Sashe 21
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuka kawai take yi ta kasa furta kalami. Ganin haka ya saki tsaki ya fice tare da buga ƙofar. Rintse idanunta ta yi cikin tsananin bakin ciki.
Ta ɗauka wasa yake mata, amma sai ta ga ya kwashi tarkacen da zai kwana da shi ya fice. Kuka take yi tun tana yi har ta ji idanunta sun ƙafe. Ita kanta ba ta san tana da kishi haka ba.
Bayan kiran sallar Isha sai ga kiran Ahmad. Tana ganin kiran ta ki wasu zafafan hawaye sun wanke mata fuska. Da ƙyar ta samu ta tsayar da hawayen ta yi sallama
"Hello Nasreen, da gaske Faruk ya ƙara aure?"
Tambayar da ya yi mata ya sanya ta fashe da kuka. Jin kukan ya sanya shi yarda da jita-jitar da ya ji.
"Haba Nasreen amma kika kasa sanar damu? Wata ƙawar Mama ta sanar mata, don ta san matar da ya aura."
"Ni ma bai gaya mini ba." Ta ce masa cikin muryar kuka.
Jin abin da ya ce sai tausayinta ta ƙamashi. Daga ji ya san tasha kuka. Ƙoƙarin kwantar mata da hankali ya shiga yi. Sai da ya ji ta ɗan saki sannan ya ce,"Wayata babu caji bari na kai shagon Ado mai caji, zan kira ki in na karɓo."
"To Yaya, ka gaida su Mama."
"In Sha Allahu." Ya ce tare da kashe wayar yana mamakinsa.
Mama da ke gefensa tana jin abin da take faɗi. Ganin ya kashe wayar ya sanya ta saki salati. "Kai amma Faruk, ba shi da kirki. Ace za ka ƙara wa mace kishiya, amma ka kasa sanar mata. Haba wannan zaluncin ya yi yawa. Ko taro ta yi ai ta rage raɗaɗi."
Ina zai gaya mata tun da ya raina ƙuranmu? Ya san bamu da abin da za mu kawo mata, da ya san za a kawo mata abin duniya zai gaya mata." Ya karashe maganar cikin ɓacin rai yana tausayin ta.
"Wallahi Baba ya cuci Nasreen." Ya ƙara cewa.
Mama dai shiru ta yi ɗin maganar ma babu amfani sai ɓacin rai.
Tana kwance tana juyi tamkar kasa. Wani irin tsananin kishinsa take ji. Miƙewa ta yi don ta ɗauro alwala ta yi sallah. Don in ba haka ta yi ba wataƙila kafin wayewar gari zuciyarta ta buga. "Ashe haka mata suke ji in aka ƙara musu kishiya?" Ta ce a ranta tana share hawaye.
A bayi wanka ta yi saboda yadda take jin zafi yana keto mata. Tana ƙoƙarin alwala sai ta ji kamar zubowar abu a ƙasanta. Tsoro ta ji din dama tana tunanin ciki ne da ita. Kusan wata uku ba ta ga al'adarta ba. Duk da cewar tun haihuwar Musaddik sai ta yi wata huɗu ba ta gani ba. Wannan dalilin ya sanya ta shiga kokwanto ko ciki ne da ita. Ganin jini ne gabanta ya faɗi. Ta rintse idanunta daidai lokacin da cikinta ya yi wani irin murɗawa.
"Wayyo Allah!" Ta ce cikin tsananin ruɗani. Jin yadda mararta ta ƙulle. Fasa alwalar ta yi ta koma ta kwanta, amma sai bacci ya gagara. Tana kwance tana juyi tana kiran sunan Allah. Ko jirgawa ta ɗauki wayarta ta kasa. Salatin ta ya farkar da Raihan.
"Umma, ba ki da lafiya ne?" Ya ce mata tana kallonta.
"Eh Raihan, ɗauko mini wayata na kira Ya Ahmad, ya zo ya kai kai ni asibiti."
"To," ta ce tare da miƙewa tana tangaɗi ta ɗauko mata wayar inda ta nuna mata. "Umma, in je in ta so Abba?" Ta ce mata ganin yadda take masoso.
"Abba bai kwana gida ba."
"To ki kira shi."
"Raihan ba zai zo ba, yau ya samu wacce ta fini." Ta faɗi hakan tana hawaye.
Ba ta fahimci komai ba sai ta yi shiru tana kallonta.
