← Book details Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 40

Sashe 18

Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sannu da zuwa Abban Raihan." Ta ce masa tare da matsawa gaban motan, tana jiran ya fito don ta ɗauki kayan da ya siyo.

Kallonta ya yi tare da jan tsuka ya shiga cikin falon.

Sororo ta tsaya tana kalonsa har ya shige cikin gidan. Idanunta suka kawo ruwa, ganin ita da miji babu maganata arziki kullum cikin faɗa da hushi.

Yana zaune ta yi sallama ta shigo hannu ta riƙe da leda. Ƙarasawa gabansa ta yi, ta ije tare da juyawa za ta shiga cikin ɗakinta.

Farouk ya bita da idanunsa cikin damuwa. Tsoro da fargaban abin da zai faru, da rayuwar ta in har ta ji gaba da hurɗa da Marwana suke damunsa.

"Ina ba zan bari ta ci gaba da hurɗa da waɗannan family ba, dole na raba su." Ya ce yana girgiza kansa.

"Nasreen," Ya kira sunanta daidai lokacin da za ta shiga cikin ɗakinta.

"Na'am," Ta amsa tare da dawowa gabansa ta tsaya.

Mugun kallo ya watsa mata, sai kuma ya gyara zama ya ce,"Na raba ki da wannan yarinyar, amma saboda ba ni da daraja da ƙima a gurinki, sai kika je kika sanar mata da ina cutar ki ta zo ta ƙwayar miki 'yanci, tun da ga ta human right ko?"

Hankalinta ya tashi matuƙa gaya, jin abin da ya faɗa."Idanunta suka suka yi raurau za ta yi kuka.

Sam ba ta ji dadin maganar da ta yi masa ba, saboda ta san cewa da ma babu abin da maganar zai jawo mata, sai wata damuwar.

"Wallahi ban aike ta ba kuma.." Ta kasa ƙarashe maganar tana in'ina.

"Ok, ita ce ta ga ya dace ta zo ta yi mini fitsara da rashin kunya ko? Saboda kin ba ta labarin rayuwar aurenmu ko?"

"Ka yi hakuri ni ban gaya mata..."

"Dallah! Rufe mini ba ki shashashar banza." Ya ce mata tare da miƙewa cikin ɓacin rai yana kallonta.

Ganin yana matsawa, ta fara ja da baya cikin tsanannin tsoro.

"Abban Raihan, don Allah ka yi hakuri karka buge ni." Ta ce masa cikin raunin murya, tare da sa hannu ta kare fuskarta, don ta san zai iya wanka mata mari.

Kunnenta ya kama ya riƙe da ƙarfi." Wallahi Nasreen, kin ji na rantse miki. In har ba ki rabu da wannan yarinyar ba, Allah sai na wulakanta rayuwarki. Bana son hurɗa da ita, in har kika ce za ki ci gaba da hurɗa ita zan yi mummunar saɓa miki, don haka ki sanar da ita kar ta ƙara zuwa mini ofis. Saboda iskanci. Ita tana yawo ta kasa samun mijin aure, ke Allah ya raba da yawo a titi ya baki miji sai ta hure miki kunni."

"Ka yi hakuri zan gaya mata." Ta furta tare da zubowar wasu hawaye a ƙuncinta.

Tsaki ya ja tare da ture ta, ya wuce yana bambami.

Nasreen kunninta take murzawa, saboda ba ƙaramin riƙo ya yi musu ba. Maganganun da sun firgita ta, amma sai dai ba ta tunanin za ta iya sanar mata da kashedinsa, kuma ba za ta iya daina hurɗa da ita kamar yadda ya buƙata ba. Tsananin mamakin rashin tsoron Marwana ya kamata, da har ta iya zuwa har ofis ɗinsa ta yi masa kashedi.

Ko da suka haɗu a makaranta washegari, ba ta yi mata magana ba. Bayan sun tashi daga lecture suna hanyar dawowa gida.

