Sashe 12
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hankalinta ya tashi jin abin da ta ce."Wallahi ba haka bane. Ya ce zai ba ki presents saboda ƙoƙarin ki. Shi ne na bashi shawarar ya sai mai waya da laptop don kin fi buƙatar su."
"Bana so ki mayar masa ina jin daɗin rayuwata a haka." Ta ce mata amma a ranta ta ji dadi sosai mamakin siya mata abubuwa masu tsada ta yi.
Ga mamaki ta sai ta ga ta gangara gefen titi ta yi parking."Don Allah kar ki yi mini mummunar fahimta. Wallahi bani da nufin tozarta ki. Yayana he is generous and kind, amma in zai ɓata miki rai zan mayar masa." Ta ƙarashe maganar sai hawaye shar a fuskarta.
"Ikon Allah! Wannan Mommy's pet zan ce ko daddy's?"
Murmushin ta yi tare da share hawaye."Brother's pet. Yayana shi ne gatanmu. Mu uku mahaifiyarmu ta haifa. Shi ne ya ɗauki duk wani ragamar rayuwarmu."
"Allah Sarki kamar Yayana dai Ahmad. Shi ne na uku a ɗakinmu, amma shi ne namiji, kuma yake ɗaukar duk dawainiyarmu. Shi ya sanya ni a makaranta yake biyan kudin."
"Ba kina da aure ba?"
"Eh," Ta ba ta amsa sai alokacin ta tuna ɓaranɓaramar da ta yi.
"Allah ya ɗaukashi kamar Ya Damir."
"Amin."
"Yanzu za ki karɓi kyautar?"
"Na gode ki yi masa godiya sosai. Allah ya ƙara ɗaukaka shi."
Amsawa ta yi sai kuma ta sanya hannu a jakarta ta zato dubu biyar."Ki sa kati."
Ta kasa karɓar kallonta kawai ta ke yi." Kar ki ce a'a wallahi Allah ya sanya mini ƙaunarki tamkar 'yar'uwata na jini. Watakila kuma don bani da 'yar'uwa mace ce."
"Zan karɓi wayar da laptop ɗin amma ban da ku..."Maganar ta katse ganin ta ɗauke jakarta ta sanya mata.
Murmushin ta yi cikin farin ciki ta ce,"Na gode Allah ya bar ƙauna."
"Daga yanzu babu godiya a tsakaninmu fatana na yi ƙoƙari lamari. Ya Damir ya tura ni waje na yi masters a can."
"Za ki yi ƙoƙarin fiye da ni in sha Allahu."
Duk yadda ta so ta kaita gida, amma taƙi sai ta kafe ta ije ta a unguwarsu.
Unguwar ta bi da kallon mamaki ganin yawancin gidajen duk na masu kudi ne, saboda za ta iya rantse wa babu gidan talaka a gurin.
"To shi ke nan, Ummu Raihan my regards to her."
Ta amsa mata sannan ta juya ta wuce ita kuma ta kunna motar ta wuce.
Tsayawa ta yi tana duba wayar da laptop ɗin."Ikon Allah! Wayar nan da laptop ɗin nan masu tsada ne, kuma wai sun ba ni kyauta?"
Gabanta ne ya fadi da ta tuna ko mai Faruk zai ce game da kyautar.
Shago ta wuce ta siya indomie, har da ƙwai da madara, sannan ta sayi kati na duba ɗaya ta wuce gida.
Da ta isa gidan sauke Musaddik da yake bacci ta yi. Kwanciya ta yi kan kujera tana hutun gajiya. Bayan ta huta sannan ta shiga kicin ɗin ta girka indomie ta ibarwa Raihan, kafin su dawo islamiya a kawo ta.
Tana zaune a falo har aka kira sallah magariba, daidai lokacin da Raihan ta shigo. Alwala suka yi sannan suka yi sallah.
Ɗaki ta ja su suka koma. Bayan ta kulle ƙofar ta ɗauko laptop ɗin da wayarta. Da ma ta sanya katin da ta siyo
Tana ta danna wayar ta kasa bacci har dare ya yi. Ko da ta ji dawowarsa ba ta damu ba, tun da ta san cewa ɗakinta a kulle yake.
Faruk kuwa tun da ranar da ya siyo mata maganin ta ƙi sha yake jin haushinta. A ranar da ya sanya matuƙar ba za ta sha ba, shi kuma ba zai ba ta abincin ba.
Mamakin inda take samun abinci ya kama shi matukar gaske. Duk da ya san ba ya wuce wannan ɗan'iskan Ƴaƴanta Ahmad.
A yau dole sai ya ganta, don haka ya je ya nemo makullin ɗakin ya sanya a aljihunsa.
