Sashe 35
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme.
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242
*WASU MAZAN*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 20
Tana kwance Mama ta shigo, da shinkafa da mai da ya ji ta da girka."Nasreen, lafiyarki lau kuwa?"
"Mai kika gani Mama?" Ta yi mata tambayar, tare da miƙewa tana gyara Musaddik da yake shan nono.
"Gani na yi kin tashi sukuku da ke,kuma kin ƙi zuwa makaranta. Ko kina so ki koma gidanki ne?"
Jin tambayar da ta yi mata ya ɓata ranta."Haba Mama, yanzu har za ki iya mini wannan tambayar? Na koma gidansa ai sai ya yi bandana."
"To na sani? Kin san ance tsakanin mata da miji sai Allah, ko kin ga wahalar da muke ciki ba za ki iya zama ba."
"Kar ki manta a cikinta na tashi, sannan babu abin da na manta. Ko da sonsa zai kashe ni na haƙura da shi. Ballantana Faruk ba shi a gabana. Mafarki na yi mara daɗi, kuma na kasa gane komai."
"Ban da abin ki mafarki ba gaskiya bane, in har ki yi addu'a babu bin da zai faru sai alkhairi."
"Na yi Mama."
"Shikenan Ubangiji ya kare mu."
"Amin," ta ce tana kallonta.
Har ta ɗaga labulen za ta fita sai kuma ta kalle ta."Yayanki ya ce zai kira amma shiru. Ɗazu kin kira shi wayar a kashe."
"Eh, wallahi sai gwadawa na ke yi, ma bari na ƙara kira." Ta ce tana kallon wayar.
"Yauwa wayar ta shiga." Ta ce cikin murna, amma har ta gaji da jira ba a ɗaga ba.
"Ki bari an jima mu gwada wataƙila ya sanya wayar a caji."
"To," Ta amsa.
Har ta miƙa zata fita aka kira wayar. Gabanta ya tsinke a maimakon ta yi farincikin ganin kiransa.
"Assalamu alaikum Yaya." Ta ɗauki wayar cikin mutuwar jiki tana faɗin haka.
Amsa sallamar aka yi jin murya da ba nasa ba, gabanta ya yanke ya faɗi."
"Ina mai wayar?" Ta yi maganar cikin ruɗu.
"Wace ce take kira?" Tambayar ya sanya ta zauna cikin tsananin tashin hankali.
"Nasreen ce ƙanwar mai wayar, don Allah yana ina?" Ta ƙarashe tambayar cikin ruɗani.
"Ya za ki kira ni kuma ki tsaya kina tambayata? Ya ƙarashe maganar cikin tsawa.
Sororo ta yi jin tsawar da ta yi mata, sai kuma ta furta."Innalillahi wa inna ilahir raju'un! A cikin zuciyarta.
"Yayane yake da wannan layin, ya tafi neman kuɗi ne zuwa kudu. Don Allah ka haɗani da shi, in yana kusa in kuma yar da wayar ya yi ka gaya mini."
Tsaki ya yi yana faɗin,"Wayata ce wannan kuma layina ne, kar ki ƙara kira na."
Jin abin da ya faɗa hankalinta ya tashi."Mai ya faru da Ya Ahmad, ya aka yi layinsa ya zo gurin wannan mutumin?" Irin tarin tambayoyin da suka cika kwanyarta kenan, har ta kasa aiki bisa ƙa'ida.
"Mama," Ta kira sunanta cikin rashin hayyaci tana jin kanta yana juyawa, tamkar ana murza sitiyarin kan motar da aka ƙure mata maneji.
Ƙarar ya sanya Mama shigowa, da sauri tana tofar da lomar shinkafar da ta kai baki."Lafiya Nasreen, Faruk ne ya sake ki?"
Kallonta ta yi kamar wacce ta taɓu."Mama wayar Yaya Ahmad na kira, wani ya ɗauka yake gaya mini wai wayarsa ce." Ta furta cikin tashin hankali.
"Kai anya ki kira numbarsa wani ya ɗauka. Ina ga dai ki sake dubawa, wataƙila ba numbarsa kika kira ba."
Jin abin da Mama ta ce sai ta yarda. Da sauri ta ɗauko wayar cikin ruɗani, domin ta tabbata layinsa ta kira."Wallahi numbar sa ce Mama. Haba ya za a yi na kasa gane numbarsa Yayana, da na haddace a kaina."
Ganin yadda ta rikice sai Mama ta kamata ta zaunar. "Natsu ki ƙara kiransa insha Allahu zai ɗauka Ahmad yana nan lafiya, jikina yana ba ni haka." Ta ce cikin ƙarfafawa duk da cewar zuciyarta na bugu.
"To Mama," Ta ce tare da fara danna wayar hannunta na rawa.
Kallonta ta yi cikin damuwa ta ce,"Na ƙara kira ya kashe wayar."
