Sashe 24
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɓata fuska ta yi jin ba ta da lafiya."Allah ya ba ta lafiya." Ta ce tare da zama kan kujerar.
Kallonta ya rinƙa yi cikin sha'awa, yana ji ina ma ace duka yaronsa ne.
Ita ma kallo ɗaya ta yi musu ta ɗauke kanta. Ba ta ce komai ba, har ya yi mata sallama ya fice. A gidan gaba ya sanya su duka, har da Little Marwana da ta na ce da ita za a je.
A hanya sai da ya tsaya ya yi musu soyayya sosai, sannan suka tafi asibitin.
Marwana bayan ta gama waya da shi likita ya kira ta. Binsa a baya ta yi cikin murna dama burinta ta ganta.
Tana kwance kamar gawa. Idanunta kawai ke motsi. Tsananin mamaki ta ke yi yaushe har ta samu ciki ya girma ba tare da ta sani ba?Addu'a ta yi wa Allah da ya fita, domin ta san tsaf Faruk zai iya cewa ba cikinsa bane, ganin ko ita ba ta san da shi ba.
"Marwana!" Ta furta cikin rawar murya sai kuma kuka.
Ƙarasawa ta yi kan gadon ta zaunar da ita."Jiya kin tsorata ni! Na ɗauka mutuwa za ki yi." Ta ƙarashe maganar cikin hawaye tana rike da hannunta.
"Ni na na ɗauka mutuwa zan yi Marwana, ina su Raihan?"
"A gidan Yaya Damir suka kwana yana hanya zai kawo su."
Kuka ta fashe da shi."Na gode da kika taimake ki. Haƙiƙa kin zamo mini 'yar'uwa. Bacin ke jiya da na mutu. Faruk zai kashe ni sam baya ƙaunata. A jiya aka ɗaura masa aure ba tare da ya gaya mini ba.Yana can da amaryarsa a hotel suna amarci, saboda mahaifiyarsa ta rantse sai ya yi mini kayan faɗar kishiya, kuma na yi taro. Na kira wayar da ya fi a ƙirga, amma bai ɗaya ba. Amarci ya fi masa lafiyata, ya san ko na mutu ba shi da asara."
"Aure?" Ta yi mata tambayar cikin tsananin mamaki.
"Aure ya ƙara ya gaya mini ba ni da ƙima da matsayi a zuciyarsa. In na ga dama na zauna da shi, in kuma bana buƙata yanzu ya san ya yi aure."
Jin abin da ta ce sai ta kama hannunta "Please ki haƙura da Faruk ki canza sabuwar rayuwa."
" Ina son mijina ina fatan na rayuwa da yarana. In har na rabu da shi ba zai bar mini su ba. Kuma ba ni da fatan da zan riƙe su a gidanmu. Bayan haka ina son shi jiya tsananin kishinsa ya sanya na yi ɓari.".
Jin abin da ta ce ya sa ta ji haushinta matukar gaske!"To zama za ki yi ya yi ta wulaƙanta ta ki? Nasreen ina son ki ƙwaci yancin kanki tun da ƙuruciyarki, kar sai kin tsufa ya tsotse kallon mangwaro ya huta da ƙuda."
"Ba za ki gane halin da na ke ciki ba. Rayuwata tana cikin gaba kura, baya siyaki. Zaman gidanmu shi ma ba mafita bace, sannan ina tausayawa rayuwar su Raihan bana son su ta so a hannun matar uba. mahaifiyata ta sha wahala sosai a hannun matar babanta."
Shiru kawai ta yi ta kasa cewa koma. Ta buɗe baki za ta yi magana, daidai lokacin da aka ƙwankwansa ƙofa. Sanin Damir ne ya sanya ta ce,"Yes come in." Bayan ta sanya mata hijabinta.
Cikin natsuwa ya yi sallama ya shigo. Yana rungume da Musaddik da ya fara bacci a kafaɗarsa. Idanunsa a kan Marwana, domin haka nan ya ji sam ba ya son ya kalle ta. Haka zuciyarsa ta kitsa masa kuma ya bi, don samun maslaha.
