← Book details Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 40

Sashe 36

Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ƙyar suka samu ta yi shiru tana faɗin."Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Domin ta yi kukan har idanunta sun bushe. Babu hawaye sai zafi da ƙunci da zuciyarta yake.

Ga dai Ahmad ya ɓace ya barsu da jimamamin rashinsa. Shi kansa Baba ɓacewarsa ta buge shi, saboda sai da ya ɗauki lokaci kafin ya dawo natsuwarsa. Da fari har sallah yana kiyaye a kan lokaci, musamman in ya tuna yadda Ahmad yake zubar hawaye a duk lokacin da ake kiran sallah yana zaune. Da ga baya kuma sai ya watsar ya koma ruwa. Dama ita sallah ginuwa take a jiki, haƙiƙa duk wanda ya yi sakaci da ita sai wani ikon Allah.

Ganin kukan ba shi da amfani, ya sanya suka maida lamuransu ga Allah. Kusan kwana uku take sauka tana fatan Allah ya bayyana shi.. Kullum gani take kamar zai yi sallama. kamar zai dawo daga tafiyar da ya yi. Kullum hotonsa take ɗauka tana kallo hawaye na zubar mata. Haka Damir ya ji a lokacin da matarsa ta mutu?" Ta yi wa kanta tambayar cikin damuwa, saboda ga shi ita tana tunanin zai dawo, amma Allah kaɗai ya san halin da zuciyarta take ciki."Idan kuwa haka ne, haƙiƙa dole ya tsane ni ya yi fatan kar ya ƙara fatan ganin mai sunanta.

Damuwar yadda rayuwarta zai cigaba take tunani. Ta san cewa rayuwarta ta shiga cikin gararin, amma duk abin da zai faru ba za ta koma gidan Faruk ba, musamman da ya ɓace ko zuwa bai yi ba.

Tun ɓacewarsa na ɗanye a lokacin da tai wata biyu. Yau ga shi ya zama wata huɗu rayuwa ta yi musu ƙunci. Kullum sai sun yi kukan rashinsa, musamman gurin kula da abin da za su ci. Wayar da Marwana ta ba ta har ta sayar da ita. Ya rage laptop ɗin. Ita ma ganin halin tsotsan tsamiya da suke yi, ya sanya ta siyar, sanin babu wanda zai biya mata kuɗin makaranta ta cire kuɗin ta ije. A lokacin da aka gaya mata kuɗin da za a siya ta yi mamaki ƙwarai. Ashe ba ƙaramin kuɗi ya kashe gurin siya mata ba. Bayan ta cire kuɗin suka fara sana'ar cikin gida. Da cinikin take samu ta je makaranta ta kuma ɗan yi wasu abubuwan na makaranta.

Damir zaune kan farar kujerar a bakin ruwa idanunsa lumshe. Zuciyarsa ɗauke da tunani barkatai. Tun ranar da suka baro Nigeriya, har yau ka kasa sakin jiki kamar yadda Mommy take so. Kullum ya kwanta bacci sai ta yi mafarkin ya, domin har yanzu zuciyarsa ta kasa daina zargin cewar shi ne ya yi ajalinta. Duk lokacin da ya tuna hakan sai ya ji tamkar zai haɗiye zuciya ya mutu. Ya yi dana sani tafi cikin kwando dubu. A hankali ya buɗe manyan idanunsa ya ɗora su kan Little Marwana, da ke gudu a bakin ruwa tana dariya, Marwana na biye da ita. Kallonta yake yi cikin tsananin tausayawa. Hawaye suka taru a gefen idanunsa."Anya za ta yafe mini kuwa?" Ya tambayi kansa cikin tsananin damuwa. Miƙewa ya yi, yana kallon ruwan da ya kusa mamaye gurin.

Hannunsa ya ji little Marawana ta kama ta riƙe tana faɗin,"Daddy, ka zo mu yi wasan gudu da kai a bakin ruwa, kuma Anty Marwana ta ce in Mommy ta dawo daga tafiyar da ta yi za mu zo tare."

