← Book details Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 40

Sashe 26

Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"I will do everything for you little sis." Ya ce tare da rintse idanunsa.

Ba tare da ya motsa ba har aka gama iban jinin. Yana kwance sai da ya tabbatar da ya huta ya miƙe. Sai bayan an kammala iban jinin, sai tsoro ya kamata ganin yadda ya koma. Tunawa ta yi da yadda yake komawa in ka gama. Tsoro da firgice ya sanya ta kusa hauka. Sam ta manta, son ƙawarta da tausayi sun sanya ta manta halin da ɗan'uwanta zai shiga."

Ganin yadda idanunsa suka birkice sai ta kalle shi, tare da kama shi da sauri cikin rawar murya ta buɗe baki ta ce,"Ya Da..."

Hannunsa ya ɗaga nata yana jin yadda kansa ke juyawa, abubuwa na rabuwa nasa gida biyu."Kar ki damu son ƙawarki ya sanya kika manta da halin da yayanki zai kasance and I will do anything for you."

Kallonsa ta yi, yana murmushi daidai lokacin da ya shiga ciki. Abin da ya ce mata kamar magana ya daɓa mata.

"Ya Damir, wallahi na manta ba ka sha ta daɗi, in har aka ibi jinin ka."

Murmushi kawai ya y, yana jin yadda kan shi ke juyawa, komai na rabuwar masa gida biyu.

"Don Allah ka bari na kai ka."

Idanunsa ya buɗe ya ɗora kanta sai ya ga kamar uku-uku yake ganinta, amma saboda ƙarfin hali ya ce,"Don't Bother ki kula da ita."

Shiru ta yi tana fargabar Allah ya sanya kar wani abu ya faru da shi, domin Allah kawai zai raba ta da Hajiya lafiya.

Tana kallon yadda yake tuƙin cikin mutuwar jiki. Ta san abinda lafiya, in har ya ce zai yi, to dole sai ya yi. Wannan dalilin sa ya ba ta ja da tsawo ba.

Ganin ya fita daga harabar asibitin, sai ta shiga ciki don ta yi mata sallama, kuma ta yi mata transfer na kuɗi, ko za a bukata kafin ta dawo.

A lokacin da ta shiga tana kwance a cikin zuciyarsa, tana girmama karamci irin na su. Tana kwance idanunta rufe hawaye yana ganganrowa Ahmad yake mata wa'azi yana kwantar mata da hankali.

"Zan je gida na dawo. Na yi miki tranfer na kuɗi a wayarki, ko ana son wani abu kafin na dawo."

Kallonta suke yi sun kasa magana."Mun gode Allah ya ƙara buɗi." Ahmad ya ce mata.

Ita kuwa sai hawaye tana kallonta. Ƙarasawo ta yi kan gadon ta shafa kanta."Ki kula da kanki kuma ki ci abinci. Zan je gida na yi wanka na dawo."

"Na gode Allah ya saka da alkhairi."

"Don't mention." Ta ce tare da juyawa ta fara tafiya. Kallo suka bita da shi har ta fita.

A hanya yana tuƙi yana haɗa hanya. Da ƙyar ya samu ya isa gida. Ko parking bai gama ba, ya samu ya ja hannun Little Marwana suka shiga cikin gidan.

Batula ta taso ta tare shi tana faɗin,"Ka daɗe fiye da yadda na yi tsammani."

Ajiyar zuciya ya ja ya kalle ta cikin rashin hayyaci. Tsoro ya ba ta ganin yadda idanunsa suka dawo.

"Lafiya mai ya faru da kai?" Sharab ya zauna kan kujera yana saukar da numfashi.

"Ba komai." Ya ce mata yana kallonta.

Tsoro sosai ya ba ta ganin yadda ya koma."No, akwai abin da ya faru."

"Na ce miki ba komai..." Ya fara maganar cikin fushi zai mike, amma sai jiri ya kwashe shi ya fadi ƙasa.

