi a zaman aure a, amma wallahi zaman gidan yari yafi mini zama da Faruk."

"Kuma ba ki da zaɓin da ya wuce zama da shi." Ya furta tare da kai lomar abincin.

Cikin takaici suke kallonsa tamkar za su rufe shi da duka suke ji. Haƙiƙa ba su yi dacen uba na gari ba."

Tsananin mamaki da ya kama su, ganin yana shirin cinye abincin nan, ya na zuba surutu mara ma'ana.

"Baba, abincin nan na Mama ne domin shi za ta ci ta sha magani."

"Ni ma bani da lafiyar ai. Jiya da na je gurin yaran nan Tukur mai kyamis ya ce yunwa takama ni. In kuma so kuke na mutu shikenan dama na san baku da asara." Ya furta ba tare da ya ƙara magana ba, sai da ya cinye abincin nan tas! Ya tsaki wata mahaukaciyar gatsa yana shafa tunbinsa.

"Yauwa, ku yi wa mahaifiyarmu magana ta cire wannan damuwar banzar da ta sanya ma kaina, saboda ita kanta ta san cewa da ace zan canza halina da tuni na canza, don haka ban ga abin da zai sanya ta sawa kanta hawan jini ba."

Ba tare da sun ce masa uffan ba suka ci gaba da kallonsa.

Har zai fita sai ya dawo ya kalli Ahmad." Ɗan bani naira ɗari biyar na sha ruwan bunu."

"Bani da shi saboda na kashe duk kuɗin a asibiti. Yanzu haka ma akwai maganin da ban siya ba."

"Ai sai ka ba da himma." Ya ce yana harararsa.

"Ke dai na san ba samu zan yi ba, don haka ba zan ɓata bakina ba." Ya ce mata tare da ficewa daga ɗakin.

"Kai halin Baba sai shi. Allah ya shirya mana mahaifinmu."

"Rashin ilimi da sanin darajar aure yake damunsa." Cewar Mama tana hawaye.

Sun kasa rarrashinta su kansu hawaye suke yi. Tun da suka taso suke cikin wannan rayuwar har zuwa girmansa ba ta sake zabi ba.

"Yanzu kin ga yadda za a yi da kuɗin nan. Ki bawa mama, dubu goma ta ije a gurinta, ta rinƙa siyan abinci tana ci. Sannan dubu biyar ki ɗauka ke ma kina buƙatar kuɗin. Dubu uku kuma a bawa Zainab ta je ta biya kuɗin islamiya da hadda."

"To Yaya Ahmad, kai kuma fa? Kana bukatar kuɗi?"

"Kar ki damu da ni. Namiji na ke zan kula da kaina."

"Amma ko dubu biyu ka karɓa."

Murmushi ya yi yana girgiza mata kai, wanda ta tabbatar ba zai karɓa ba tun da ya ce.

"Yaya Ahmad, Allah ya buɗe maka saboda kula da mu da kake yi."

"Amin," Shi da Mama suka amsa har da Zainab.

Miƙewa ta yi da sauri kamar an tsikareta ta ce,"Bari na tafi gida Raihan na can zan biya na ɗauke ta, kuma ban yi abinci ba."

"Har yanzu dai yana nan yana ba ki abinci tazarce ko?" Mama ta tambaya cikin ƙunar rai.

"Ai Mama, yadda yake mini ya wuce tazarce. Girki ɗaya zan yi sai kuma gobe. Ga shi ba ya isanmu sai dai na haƙura."

"Allah ya kawo mafita ki kammala karatun ki. Ko koyarwa kika samu a makarantar gashin kai, za ki samu sauƙin rayuwa."

"Amin Allah kuma ya sa ya yarda."

"Inda uban kuturu ya yi kaɗan kenan." Cewar Ahmad da sauri.

"To, mai za ka yi masa? Matarsa ce fa. Kai dai Allah ya sanya ya amince ɗin dai."

"Hmmmmh! Aiko da wuya, gurguwa da auren nesa."

"Ashe ko za a kwashi 'yan kallo ni da shi. Don yadda na ke kashe kuɗi a karatunta dole ta amfani da shi."

"Allah ya sa." Mama ta ce tana nishi da ƙyar.

"Mama, na tafi zan dawo in sha Ubangiji ya ƙara sauki."

"A gaida gida na gode, kuma ki gaishe mini da kishiyata."
Chapter 8 · 0% Book details