"Ya Damir, welcome." Ta ce tare da ƙarasawa ta kai hannu za ta karɓi Musaddik.
Idanu ta zuba masa da nufin ta yi masa kallo ɗaya, amma sai ta kasa ɗauke idanunta. Wani irin abu mai ƙwarjini ta gani a cikin idanunnasa. Zuciyarta ya fara bugu fiye da wanda take yi. Rintse idanunta ta yi tana son kauda idanunta gare shi, amma ta kasa kallon sa take cikin tsananin sha'awar ina ma ace shi ne mijinta, mahaifin 'ya'yanta. Ganin yadda ya rungume shi cikin tsananin so da ƙauna. Namiji Kyakkyawan gaske ingarma da shi ga shi dogo sosai, mai faffaɗar ƙirji. Shigarsa da kamarsa suka sanya ya ke ɗauke da wata irin charisma dake sanya masa ƙima da daraja ga duk wanda ya kalle shi.Wani irin ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi, tare da ta'awizi a zuciyarta, domin ta san sheɗan yake ƙoƙarin ƙitsa mata surarsa a zuciyarta.
"Haƙiƙa matarka tafi ko wace mace sa'a, duniya samun miji kamarsa ba ƙaramin tagomashin bane. "Ta furta a cikin zuciyarta.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta saki tare da rintse idanunta. Da sauri suka kalle ta har da shi da bai yi ninya ba. Gabansa ya yi matuƙar faɗi. Ganinta mace kyakkyawar gaske! Mai manya idanu masu tsananin ƙwarjini. Ƙara kallonta ya yi, duk da ba ta da lafiya, amma hakan bai hana bayyana kyawunta ba. Jikinsa ya yi sanyi, sanyin da ya hana shi jirgawa. Ganin hakan ya sanya Marwana ta ƙarasa gabansa ta karɓi Musaddik ta kwantar da shi. Yana tsaye a gurin kamar gunki yana kallonta da ta fuskar da kanta ƙasa, tana wasa da yatsun hannunta.
"Ya Damir, ga ƙawata wacce na ɗauke kamar 'yar'uwata Nasreen. Nasreen, ga Yana Damir, wanda ba ni da kamarsa. " Ta ce ganin ko wannensu ya kasa motsi.
Ɗago idanunsa ya yi, ya ƙara kallonta daidai lokacin da, ita ma ta yi nasarar kallonsa. Zuciyarsu ta buga a tare.
"Sannu ya jikin ki?" Ta ji muryarsa mai kama da sarewa yana faɗin haka.
"Da sauƙi," Ta ce cikin sanyin murya, don bai ji abin da ta faɗa ba, don kawai yana kallon bakinta ne.
"Ya jikinta mai likitan ya ce?" Ya yi wa Marwana tambayar haka yana mai da idanunsa gareta.
"Jikin da sauki, amma kuma ya ce sai an ƙara mata jini."
"Ok, ba matsala bane, amma kin kira mijinta?"
"A'a, tun jiya dai."
"Sai ki kira shi, ya san halin da matarsa take ciki, duk inda ya je ai dole ya dawo."
Kallonsa ta yi sai hawaye shar.
Marwana hannunsa ta kama suka fita."What? Kina nufin mijinta aure ya ƙara ya tafi ya barta a cikin wannan halin?" Ya yi mata tambayar cikin damuwa.
"Eh, yana hotel yana cin amarcinsa."
"Kai wannan mutumin ba abinda imani. Matarka na cikin wani hali a kira ka, amma ka kasa amsawa saboda kana amarci? Akwai abin da ya fi iyalinsa mahimmanci?"
"Yaya sai ka yi mamaki wallahi auren bai gaya mata ba."
"Ikon Allah! Amma WASU MAZAN suna matuƙar ba ni mamaki."
