Sashe 17
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kama hannunta ta yi ta riƙe jin abin da ta ce."Haƙiƙa kin wuce matsayin ƙawa a gare ni sai dai 'yar'uwa. Ina fatan Ubangiji ya bar mu tare."
"I will do anything for you Nasreen. Soyayyar ki Allah ya saka mini, saboda yadda na ke jin ki tamkar Hajiya ta haife ki."
Daga nan gida suka wuce sai da ta kai ta har unguwarsu, sannan ta yi parking don ta sauka."Zan yi masa magana domin ba zan iya jure ganin yana dukanki ba, zan gwada watakila ya daina."
Fita ta yi daga motar sanna ta leƙo ta windon motar tana kallonta ta ce,"To shikenan, tun da kin na ce sai na yi miki fatan alkhairi Allah ya sa ya daina, saboda Ni kaina zan so na samu 'yanci a gidan aurena."
"Zan gwada kuma zai daina in sha Allahu."
"Ina fatan haka sahibata." Ta ce tare da ɗaga mata hannu.
Makaranta innsha Allahu yau zan yi posting safe da yamma a cigaba da surbubuɗo comments ❤️❤️❤️❤️💃💃💃💃
WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme.
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43
*WASU MAZAN*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 11
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
Kamar yadda ta yi mata alkawarin cewar za ta same shi. Har ofis ɗin shi ta je. Farouk zaune da waya a hannunsa yana chatting da amaryarsa to be.
Tsaddaden murmshi yake saki fuskarsa ɗauke da annuri. Cikin nishaɗi yake sakin murmushi yana jujjuyawa kan kujerar da irin mai juyawa nan.
Da ya ga chatting ɗin ba zai gamsar da shi ba, kiran wayar ya yi. Daga ɓangaren da ya kira, aka saki wani lallausar murmushi bayan ta yi sallama.
Shi ma murmushin ya sakin mata, yana jin kamar ya zaro ta cikin wayar.
"Ni fa gani na ke kamar da wasa sanya ranar da aka yi mana. Wallahi na zaƙu na shigo gidanka a matsayin mata, na nuna maka tsantsar kula, domin uwargidanka sai ta raina kanta. In ban da shashanci ace ta samu miji kamar ka, kuma ta kasa kula da kai?"
"Hmmmmh! Ni kaɗai na san halin da na ke ciki, saboda matata shashasha ce. Wallahi halin da na ke ciki, da zan gaya miki sai kin tausaya mini. Sam ba ta iya gyara kanta ba, kuma ba ta san yadda ake tattashin miji ba."
"Ba ka da matsala Hubbyna, domin ni zan share maka hawayen da matarka ta kasa share maka."
"In har kika ɗauke mini damuwata, ni kuma zan zamo miki miji abin alfahari, saboda Nasreen sai ta raina kanta. Zan barta da yara ta yi ta fama da ɗawainiyarsu. Ni kuma na kula da ke sarauniyar zuciyata."
"Duk abin da kake so ka samu babyna. Za ta sha kallo, don babu kalar soyayyar da ba zan yi maka ba, ita kuwa sai ta yi ta zama da gidadancinta."
"Kar ki damu masoyiyata, zamu ci duniyar rayuwar aurenmu da tsinke."
Wayar suka ci gaba da yi da musayar kalamai. Kalaman da ya kamata da wanda bai kamata ba, suka rinƙa faɗa wa junansu. Daga bisani suka yi sallama, bayan ta yi masa alkawarin turo masa da zafafan hotunan da ta ce masa ta ɗauka.
Suna gama wayar ta tura masa da hotunan. Kallon hotunan yake yi yana murna da ya samu mace wayayyiya, ba irin matarsa da ba ta san komai ba sai gidandanci.
Yana cikin kallon hotunan, Marwana ta ƙwanƙwasa ƙofar cikin fargaba, don ba ta san yadda za su kwashe ba.
Da sauri ya amsa tare da ba da umurnin shigowa.
Cikin siriyar sallama ta shigo cikin ofishin. Farouk ya miƙe bayan ya amsa sallamar da sauri yana kallonsa.
Miyau ya haɗiya da ƙyar yana mata kallon ƙurulla. Idanu ya zuba mata kamar zai lasheta. A zuciyarsa tunani yake yi kamar ya taɓa ganinta.
"Ba ka gane ni ba ko?"
"Eh, wallahi amma kamar na taɓa ganinki." Ya ce mata cikin tashin murya yana mata wani kallo ƙasa-kasa.
"Da ma na yi tunanin ba za ka gane ni ba, saboda sau ɗaya ka taba ganina."