Ganin haka ta sa ya ihu, tana girgiza shi tana kiran sunanshi, amma ina idanunsa sun ƙafe. Jin ihu ta ya sanya Baba Azumi ta sheƙo don ta ɗauka haihuwar ce ta taso. Ganinsa kwance babu numfashi tana girgiza shi sai ta ruga waje ta kira maigadi. Da ƙyar suka sanya shi a cikin mota.

Wayarta ta ɗauka ta kira Hajiya ta sanar mata suna asibitin. Hankalinta ya tashi matuƙar gaske! Ta shiga tambayarta.

"Lafiya mai ya faru? Na kira shi ya ce mini yana asibiti, zai zo gidana in ya dawo. Dama ba shi da lafiya ne? Saboda da na kira shi kamar ya ce mini dubiya za shi." Jin tambaye da take mata cikin ruɗani ya sanya ta ce,"Ni ma ban sani ba, ya dawo mini kamar ba shi da lafiya sai kawai ya faɗi." Ta karashe maganar cikin kuka.

"Ina Marwana?"

"Tana asibiti ƙawarta ce babu lafiya shi ne suka kaita tun jiya da daddare."

"Ƙawarta?" Ta yi mata tambayar cikin tsananin mamaki, tana tunanin wace ƙawar ce.

"Eh, ita da shi suka kaita asibiti don ta yi ɓari tana zubar jini."

Kanta ya kawo wuta ta tuna da Nasreen. "Ok, ma za ku kaishi asibitin gani nan sai na ji abin da ya faru."

"To Hajiya sai kin zo." Ta ce tare da kashe wayar tana kallonsa. Kuka take yi sosai tana girgiza shi.

Sun shiga cikin asibitin ta buɗe ido sai kuma ya fara jijjiga ya ƙara sumewa. Tsananin tashin hankali ya ƙara kamata. Dafe cikinta ta yi da yake juyawa.

Marwana tana tuƙi zuciyarta na bugawa na halin da yake ciki. Dana sanin iban jinin ya fi kwando masaki. Ta san yau Allah kawai zai raba ta da Hajiya, domin ko mai za ta ce mata ba za ta fita ba, daga ƙarshe ƙalubantatarta za ta yi cewar ƙawa tafi shi matsayi, da har zai sanya halin da take ciki ya sa ya ta manta halin da zai shiga.

Tana ƙoƙarin karya kwanar gidansa kiran Hajiya ya shigo. Saboda tsananin tsoro har parking ta yi kafin ta ɗaga wayar.

"Marwana?"

"Na'am," Ta masa cikin rawar murya jin yadda ta kirata.

"Mai ya samu yayanki ya sume kuma wace ƙawarki kuka kai asibiti?"

Tambayar da ta yi mata ya tsinkar da zuciyarta."Ya sume?" Ta yi mata tambayar cikin tsananin tashin hankali.

"Ya ina tambayarki kina tambayata? Kina ina ne?"

"Um, eh, ina kwanar shiga gidansa." Ta ba ta amsa cikin rawar murya.

"To ma za ki dawo asibiti don yana can sai ki yi mini bayani." Ta ce tare da kashe wayar.

"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Na shiga uku!" Ta furta bayan ta yi jifa da wayar ta yi reverse ta nufi asibitin.

A lokacin da suƙa karasa da shi aka kai shi asibitin.

"Innalillahi ba yanzu muka ibi jininsa ba?"

"Jini?" Batula ta tambaya tana zare ido. Duk da cewar, ba ta san cewa yana shiga cikin yanayin ba in har aka iba, amma ta yi mamakin abin da ya sanya aka iba.

Tana ƙoƙarin tambayarsa daidai lokacin da Hajiya ta karaso. "Ina Damir ɗin mai ya faru da shi?"

"Ban sani ba yana ciki likitan dai ta ce mini jininsa aka..."

"Ji mene ?" Ta yi mata tambayar tamkar zata zauce.

Ganin ta firgita ya santa ta ce,"Eh, jininsa aka iba haka suka gaya mini."