Shiru suka yi kowa da abin da yake tsaƙawa a ransa. Can ya sauke numfashi ɗauko wayarta ki kira shi. Ba musu ta juya ta ɗauko wayar. Ta yi masa kiran duniya, amma bai ɗaya ba.
A lokacin sun ta shi daga bacci kenan. Saboda gajiyar da suka yi, babu wanda ya iya motsawa har aka kira sallah aka idar. Sai gurin tara saura suka ta shi. Ganin bai yi sallah ba, hakan bai dame ta, domin ita ma ba ta damu da sallar ba.
Bayan sun yi wanka sannan suka yi sallah. Matsawa kusa da shi ta yi tare da janyo shi ta haɗa bakinsu, tana masa wani irin salo.
Janye jikinsa ya yi tare da ture ta."Please, baby ki bari na huta, kuma yunwa na ke ji."
Jin abin da ya ce ta ɓata fuska ta matsa can ta zauna. Ganin ta ɓata rai ya janyota. Babu yadda zai yi, haka nan ya biye mata, amma shi kansa ya san yana buƙatar hutu. Kamar yadda lamarin ya faru cikin daren juya haka suka gudanar. Sam babu tsari na addini suka rinƙa ihu. Ita ta fara dama haka yake sosai ya biye mata. Ya sha fama da Nasreen kan hakan, amma ta ƙi tare da yi masa nasihar hakan ba koyarwa bace ta addinin Musulunci, sai dai Yahudu da suka kawo wannan salon, ɗin su ɓata tarbiyarmu da tsarin Islama.
Da ƙara ya iya ɗaukar wayarsa ya sanya aka kawo musu abinci. A nan ya ga tarin kira sau babu adadi. Tsuka ya ja tare da jifa da wayar.
"Shashashar banza! Ba ina gaya miki da ma akwai lokacin da za ki yi sani sani ba? Wato tun jiya idanunki sun raina fata? Ai dama za ki gani. Baƙincikin kishinta sanya kin kasa bacci sai kirana kike yi. Ai kin riga kin makaro, tun da na samu macen da za ta yi mini duk abin da na ke so. In har ba ki takatsantsan ba, walllahi saf zan yarda ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda." Shi kaɗai yake ta maganar.
Rashida ta kalle shi."Babya magana kake?" Ta yi masa tambayar tana masa wani irin kallo tare da hura masa kiss.
"Ni da wancan shashashar ce. Kira yafi sau ɗari." Dariya ta yi ba ce komai ba tana kallon sa.
Ya buɗe baki zai yi magana sai kiranta ya shigo. Kin ɗagawa ya yi har aka kira sau bakwai. Ganin ta na ce sai ya kai hannu ya ce,"Bari na ɗaga na ji uban me za ta ce mini."
Carab ta riƙe hannun sa."Ni baby, kishi ne kawai yake damunta. Ba ta son mu ci amarci. Ka shareta, don ni na fi son mu yi amarcinmu anan. Ka san matan Hausawa suna da kishin tsiya."
"Ok, babyna yadda kika ce haka za a yi. Ai ni in har za ki iya sarrafa ni a gado kin riga kin samu kaina har da ƙafafuwana. Ita shashashar sai dai ta kwanta kamar gunki. Kai matan Hausawa sam ba su yi ba."
Dariya ta yi jin abin da ya ce, tana masa salon da take son ya bambanta ta da matan Hausawa.
"Ikon Allah! Har yanzu ba ya amsa Calls din." Marwana ta ce cikin takaici.
"Ungo wayata kira shi da nawa." Ya ce mata yana miƙa mata wayar.
Karɓa ta yi tare da cire password ɗin. Ta danna numbobinsa a wayar. Cikin mamaki ta ga ya ɗaga wayar da sallama. Kallon junansu suka yi cikin mamakin rashin ba ta daraja.
Ta san zai iya tuna muryarta sai ta miƙa masa wayar. Ƙin karɓa ya yi."Ki yi magana kin san ba shi da mutunci, zai iya mini wata fassarar, kuma bai kamata na yi masa magana."