Sashe 7
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"No matar aure ce ba zai kin kira ba, amma kuwa zan yi mata kyauta ta musamman, domin kamata ya yi gwamnati ta ɗauki nauyinta."
"Gaskiya Yaya."
"Gobe sai ki shirya mune ki zaɓi duk motar da kike so, in kuma na Muhsin da kika na ce sai ya bar miki dama motar mata ya je ya siya."
"No bana sonta, ba ka ga ya je ya ƙuje ta ba?"
"Ok, tom sai ki shirya goben."
" Na gode Allah ya ƙara budi." Tace masa cikin tsananin murna.
"Ina little Marwana?"
"Tun da muka shiga gidan Hajiya, ta ga za ta fita sai ta manne mata, kin santa da son yawo da Hajiya."
"Hajiya da ita ai sai Allah."
"Yanzu kin gama ne?"
"Eh bari na kai mata yaron."
"Ok," Ya ce tare da sanya hannu a aljihunsa ya ciro kuɗi 'yan dubu-dubu har 20k.
"Ga shi a siya masa chocolate."
"Thanks Yaya."
Da sauri ta shiga cikin abin tana nemansa. Ganin ta can a gefe ta ciro jigattaciyar wayarta taba ƙoƙarin kiran Ya Ahmad.
Ba tare da ta ji zuwa ta ba sai dai kawai ta ji maganarta.
"Ga shi zan wuce gida."
Da sauri ta shiga tare da ɓoye wayar a jaka.
"Sannu ya wahalar da ke ko?" Ta yi tambayar tana ƙoƙarin ɗaukar shi.
"Kai haba wane wahala." Ta ce mata tare da miƙa mata kuɗin.
"Ya Damir ya ba wa Musaddik."
Zare idanunta ta yi tana kallon kuɗin tare da haɗiye miyau da ƙyar.
"Kai haba duka wannan uban kuɗin ai sun yi yawa."
"Kar ki damu Yaya zai iya ba shi fiye da haka."
"Gaskiya ba zan karɓa ba."
"Saboda me?"
"Saboda sun yi yawa, kuma daga haɗuwa da ke yau, sai ki yi mini kyautar wannan kuɗin."
"Musaddik ya yi ma kyautar, don haka ya zama dole ki karba, kuma kin san wane ne Ya Damir da kuɗin da yake da shi? Ban ba ki san shi bane." Ta ƙarashe maganar, tare da cusa mata kuɗin a jaka, sannan ta juya ta fara tafiya tana faɗin.
"Sai gobe zan wuce."
A ranta ji ta yi kamar za ta sume ganin kuɗin, domin rabin ta da ta samu irin wannan kuɗin har ta manta."
Miƙewa ta yi ta goya Musaddik sannan ta ɗauki jakarta ta tafi.
A hanya ta ciro wayarta ta kira numbar Faruk da yake zaune a ofis ɗinsa yana waya.
Yana ganin kiran na shigowa, amma bai damu ba ya ci gaba da wayarsa, har lokacin da ya gama, sannan ya kashe tare da sakin wawan tsaki.
"Ko uban me za ta ce mini oho? Ana magana da mata ba ke kamar sandar rake ba ki addabe da..." Maganar ta katse sakamakon kiran da ya ƙara shigowa.
"Wai mene kin addabe ni, ko ke makauniya ce? Tun da kin ga ina waya ba sai ki yi haƙuri ba."
"Ka yi haƙuri kiran ne da mahimmanci zan gaya maka ina son na je na duba Mama jikinta ya tsananta."
"Wannan ne kira mai mahimmanci?" Ya yi mata tambayar cikin tsawa wanda ya sanya ta yi sororo sai kuma ta ce," Mahaifiyata ce fa ba lafiya?"
"To ni ina ruwana in kin so kar ki dawo ba ta shafe ni ba. Kin ga sai na huta da ci da ke." Yana faɗin haka ya kashe wayar tare da ƙara jan tsuka mai ƙarfi ya kashe wayar.
Ranta ne ya ƙara ɓaci, ta kalli wayar hawaye na son zubowa a fuskarta, amma sai ta daure ganin yau rana ce ta musamman, domin ko babu komai za ta taimaka a ciwon Mama.
Tsayawa ta yi, ta sayi lemo da ayaba na dubu ɗaya, sannan ta siya mata gashashshen nama da dubu.
A ƙofar gida ta kusa cin karo da Zainab.
"Ina za ki je kike sauri haka har za ki buge ni?" Ta ce mata daidai lokacin da suka ci karo.
"Oyoyo Anti Nasreen." Ta furta tare da rungume ta tana shafa kan Musaddik.