Hira suke yi sosai Marwana tana gaya mata yadda ƴaƴanta yake matuƙar sonta. Da irin darun da take yi masa. Sosai take dariya tana kallonta cikin matsanancin farinciki. Tuni ta fahimci Marwana irin mutanen nan masu sanya mutum cikin farin ciki ko da ba su shirya ba, saboda rabon da ta yi irin dariyar nan ba za ta iya tuna ranar ba.

Marwana dariya take yi sosai tana tuki, tana kallonta yadda take dariya cikin farinciki. Ƙara kallonta ta yi, sannan ta ci gaba da tuƙa motarta cikin kwanciyar hankali.

A lokacin da suka isa inda za ta ije ta. Marwana ta kalleta ta ɗauko.

"Ga shi ki je kici gaba da aiki da shi, domin a yadda na ga Faruk ya razana ba zai hana ki ba."

"Haka kike tunani? Faruk sam ba shi da tsoro."

"In har kina jin tsoronsa ba za ki taɓa ƙwatar 'yancinki ba. Rayuwar aure ba ƙangin bauta bane, domin ya kamata Faruk ya mutuntaki a matsayinki na matarsa kuma uwar 'ya'yansa."

"Ba na son abin da zai kawo mini saɓani tsakanina da shi..."

"Kar ki damu ki karɓa, kuma in sha Allahu, babu abin da zai faru."

"Na gode da ƙaunar da kike mini Allah ya barku tare."

"Tsakaninmu babu godiya domin kin zama 'yan uwa."

Fita ta yi daga cikin motar, tana ɗaya mata hannu har ta ɓace daga gurin.

"Haka Ubangiji yake ikonsa, sai ya haɗa ka da mutanen ƙwarai." Ta furta tana kallon hanyar da ta wuce.

Faruk yana ta shirin aure ba tare da ya sanar da Nasrin ba. Har ana saura sati uku ba ta da labari.

Ta fara zargin ko aure zai yi ganin yadda yake ta gyaran gidan. Hankalinta ya tashi matuƙar gaske. Tana don ta yi masa maganar, amma tana tsoron abin da zai gaya mata.

Wata zuciyar ta shawarce ta da ta yi shiru ta zuba masa na mujiya, don ya fi mata alkhairi kan abin da zai gaya mata.

Faruk kuwa har ya kai kuɗin sadaki, da yake bazawarace ba a wani sanya ranar da tsayi ba. Sosai suke shirye-shirye a tsakaninsu.

Har ana saura kwana biyar bai sanar mata da maganar aurenta ba. Maman Muwaddat ce ta ji zancen bikinsa, wanda ya tayar mata da hankali. Sosai tausayinta ya kamata, duba ga halin da take ciki na zaman aurensa, ina ga kuma ya ƙaro mata kishiya. Ita ba auren ne ma ya fi tayar mata da hankali ba, wacce zai aura. Rashida bayerabiya ce amma ta zauna a cikin Hausawa. Mace ce jarabbiya sam ba ta da hakuri. Ko shi kansa bai san ruwan dafa kan zai ɗauko ba. Sannan ga shi ta girme wa Nasreen don ba sa'arta bace. Ko da ace Faruk zai ba ta shekarun bai wuce ɗaya ko su zo tsara ba. Idanunta a buɗe suke saboda mace ce wayyaya, wacce take cuɗanya da maza, don har sai da abinci a bakin titi ta yi. Daga baya ne da ta auri mijinta, sai da ta mayar da shi matsiyaci, sannan tsuka rabu. Bayan sun rabu ta kafa zawarci. Maza sosai take tatsa, don ko Faruk da fari ba ta yi ninyar auren sa ba. A cewar ta maza mugayen ne mayaudara masu daɗin baki. Mahaifiyarta tasha wuya sosai a gurin mahaifinsu, kafin Allah ya ɗauki kwananta. Su kansu ba su samu kyakkyawar tarbiyya da kula a gurinsu ba. Wannan dalilin ya sa ta ɗauki aniyar tsakaninta da su babu sausauci. Da fari ta yi ninyar shanye ƙwallon mangaro ta huta da ƙuda, amma kuma sai ta ga Faruk ya yi mata. Yana da zubin halitta mai kyau, sannan ga shi ɗan gayu, mai tashe da nera da ƙuruciya. Abin da ya ƙara jan hankalinta yadda yake kushe matarsa da cewar ba ta ba shi kula. Wannan dalilin ya sanya take son aurensa don ta more ƙuruciyarsa, domin har zuwa gurin malaminta ta yi don a karkato mata da hankalinsa. Abu ɗaya ta fara fuskanta game da shi wato maƙo. Duk yadda yake iƙirarin yana sonta, amma ba ya sakin mata kuɗi sosai. A ganinta hidimar da yake yi na bikinsu ya yi mata kaɗan, amma sai ta share ba tare da ta nuna masa komai ba, burinta kawai ta shigo cikin gidansa, yadda za ta samu damar juya shi, ya zamo mata janitalau.