Hawaye suka cika masa idanunsa. Har yau ta kasa fahimtar Batula ta yi musu nisa."Mommy ba za ta dawo ba, domin ta tafi inda ba a dawo wa." Ya ɗauke ta tare da shafa fsskarta yana faɗin haka.

Kallon da ta yi kamar mai tunani,"Daddy, to za ka siyo mini wata Mommy?"

Tambayar da ta yi masa, ya sanya tashin hankali a zuciyarsa."Ba zan siyio miki wata ba, amma na yi miki alƙawarin zan ba ki ƙular da kowace uwa za ta bawa 'yarta."

"No, daddy na fi so ka siyo mini wata." hankalinsa ya ƙara tashi jin abin da ta ce. Ije ta ya yi zai tafi ba tare da ya ce komai.

Hannunsa Marwana ta riƙe cikin hawaye."Ka yafe mini Yaya, har yau ina tuna ni na yi sanadin gushewar farincikinka, ina shiga cikin tsananin tashin hankali. Don Allah ka yafe mini Yayana." Kukan da take masa ya ƙara ninka masa damuwa.

"Sis, ki bar kuka komai ya wuce."

"Karka faɗi haka domin ka canza ka koma kamar ba kai ba, duk lokacin da na ganka a wannan yanayin ina jin kamar na kashe kaina."

"Kar ki damu ki manta komai lokacin ta ne ya yi, sannan bamu da ikon dakatar da mutuwarta."

"Ka yi mini alƙawarin za ka daina sanya damuwa a cikin ranka. Za ka dawo kamar da, yayana wanda na sani yake sani dariya da farinciki?"

Shiru ya yi yana tunani sai kuma ya ƙwace hannunta ya fara tafiya.

Sosai take kuka tana kallonsa har ya yi nisa ya zauna a can gefe.

Duk da cewar sun je gurin domin su sanya shi farunciki, amma haka suka dawo jiki a saɓule.

A lokacin da suka dawo Mommy tana zaune da qur'ani a hannunta tana karantawa. Shigowarsa ya sanya ta dakata, bayan ta kai ƙarshen ayar. Kallon sa ta yi har ya shige cikin ɗakinsa.

Marwana ta zauna kusa da ita tana hawaye."Ya Damir zai koma kamar da?"

"Ni ma na fara tunanin haka, ina ga za mu koma gida kawai, saboda zuwanmu bai yi amfani ba, kullum cikin damuwa, sannan ga campani babu mai kula da shi."

"Haka ne amma Mommy ya kamata mu ƙara lokaci kafin mu koma."

Shiru ta yi ba tare da ta ce mata komai ba.

Ganin wata biyar da ɓacewar Ahmad ba tare da Faruk ya zo ba, ya sanya Baba ya shirya ya je gidansa.

A lokacin yana falo yana kallo shi da gumbiyarsa da take kwance kan cinyarsa. Wasu irin arnan kaya ta sanya, wanda da su gwanda babu. Hakan ba ƙaramin yi masa daɗi ya yi ba, musamman da take da cikar jiki ko ina duk tsoka. Ya tasa ta ya yi ta kallo. Tuni suka fahimci juna game da tsarin iyali. Duk abin da yake so shi take masa, wannan dalilin ya sanya hankalinsa ya kwanta har wani ɗan tumbi ya yi.

"Baby, kamar ana knoking get?" Ta ce masa tare da ɗaga kanta tana kallonsa.

"Ni ma haka na ji." Ya ce sannan ya miƙe ya sanya doguwar riga ya fice.

Ganin Baba ya ɗaure fuska yana kallonsa a wulaƙance."Lafiya?" Ya ce masa yana kallonsa.

"Lafiya lau, ba ka gane ni bane Farukuu?"

