Sashe 20
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har ana ɗaurin aure Faruk bai sanar mata ba. A ranar ta ga ya yi wanka ya ɗauki gayu ya fice daga gidan. Tana jin mutane suna kiransa a waya. Bayan ya fita ta fashe da kuka sosai. Tabbas ta tabbata yau za a ɗaura masa aure, don ko bai gaya mata ba, wankar da ya yi ya isa ta fahimci aure zai ƙara.
Tana zaune a gurin tun da ya fita ta kasa motsawa. Kuka take yi sosai tana tausayin kanta, ganin tana rayuwa da mutumin da bai san darajar ta ba. Tunanin zaman da za su yi da amaryar take yi.
Saboda bai sanar mata ba ya sanya babu wacce ta gayyata, don ko 'yan gidansu ba ta sanar musu ba. Kamar yadda bai gaya mata ba, duk wanda ya tambayeta sai ta ce ba ta da labari. Ita ma amarya kawai ta gani. Duk yadda take da Ya Ahmad ta kasa da ar masa, domin ta san babu abin da zai iya mata sai dai ta tayar masa da hankali.
Bayan fitarsa babu jimawa aka ƙwanƙwasa get. Sai da ta wanke fuskarta, sannan ta je ta buɗe get ɗin. Ganin Yarsa Asiya ce ya sanya ta yi murmushin yaƙe."Sannu da zuwa." Ta ce mata ba tare da sun haɗa idanun ba.
Turus ta yi ganin yadda idanunta suka kumbura."Nasreen lafiya? Ko kishin ne ya sanya kika koma haka?" Ta ce mata tana kallon harabar gidan ganin babu alamun ana taro.
Kasa magana ta yi saboda zubowar hawaye. Matsawa ta yi ta ba ta hanya. Ganin haka ya sanya ta tura ƙofar ta shiga ciki.
"Ke Nasreen, lafiya ban ga ana taro ba? Ko ba yau bane ɗaurin auren?"
Tambayar da ta yi mata, ya sanya ya ji kamar ta kwasa mata mari. Ashe ta san da bikin ba ta gaya mata ba, in shi ya ƙi sanar da ita, yadda ta ɗauke ta 'yar'uwa ai ya kamata ta sanar mata. Dangin miji kenan.
"Ni ma ban san zai ƙara aure ba, hasashen haka kawai na ke yi, don bai gaya mini ba." Ta ce tana hawaye.
"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Amma Faruk ya cika tantiri. Wannan wane irin rashin dalci ne? Wallahi tun da ya je mini da maganar ƙarin aure nan, na yi masa tatas da na ga ba zan iya hana shi ba, tun da addini ya ba shi dama. Sai na ja masa kunne kan ya yi adalci ya sanar miki kuma ya yi miki kayan faɗar kishiya."
"Hmmmmh!" Kawai ta ce tana share hawaye.
Ganin ba ta ce komai ba sai ta kalle ta ta ce,"Nufin shi haka zai ƙara auren ba tare da kin yi taro ba?"
Ba ta ce mata komai ba don bata dan me za ta ce mata ba.
"Bar ni dashi bari na kira sa ɗan ƙwal uba." Ta ce cikin takaici. Ciki suka shiga ta zauna, daidai lokacin da kiran wayar ya shiga. Kira har sau bakwai ta yi masa ba a ɗaya ba.
Tana zaune cikin takaici tana jin kamar ta je ta duke shi, sai ga shi ya kira ta."Hello Anty Asiya, an ɗaura na zama mijin Rashida." Ya ce mata cikin tsananin farin ciki.
Maganar da ya yi ta ji kamar ya soka mata allura."Innnali wa inna ilahir raju'un!" Ta furta sai hawaye shar! Da sauri ta share don karta gani, amma ta makara domin idanunta na kanta.
Tausayi da kunyar abin da ya aikata, ya sa ta ta lailayo ashra ta yi masa."Ashe ba ka da kirki Faruk? Kan me za ka ƙara aure ba tare da ka sanar da uwargidanka ba?"
"Haba Anty Asiya, saboda wannan kike so ki ɓata mini ranar farinciki? Ina gaya mata mai za ta yi? Na san dai iyayenta talakawa ne ba su da abin da za su yi mata. Ballantana na sa ran za a kawo mata wani abu. Zuwa kawai za su yi su ɓata mini gida su cinye abinci."
Takaici da haushi da ya sanya ta ce,"Uwarka na ce Faruk! Wai mai yasa ba ka da mutunci ne?" Ta ce masa cikin tsananin kunyar abin da ya faɗa.
"Kin ga Anty ina cikin taro zan kira ki." Ya ce yana ƙoƙarin kashe wayar.
Kafin ta yi magana ya datse wayar. Dafa Nasreen ta yi da take kuka sosai, jin abin da ya ce."Ki yi haƙuri kin ji wallahi dole ya dawo, sai ya yi miki kayan faɗar kishiya kuma sai ya san bai kyauta ba." Ta ce tana mamakinsa.
"Ki barshi kawai, fatana Allah yasa ya zaɓo wacce za mu zauna lafiya da ita."
"In sha Allahu ina fatan haka nima, kuma ki ci gaba da haƙuri. Kin san dole in aka ƙara wa mace kishiya ta yi haƙuri."
"To," Ta ce tana share hawaye. Zama ta yi tana ta bata baki har ta ji kishin ya ragu. Wayarta ta ɗauka ta kira mahaifiyarsa ta zayyane mata komai. Sosai ranta ya ɓace ta ce,"Ki bar ni da shi, wallahi dole ya ɗaya tarewar nan, har sai ya yi mata kayan faɗan kishiya, kuma ya ba ta abin da zata dafa ta tara mutane. Wannan wane irin rashin mutunci ne? Ga duka ga mari ga tsinka haka. Ko da cinya ya barta suka yi taro ai za ta ji daɗi."