"Nasreen don Allah ki natsu Ahmad yana lafiya, duk ina yake zai kira. Addu'ar da na ke masa, Allah zai kare shi."
Ɗaga mata kanta ta yi ba tare da ta furta kalami ba. Mafarkin da ta yi ya dawo mata. Tunani take yi in ba shi ya za ta yi.
Duk da Mama ta ce ta bari zuwa an jima ta kira, amma haka ta rinƙa kiran waya ba ta shiga. Ganin dare ya yi sai hankalinsu ya tashi.
Da ƙyar bacci ɓarawo ya kwashe su. Da asuba kiran farko ta tashi ta ƙara kira, amma har lokacin wayar a kashe.
Tun suna jiran kiransu har suka fara shiga damuwa. Ganin an kwana biyu sai Mama ta shirya ta je gidan ogansa. Yadda ta tarar da matarsa cikin damuwa ya tayar da hankalnta ƙwarai.
"Wallahi sai dai mu yi addu'a, saboda ni ma ina ta kiran numbar Baban Intisar a kashe "
"Ikon Allah! Ko mai ya faru?" Ta ce cikin damuwa.
"Bamu sani ba sai dai mu yi addu'a."
"Addu'a ya zama dole. Allah ya jishe mu alkhairi."
"Amin,"Ta ce tare da sauke tagumi.
Nasreen da take tsaye tana zubar hawaye. Ta kasa cewa komai. Tunani take inda yake. Wane hali yake ciki? Da kuma tunanin dalilin da ya sanya layinsa yake hanun wani.
"Don Allah ga numbata in kin ji wani labari ki kira ni." Ta ce mata cikin damuwa.
"To in sha Allahu kuma mu ci gaba da kiran ƙila kuma rashin caji ne."
"Allah shi ya barwa kansa sani da su."
Sallama suka yi mata suka dawo gida. A ranta sun kasa bacci sallah suke yi suna roƙon Allah. Nasreen kuka take yi tana addu'ar Allah ya bayyana shi.
Ganin an kwana uku babu labarin da ya sanya ta tari Baba da maganar cikin damuwa. Kallonta ya yi jin abin da ta ce."To Amaduu yaro ne da za ki tashi hankalinki? Yana nan watakila bai samu damar kiranki bane."
"Ni dai na damu da halin da yake ciki."
"To mu jira iya wata ɗaya suka ce za su yi mana."
"To shikenan Allah ya bayyana mana su."
Fita ya yi daga gidan ita kuma ta tashi ta shiga ɗakinta.
Ganinta zaune a ƙasa tana shatatan hawaye ta yi tagumi ya sanya ta ƙaras kusa da ita."Don Allah ki bar sa wa kanki damuwa, mu yi addu'a kawai. In sha Allahu lokacin da suka ina za su dawo."
"To Mama Yaya Ahmad shi ne na ke gani nake jin daɗi, in har babu shi rayuwa ta zata munanta."
"Akwai Allah ki yi addu'a." Ta ce mata cikin tsigar rarrashi. Haɗiye kulan da yake son kumbce mata ta yi.
"Bari na yi wanke-wanke."
"To maza ki yi ki ɗora abinci."
Tun daga ranar suka cigaba da addu'a, kuma kullum sai sun kira layinsa, amma wannan mutumin ne, daga baya sai ya yi blocking ɗin su. Kafin wata ɗayan sun yi shi cikin tsoro, firgice da ruɗani. A ranta da wata ɗaya ta yi, sun shiga cikin fargabar ko zai dawo, amma shiru har aka ƙara kwana uku babu Ahmad babu ogansa. Lamarin sai ya firgita shi. Shi kansa Baba hankalinsa ya tashi matuƙar gaske. Cikin tashin hankali aka sanya cigiyarsu, amma shiru babu labarin su tamkar malam ya ci shurwa.
Iya tashin hankali wannan ahali sun shige. Kuka Nasreen take yi cikin damuwa ta ce,"Ya Ahmad shi ne gatanta yau kuma ya nace babu shi babu labarin sa. Na shiga uku Allah ka bayyana mini Yayana. Kuka take tana sumbatu taba faɗin kalaman da basu kamata ta faɗin ba Ganin haka Anty Binta ta kamata ta zaunar da ita. "Nasreen ki bar kuka ki yi hakuri kar ki yi saɓo, in sha Allahu Ahmad zai bayyana."
"Saboda me za ki hana ni kuka? Bayan kin san daga yau na rinƙa yi har ƙarshen rayuwata. Ya Ahmad shi ne gatanta kuma ya tafi ya bar ni." Sai ta ƙara fashewa da gigitaccen kuka.
"In sha Allahu za a gan shi mu cigaba da addu'a da sadaka." Mama ta ce zuciyarta na ƙarfafa mata yana raye.