Sai da ya shigo ya ci abinci da ya ƙoshi sannan ya buɗe ɗakin.
Jin kiciniyar buɗe ɗakin, ya sa ya ta yi maza ta mike za ta ɓoye wayar, domin har yanzu ba ta san mai za ta ce masa, don ta san ba lailai bane ya yarda. Sai dai, duk ƙoƙarin ta na son yin hakan, kafin ta ɓoye har ya buɗe ƙofar ya shigo.
"Saboda kin mayar da ni ɗan'iska, ba ni da matsayi a gurin ki. Shi ya sa kike kull..."
Maganar ta maƙale masa sakamakon wayar da laptop ɗin da ya gani.
"Ai iyye!" Ya faɗa cikin tsananin mamaki yana kallonta.
"Ke! Gidan uban wa kika samu waɗannan?" Ya yi mata tambayar tare da ɗauka yana kallonta.
Haɗa wayar ya yi da tasa yana kallo, duk da cewa ya san tafi ta sa tsada.
"Nasreen?" Ya kira sunanta cikin tsanani mamaki.
"Na..am,"Ta furta cikin tsananin tashin hankali tana kallonsa tana matsawa.
"Gidan uban wa kika samu waya?"
"En..uhm..e." Ta ce mishi tana zare ido.
"Ta tabbata mazan jami'a kike bi. Shi ya sa kika raina ni, sam ba ki ɗauke ni a bakin komai ba. Ni da matsiyaci a gurin ki duk ɗaya."
Zare idanunta ta yi cikin tashin hankali tare da matsawa ganin yana dumfarota.
"Tsaya ka ji Abban Raihan, wallahi ban taɓa bin wani ɗa namiji ba. Don Allah karka buge n.." Ta yi shiru tare da ƙwala ƙara ganin ya kai hannu ya mangareta.
"To in ba maza kike bi ba uban wa ya baki?" Ya faɗa tare da kai mata wani bugun.
Faruk lafiyarka kuwa? 'Ya mace ba abin duka bane. Tsakanin mata da miji ya kamata akwai kyakkyawar fahimtar da kowanne zai san abin da ɗan'uwansa zai yi. To mu je dai zuwa mu ji yadda za ta kama Ba kwa comments lafiya?🙄🙄 In har ana son posting safe da yamma na ga ruwan comments.
WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme.
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
*WASU MAZAN*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 8
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
"Kyauta yar aji.." Sai kuma ta canza maganar tana cewa,"Ya Ahmad ne ya siya mini."
Ganin yadda ya zare mata ido yana son jin abin da za ta furta, sai ta canza shawara ta ce,"Ahmad? Ƙarya ne domin aikin kanikancin da yake yi, da ci da mahaifiyar da nema mata lafiya, ba zai bari ya siyaiki ba."
"Na rantse da gaske ne ka kira shi ka ji." Ta faɗa cikin muryar kuka.
"Na kira shi na ji uban me? Maza kike bi da aurena kike kula maza? Wannan dalilin ya sa ya har kwana biyar ban baki abinci ba, kuma ba ki damu ba." Ya faɗa tare da cire bell ɗin da ya shiga fuskanta tana ihu.
Ganin yana shirin illantata, ya santa ta yi maza ta faɗa bayi ta rufe ƙofa.
"Ki buɗe ƙofar nan, kafin na buɗe da kaina na yi maganinki."
"Don Allah ka yarda da ni, wallahi ba zan taɓa cin amanar ka ba."
Yaran sun yi tsuru-tsuru, suna kallonsa don Raihan kuka take yi sosai. Duk da cewar sun saba ganin yana dukanta, amma na yau ya ƙazanta.
"Abba, don Allah ka daina dukan Umma." Cewar Raihan tare da kama hannunsa. Ba tare da ya kalli Raihan da take kuka ba ya ce,
"Allah ya kaimu safiya, da asuba zan kaiki gidan na tsare Ahmad, na ji ko shi ya siyan miki." Ya faɗa tare da yarda bulalar.
Saboda tsoron karya dawo a ranar kusan a bayi ta kwana. Ta yi kuka har ta bawa uku lada. Gabakiɗaya jikinta ciwo suke mata. Kwata-kwata ba ta yi tunanin zai ɗauki zafi sosai haka ba, in ya ga ta da su. Matuƙar nadama da dana sani suka cika ta. Tun da ya ce za su je gurin Ahmad, take ta kiran wayarsa ta sanar masa maganar, amma cikin rashin sama wayar ta sa a kashe Ga shi dama shi kadai yake da wayar a gidan.
Kiran sallar asuba ya tashi ya rinƙa buga mata ƙofar ta buɗe. Tsananin mamaki da ya kamata, domin in dai da asuba ne sam baya tashi da wuri.