"Saboda me aka ina mai aka yi da shi?" Ta yi tambayar daidai lokacin da Marwana ta shigo, jin tambayar da take yi wa likitocin ta santa ta tsaya tana zare ido.

"Wata petien da suka kawo da daddare wacce ta yi ɓari aka sanyawa jinin Damir?"

Mamaki ya cika Hajiya ta juyo tana kallon Marwana da ta gama tsurewa."Petien? Wai mai yake faruwa Marwana? Ko kun fara yin abu ba tare da na sani ba?"

Daurewa ta yi cikin rawar murya ta ce," Ƙawata ce Nasreen wacce na gaya miki tana samun matsala.da mijinta. Ta yi ɓari kuma ya yi sabon auren ya tafi ba tare da ya kula ta ba. Shine ta kira ni ta gaya mini. A daren muka je muka ɗauko ta. Yau likita ya gaya mana sai an ƙara mata jini. Mun kira mijinta ya ƙi zuwa shi ne na roƙi Yaya ya ba da jininsa, tun da kalar jininsa take da shi."

Kau ta ji ta wanke mata fuska da mari."Ashe shashasha ce ke? ba ki da hankali. Saboda wata sai ki nemi kashe ɗan'uwanki?"

Kuka take yi sosai cikin muryar kuka ta ce,"Hajiya ki gafarce ni wallahi na manta cewar yana shiga cikin wannan yanayin."

"Saboda me za ki tuna, tun da wata banza can ta fi shi matsayi." Ta yi mata maganar tana hararar ta

Matsawa ta yi zata kara marinta, daidai lokacin da likitan ya ce su shiga ɗakin da yake. Batula da ba ta a cikin hayyacinta jin an ƙarawa wata mace jinin mijinta. Idanun ta suka rine da kishi. Ranta ya ɓaci laifinsu ta gani, domin in har da bai amince ba, babu yadda za a yi a iba. Tuna waya da laptop ɗin da ya siya mata wanda sai Marwana ta gaya mata da suna hira, amma bai taɓa gaya mata ba, duk da cewar sun yi alkawarin ba za su rinƙa ɓoyewa junansu komai ba.

"Son matar aure yake yi?Ta yi wa kanta tambayar cikin tsananin tashin hankali! Sai kuma ta ƙara tambayar kanta da cewa," Wannan dalilin ya sanya har ya ɗauki yaranta suka kwana a gidansa, kuma ya kasa bacci ya rinƙa kula da su. Why mijina? Mai ya sa za ka yi ƙoƙarin sanya na daina yadda da kai" Ta ji zuciyarta ya yi mata tambayar da har sai da gabanta ya faɗi.

Rintse idanunta ta yi, tare da fita cikin ɗakin zuwa inda ta ji an ce an kwantar da ita. Nasreen tana kwance har yanzu hawaye yake bin ƙuncinta. Kamar yadda ta ga 'ya'yanta dama ba ta yi tunanin mummuna ba ce. Tana kwance tana rintse idanunta har ta gana kallonta ba tare da ta san ta shigo ba.

Fita ta yi zuwa cikin ɗakin da yake kwance. Kansa ya dafe yana kallonta sai kuma ya ƙara suma.

"Wallahi Marwana in har kika yi sanadin da na rasa Damir sai kin gwammce kin bi shi lahira." Kuka take yi tana girgiza shi tana kira sunasa"Yaya ka tashi don Allah Karka mutu."

Hajiya fita ta yi da sauri, zuwa ɗakin da Nasreen take kwance. Ganin haka ya sa ya Marwana ta bita."Don Allah Hajiya kar ki tozarta su, wallahi ba su da laifi kan lamarin laifine. Don Allah kar ki yanke ƙawancen da muke fatar mutuwa kawai za ta raba shi."

"Ko mahaifiyarki ce sai na wulaƙanta ta."

Da sauri Nasreen ta buɗe ida ita jin abin da matar take cewa.Ahmad shi ma miƙewa ya yi yana zare ido.
Chapter 26 · 0% Book details