"Faruk ba ya kyautawa Mama." Ta ce mata jin abin da ta ce.
"Ki ƙyale shi zan kira shi. Mika mata wayar."
Ba musu ta miƙa mata ita kuma ta karɓa. Sosai ta ba ta baki sannan ta yi mata alkawarin ta sa ya shi dole ya yi.
Bayan an gama ɗaurin auren aka je dinner. Daga dinner a mota sai da ya ji kamar zai karɓi haƙkinsa, saboda yadda ta rinƙa masa. Shi kan yasan ya zu ya yi aure, tun kafin ta shigo cikin gidansa. Da ƙyar suka rabu bayan ya fara more sadakinsa.
A hanya Mama ta kira shi. Da ya ɗaga ya gaishe ta. Tatas ta yi masa sannan ta kafa masa cewar dole a ɗaga tarewar har sai ya yi mata. Ransa ya ɓaci sosai jin abin da tace. A ransa ya sanya hakan ba zai faru ba, wai gurguwa da auren nesa. Yadda ya ƙosa a kawo ta ya more sadakinsa. Don shi kadai ya san zumuɗin da yake yi. Sauri yake yi ya koma don sun ce za su kawo kaya.
Cikin ɓacin rai ya shiga cikin gidan. Bai samu ya yi mata rashin mutunci ba, saboda masu kawo kaya da suka iso. Nasreen na ganin kayan ta tabbatar da auren na sa. Ɗaki ta koma har suka gama jera kayan a ɗayan ɗakin da ya gyara. Da yake gidan four bedrooms ne. Nata sai na yara da kuma na sa. Ɗaya tun da ya fara burin aure ya rufe shi. Ya zama za su rinƙa sharing falo da kicin.
Bayan an gama jera kayan ya shigo cikin ɗakin. Tana zaune da carbi a hannunta tana ja. Ɗayan hannun kuma tsaƙon da Marwana ta tura mata na assignment da ta yi take dubawa, duk da cewar hankalinta ba shi sosai a kan wayar.
Ganin ya shigo ya sanya ta miƙe."Saboda na aure ki ba zan yi aure ba, ko kuma ke kike aure na da dole sai na gaya miki zan ƙara aure?" Ya yi mata tambayar yana zare idanunsa.
Miƙewa ta yi cikin tsoro tana kallonsa sai kuma hawaye."Abban Raihan, ni fa matarka ce ina da haƙƙi a kanka, ya kamata ka gaya mini."
"Ashe da sauƙi tun da matata kike ikona. Na ɗauka uwata za ki ce?" Ya yi mata tambayar yana zare mata idanu.
Jin abin da ya ce ya sanya ta share hawayenta tare da zubowar wasu."Look Nasreen, kin san yanzu ba ɗaya bane da da, saboda ina da wata matar, ba zan jure rashin mutunci ba, don ban ga amfanin ki a gidannan ba, sai dai ki ci ki yi kashi ki tara mini yara?"
Jin bin da ya ce ta kalle shi,"To mene auren Faruk? Ai samun zuriya shi ne albarkar aure."
"Ni ba wannan bane albarkar aure. Na huta da matata ta yi mini biyayya, kuma ta so duk abin da nake so."
Kallonsa kawai ta yi cikin rashin hayyaci ba tare da ta ce masa komai. Ganin haka ya sa shi harararta.
"Kin san Allah ba zan ba ki ko ƙwandala ki tara mini gayyar talauci ba, kin hana na tare da amarya saboda baƙin kishinki. Hotel za mu je don yau babu abin da zai hana ban more sadakina ba, kuma kika ƙara sanar wa Mama waje za ki yi sai ki je ki yi zawarci, na ga uban da zai ƙara aurenki, a yadda kika yangwaɗe babu mamora a jikin ki, dubi fa yadda kika dawo komai ya shafe, gabakiɗaya kin haɗe da ko'ina, kuma kike kishin kar na auri wata?
"Kallonsa ta yi cikin tsananin mamakin abin da ya furta."A haka ka aure ni Faruk? Lokacin da ka aure ni a haka na ke? Kai da kanka ka sha yabon surata, ita ma kanta wacce za ka auri za ta dawo haka matuƙar za ta yi ciki ta haihu, kuma ka kasa ba ta kulawar da ya kama."
Kallonta yake yi kamar wata mahaukaciya."Sai aka ce miki mahaukaci ne ni da zan barta ta haihu? To ki jira ki zuba idanu ki ga yadda za mu more rayuwa, saboda ban aure ta ba don ta haihu."
"In har tana da hankali ba za ta yarda da hakan ba, saboda babu macen da za ta yarda da wannan. So kake ta kare rayuwar ta ba tare da ta haihu ba? Akwai sufa da yanayin rayuwar da mutum yake shiga, dole yaranka kawai za su taimaka maka."
"Ki bar ni in na shiga lokacin sai ki zo ki gaya mini haka. Ina da kuɗi da kyau sam ba zan tagayyara ba."
"Ba komai kuɗi suke yi ba kuka dukkaninsu masu wucewa ne." Ta ce masa tana kallon sa.
Tsaki ya ja yana harararta."Na dai gaya miki sai ki san yadda za ki zauna a cikin gidan nan. Don wallahi in har kika yi gigin da na sake ki, ba za ki taɓa samun miji irin na."