A na saura kwana biyu, Maman Muwadda ta shirya sanar mata da bikin, ganin ranar da ta shiga cikin gidan ba ta yi mata maganar ba.

A ranar da ta je, sai ta tsokane ta don ji ko ta san da maganar, amma sai ta yi murmushin yaƙe ta ce,"Wallahi sai gyaran gida yake yi. Wataƙila aure zai yi, don ya sha gaya mini ba zai zauna da ni kaɗai ba."

Jin hakan ya sanya, a wancan ranar ta kama bakinta ta tsuke, don ba za a ji mutuwar Sarki a bakinta ba, amma daga baya sai ta ga in har ta bari aka yi bikin, kamar ta cuce ta ne.

Bayan ta shiga cikin gidan ta zauna. Nasreen da take zaune a falon tana yi wa Raihan tsifa. Ganin ta ya sanya ta miƙe tana murmushi. "Ban ji ƙwankwasa ƙofar ki ba?"

"A buɗe na ga gidan har na yi mamaki."

"Ikon Allah! Kuma ban san abuɗe yake ba, watakila da na fita siyo ashana na manta na kulle. Kin ga da Abban Rainah ya dawo dai ya zamar mini abin faɗa."

"To ki rinƙa kula." Ta ce mata bayan ta zauna.

"Raihan, tsifa ake yi?" Maman Muwadda ta yi mata tambayar tana shafa kanta.

"Wallahi kuwa, kin san gobe Monday shi ne na ke son muje kitso."

"Haka ne, ni ma can na barsu suna tsifa."

Sun ɗan yi shiru, babu mai magana a tsakaninsu. Nasreen ta fahimci kamar akwai maganar da za ta gaya mata.

Maman Muwadda ta gyara zama, ta buɗe baki kenan ta ji ƙarar motar Faruk yana hon.

Da sauri ta mike jikinta na zikiri. Ganin haka ya sa ita ma ta miƙe."Dama magana na ke so mu yi kuma ga shi ya dawo."

"Ok, in ya tafi zan shigo."

"A'a ki aiko Raihan ta kira ni, don na fi son mu yi ta a nan, zamu fi samun natsuwa."

Gabanta ne ya faɗi jin abin da ta ce."Lafiya Maman Muwaddat, ko laifi na yi miki?"

"Lafiya lau, kuma babu laifin da kika yi mini. Ai tsakanin mu babu wannan, domin da ace kin yi mini laifi zan sanar miki, saboda kamar 'yar'uwa na ɗauke ki."

Tunanin abin da za ta gaya mata yi, amma sai ta kasa fahimta."Ok, to shikenan, zan aiko ta gaya miki. Bari na je na buɗe kafin ya zama rigima."

A tare suka fito. Maman Muwaddat ta fice ita kuma ta buɗe masa get. Kallo ya bi ta da shi har ta ɓule, sannan ya mai da idanunsa kan Nasreen da take tsaye tana jiran ya shigo.
Chapter 18 · 0% Book details