"Na gane ka mana ba uban Nasreen ba ne?" Jin tambayar da ya yi masa, ya sa ya jikinsa ya yi sanyi.

"Eh ni ne..."

"Allah ya sa dai lafiya? Kuma ina fata ba tambayata kuɗi ka zo yi ba?"

"A'a Faruk yaron kirki, ba ka san Ahmad ya ɓace bane?"

Ɗan jim kamar bai sani ba sai kuma ya kalle shi."Na ji wataƙila kunya ta sanya shi ɓoye kansa ya ga ba shi da kuɗin da zai iya biyana."

"Allah dai shi ya barwa kansa sani fatanmu ya bayyana shi."

Ba tare da ya amsa ba sai motsi da bakinsa da ya yi.

Ganin bai tanka ba, sai ya gyara tsayuwa ya rasa abin da zai ce, amma dai ya daure cikin rashin ƙwarin gwiya ya fara magana da cewa," Da ma na zo kan maganar matarka..."

"Ba kun ce za ku kai ni kotu ba? Ina jiran a yi mini sammaci sai na je na amshe kuɗaɗena kashe."

"Ka bar wannan maganar ai wanda ya tsaya mata ya ɓace. Ni kuma ka san dai ba zan goyi bayanta ba, dole gidan ka za ta dawo. Don ba za ta yi mini zawarci da yara ba."

"Na san ya ɓace, ina jiran na ga inda za su samu wanda zai tsaya musu ne. Tun da an gaya mini wanda yake hure mata kunnin ya bar ƙasar"

"Duk haka ba ta ta so ba. Ka san dai Nasreen da auren ka ba za ta kula wani namijin ba?"

"Ok, ka yarda da ita kenan? Tarbiya ka bata da har za ka shede ta?"

Shiru ya yi jin abin da ya ce sai kuma ya nisa,"Faruk duk wannan maganar ba ta taso ba, ka yi hakuri ka zo ka ɗauki matarka..."

"Na zo fa ka ce?" Ya katse shi yana faɗin haka, sai kuma ya girgiza kansa ya ɗora da cewa,"In har ba za ta dawo ba, sai ta yi ta zama har Mahadi ya bayyana. Ai ni wallahi rage mini aiki ta yi, don yanzu hankalina kwance na samu mace mai ladabi da biyayya."

"Yanzu dai duk zancen tone-tone bai ta shi ba, kai da Nasreen kin riga kun zama ɗaya. Ka yi haƙuri ko don tausayin yaranka."

"Tun da ba ta tausaya wa kanta ba sai ta ci gaba da zama ba. Na san dai rayuwarta a garari zai ƙare, wanda yake yi mata ƙaryar zai tsaya mata kunya ta sanya ya gudu."

"Ni zan wuce in sha Allahu za ta dawo yau."

"A'a ban shirya ta dawo yau ba." Ya ce yana kallonsa saboda ya yanke shawarar ya je ya gasa mata maganganu.

"Ka bari zan zo sai mun yi magana da ita na gaya mata dokokin gidana."

Jin abin da ya ce ya yi shiru ya kalle shi zai tafi.

Faruk ya raka shi da idanu ya ɓule, ya san kallon da yake masa ya ba shi kuɗi."Wallahi ai daga yau ka daina cin sisina. Yar ka ce yanzu na samu wacce ta fita, don inta ga dama ta zauna in ba ta buƙata ga hanya nan." Ya furta yana nuna hanya.

Da ya shiga cikin gidan har lokacin tana zaune. Ganin ransa a ɓaci ya sanya ya dawo kusa da shi."Hala 'yan maula ne?" Ta yi masa tambayar haka, don ta san a tambaye shi kuɗi ne ya fi ɓata ransa.

"Baban wannan mara mutuncin Nasreen ne ya zo, wai na je na ɗaukota. Ni kuma na gaya masa ai ba ni na kaita ba."
Chapter 36 · 0% Book details