"Eh, gaskiya ba lailai na gane ki ba. Daga ina baiwar Allah? Saboda da kika shigo na ɗauka 'yan matan hurul ain ce ta faɗo duniya.
Haushi da takaicin abin da ya faɗa suka sanya ta murmushin dole." To ba ita ba ce, domin ni mutum ce kamarka." Ta furta a gajarce tana gyara zamanta.
"To ai dole mutum ya yi tunanin haka, saboda kyawu ki da zubin jikin ki."
"Ƙawar matarka Nasreen ce." Ta furta masa tana kallon sa jin abin da ya ce.
Lokaci guda fara'ar fuskarsa ta kau. Ƙara ɗauke fuska ya yi."Ok, mai ya kawo ki ofis ɗina?" Yadda ya yi maganar, ya sanya zuciyarta harzuƙa don sam ba ta da hakuri.
Faruk kuwa, ji ya yi ransa ya ɓaci matuƙa, domin ya ɗauka tarkonsa ya kama kurciya.
Ganin ya yi shiru, ya sa ya ta ƙara gyara zama ta ce,"Na zo kan kyautar da na yi wa matarka Nasreen?"
"Ke dakata! Ya katse ta yana faɗin haka sannan ya ɗora da cewa,""Nasreen matata ce kuma ina da ikon na zaɓa rayuwar da na ke son ta yi..."
"Ka yi haƙuri ba ni da nufin na yi kutse a cikin rayuwar ku, amma don Allah. Ka ji tsoron Allah, ka san cewa Allah yana ganin rayuwar da kuke yi kai da ita, kuma zaman aure ba zaman bauta ba ne. Wallahi ni na yi mata wannan kyautar, ba tare da ta roƙe ni ba, kuma a tunaninta farinciki za ka yi, saboda maƙiyinka ba zai taba..."
"Ke! Fitar mini da ga ofis." Ya furta cikin tsananin fushi yana nuna mata hanya."Kin san Allah? In har kika ƙara gigin tako mini har ofis, sai ka wulaƙanta rayuwarki."
"Ba ka isa ga wulaƙanta rayuwata ba, saboda bacin darajar da Ubangiji ya yi mini. Ba ka kuma san ni waye ba? In har Kasan Damir Hussain Gamawa ba za ka yi gigin nuna mini ɗan yatsa ba."
Idanunsa ya zare lokaci guda ya ji zufa na keto masa. Tsananin mamaki ya kama shi tare da tunanin yadda aka yi Nasreen har ta ƙulla abota da ita. Haƙiƙa sanin ita ko wace ce, ya yi matuƙar razana shi sosai.
"Wane ne a duniya bai san Damir ba yaro matashin mai tashen nera. In har kuwa ƙanwarsa ce za ta iya mata kyautar da ya fi haka.
"Ina dole na raba ta da ita, domin shigowa wannan zuriyar a rayuwar Nasreen tamkar arziki ne ya shigo a cikin rayuwar su Nasreen gabakiɗaya." Ya furta yana share zufan da ya tsatso a goshinsa.
"Ba na zo na yi maka barazana da arzikin Yayana bane, don ka daina wulaƙanta matarka. Na zo na gaya maka zaman aure ba wasa bane, ko shirin Film da za ka rinƙa tozarta matarka, kuma duk zaman da kuke yi a ranar gobe kiyama, sai Ubangiji ya tambaye duk wanda ya cuci wani a cikinku, saboda iyayen Nasreen talakawa ne hakan bai zama hujjar da za ka rinƙa wulakanta rayuwarta ba. Ina rokon ka da Allah ka ji tausayinta ka daina cutar da rayuwarta."Ta ƙarashe maganar tare da ficewa daga ofishin.
Jaɓar ya zauna yana share zufan da take kwararo masa. Idanunsa ya zaro yana kallonta da ta rufe ƙofar da ƙarfi, har sai da ya rintse idanunsa zuciyarsa na bugu.
Wani irin kishi da baƙin ciki, sosai ya ji na ganin mutanen da Allah ya haɗata da su.
Miƙewa ya yi, da sauri ya fice daga ofishin zuciyarsa na bugu, saboda magungunta sai kuwwa suke masa a kansa.
Nasreen na kwance a falo, tana kallon Raihan da take ta tsalle-tsalle a falon tana murmushi.
Jin hon ɗin motarsa, ya sa ta tashi da sauri don ta buɗe masa get, tare da mamakin abin da ya dawo da shi da wuri.
Bayan ta buɗe masa get, ya shigo ta kalle shi ganin yadda ya shigo babu fara'a. Gabanta ne ya buga sosai, saboda ta san hushin a kanta zai sauke.