"Zan siyo ruwan gishiri Mama ce za ta sha. Ta ce jikinta babu ƙarfi."
"Sai kin dawo to."
"Anty kawo shi." Ta ce tana miƙa hannu ta Kwanto mata shi.
"A'a, ki yi sauri ki dawo."
"To," Ta ce tare da shafa kanshi ta ruga da sauri.
Da sallama ta shiga cikin tsakar gidan, da Mama Dije take zaune tana ƙoƙarin hura wuta.
"Yau 'yan boko ne a gidan? Ko da yake dole ki zo tun da tsohuwa babu lafiya." Ta faɗa tana yatsina bakinta.
"Ina wuni?" Kawai ta ce mata ba tare da ta ji abin da za ta faɗa ba ta shige.
Rakata ta yi da kallo ba ta amsa gaisuwar ba.
Ɗakin ta buɗe ta shiga, tare da saurin ƙarasawa, kan lamushashiyar katifar da Mama take kwance.
"Sannu Mama, ya jikin ki?" Ta yi mata tambayar tana daga goshinta da ya ɗauki zafi kamar tukubar mai tsire.
"Yauwa ya gidan?"
WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme.
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43
*WASU MAZAN*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 5
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM

"Yauwa ya gidan?" Ta amsa cikin rawar murya.
"Allah ya ƙara sauki."
"Yaya Ahmad mai ke damunta?" Bayan ta yi mata fatan samun sauƙi, ta juya tana kallonsa tare da tambayarsa hakan.
"Ciwon nan dai nata. Yanzu likitanma ya ce gaba take da zuciyarta ta buga, matuƙar ba za ta cire damuwarta ba." Ya ba ta amsa yana share hawaye.
"Haba Mama! Sanya damuwa a cikin ranki ba shi zai kawo karshen matsalar nan ba. Mama, iya tsawon shekarun da kika yi da Baba ya kamata ki yi hakuri ki rungumi ƙaddararki."
"Ya zan yi Nasreen? A halin da na ke ciki na fi buƙatar mutuwa fiye da rayuwata, domin ban zaɓawa rayuwata da na yarana bango mai kyau ba. Ina dana sanin auren mahaifinku, kamar yadda na tabbata ke ma dana sanin da za ki yi kenan. Na cuci rayuwata wanda a dalilin haka na sanya ki da yaranki cikin halin ƙaƙa na iya."
"Mama, babu wanda ya isa ya tsayawa kansa rayuwa. Kowa da kika ganshi rayuwa yake yi ba tare da ya tsara wa kansa ba. Allah ya ƙaddara shi ne mijinki, kamar yadda babu makawa sai na auri Faruk. Ki kauda damuwa mu rungumi ƙaddara da Allah ya ɗora mana."
Kuka ta fashe da shi ganin Nasreen na hawaye. "Ina tausaya wa makomar rayuwar ki da 'ya'yanki kamar yadda na ke tausaya wa kaina."
"Mu roki Allah kuma mu mai da lamuranmu ga Ubangiji." Ta ce tare da buɗe jakarta ta cire lemu da ayaba da kuma ƙunshi nama.
"Ina kika samu kuɗi? Ke da ake taimaka miki?"
Murmushi ta yi jin abin da ta ce, tana kallon Ahmad da ya kashe ta da ido.
"Ai yau na haɗu da gamdatakar!" Ta ce tare da fito da dubu goma sha takwas ta ɗora a gado.
Zare idanunsu suka yi. Mama cikin ƙarfin zuciya ta miƙa wanda ganin haka ya sanya ta jingina mata filo a bayanta.
Take ta kwashe kaf abin da ya faru ta gaya musu.
"Kin san bana son leƙen rayuwar wasu? Ki tsaya a matsugunin da Allah ya ije ki, domin yawancin masu kuɗi wulakantattu ne."
"Wallahi Mama sai da na ce mata ba zan amsa ba. Kin ga ko abincin da ta siya mana ƙin ci na yi, amma ta kafe na kaiwa yarana gida." Ta ƙarashe maganar tana miƙa mata take away ɗin abincin
"Ga shi ƙila ki samu kici." Ta ce bayan ta ije mata.
"An ya wani abu zai iya shiga cikin nan?"
"Ki daure rayuwa dole sai da abinci."
Gyara.
Nasreen ta ɗauki cokali sannan ta iba tare da kai mata bakinta.
Buɗe bakinta ta yi a hankali ta karɓa."Yauwa Mama, ko ke fa. Allah ya ba ki lafiya."
"Amin," Nasreen ta amsa tare da miƙewa bayan ta karɓi ruwan gishiri ta ta miƙe don ta ɗauki kofi ta jiƙa mata.