Yau pages ɗin masu kishiya ne a fito masu kishiya a gaya mana abin da aka ji da mijinki zai ƙara aure. Akwai wacce mijinta ya ɓoye mata kamar Nasreen? In akwai wane mataki ta ɗauka? Ga Nasreen duk da ba ta zama da shi na daɗi, amma zafin kishi ya sanya ta yi ɓari. Tana ta kiran ango yana can gurin amarya ya ji sabon guri🙈🙈🙈💃💃 to ko zai zo ya taimaka mata ko kuma amarcinsa zai sha da amaryarsa Rashida? Faruk sau a sausauta don ma bazawara ce 😆😆 makar ta duk da na yi da tsayi in kuka tashi kaina zan iya antayo muku next page don mu ji yadda za ta kaya. Aci gaba da comments ina murmushi ina shan ganta ina karantawa. Na gode muku sosai Allah ya bar ƙauna.
WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme.
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43
*WASU MAZAN*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 13
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
Raihan ba zai zo ba, yau ya samu wacce ta fini." Ta faɗi hakan tana hawaye.

Da ta kira wayar sai ta ji a kashe. Tunawa da ta yi ya ce ba shi da caji, ya sanya ta yi tunanin ƙila bai karɓa ba.
"Wa zan kira?" Ta yi wa kanta tambayar cikin tsananin tashin hankali, domin har ta fara fita hayyacinta. Maman Muwaddat ta faɗo mata. Da sauri ta nemi layinta, amma cikin rashin sa'a wayar a kashe. Juyi take tana salati. Ƙoƙarin miƙewa ta yi don ta je ta ƙwankwansa musu, amma da sauri ta kwanta jin ba za ta iya tafiya ba.
Kwanciya ta yi kan gadon ta ce,"Wash Allah zan mutu!" Kuka take yi sosai ta sadaƙar mutuwa za ta yi.
Wayar ta ƙara janyowa ta nemi layinsa don ganin za ta mutu. A lokacin yana kwance ya rungume amarya Rashida da take ji kamar za ta mayar da shi ciki, musamman ganin kalar soyayyar da yake nuna mata.
Kiran ya shigo daidai lokacin da ya ƙara rungumota ya haɗa bakinsu. Jin su suke a wata duniyar. Haƙiƙa ji yake yau ya samu matar da yake so, wacce za ta yi masa duk abin da yake muradi a makwanci. Ganin yadda ta cire kunya take nuna masa kalar basirar ta, wacce ya yi farincikin da samun mace mai irin basirar. Sun yi nisa su shiga wata duniyar. Ana ta durzar amarci ba tare da ya kula da kiran Nasreen da yake ta shigowa ba.
Ko da hankalinsu ya dawo jikinsu, Rashida ba ta barshi ya rintsa ba domin so take ta nuna masa ya samu kalar macen da take fata, don a daren cinye shi ne kawai ba ta yi ba.
Jin sa yake cikin aminci ya rinƙa takaicin kansa da ya zauna ya auri mace Bahaushiya, wacce ba ta san komai ba, sai ta ci ta tara masa yara. Ai matan yare sune ka aure su zaka more aure, babu kunya a baka kalar rayuwar da kake so.
Ganin ba zai ɗauka ba, ya sanya ta daina kiran tare da takaicin kiransa. Kishi da tunanin halin da suke ciki yanzu ya ƙara rikita jikinta. Ganin za ta mutu ya sanya ta nemi layin Marwana.
Marwana dake zaune a falon Damir tana kallo. Little Marwana kwance a cinyarsa tana shafa kanta. Tun da cikin ya girma sai Hajiya ta sanya ta dawo gidan. Sosai cikin ya girma ga kumbura da take yi. Likita ya sanar da su ba za ta iya haihuwa ba, dole sai dai a cire cikin. Ɗin haka ya shawarci Damir da zarar cikin ya shiga wata tara za a yi mata C.A. A yanzu haka shirye-shirye tafiya suke yi zuwa waje, don har ya yi musu viser lokaci kawai yake jira.
Wayarta a hannunta bayan sun gama waya da masoyinta. Har ta ije sai kuma ta ɗauka tana kallon hotunan da ya turo mata.
Ganin kiran Nasreen ya tsorata. Kallon agogo ta yi tana mamakin dalilin da ya sanya ta kira ta. Tunawa da ta kirata da rana, amma ba ta ɗaga ba, ya sanya ta danna kiran tana dariya.