Sashe 28
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin abin da ya faɗa ya sanya shi daga kansa yana salati. Kansa ya zarga da kuma yarda da ya yi aka ibi jininsa, domin da duk haka ba ta faru ba. Ina ma ace lokacin da ta buƙaci ya zo ya kaita asibiti bai zo ba.
"Ku shiga ciki tana son ganin ku." Tsoro ya sanya shi kasa jirgawa har sai da Hajiya ta ja hannunsa suka shiga.
"Wayyo Allah!" Ta ce tare da miƙa masa hannunta.
Kama hannun ya yi ya ƙarasa kusa da ita."So kike kiyi mini asarar kanki? Wallahi babu abin da ya haɗa ni da ita. Ƙawar Marwana ce, kuma kin san zan iya komai a kanta. Wannan dalilin ya sanya har na ba ta jinina, don na faranta mata."
"Ka yafe mini mutuwa zan yi, sannan ka kula mini da Little Marwana. Ka tuna da alƙawarin da ka yi mini cewar ko na mutu ba za ka ƙara aure ba. Ina mugun sonka, don Allah kar ka auri ko wace 'ya mace. Ka jira mu yi rayuwarmu a Aljanna."
"Ki bar wannan maganar ba za ki mutu ba. Za ki haifa mini yarona kuma ki raine shi da hannunki."
"Lokaci ya ƙure ka yafe mini." Ta ce tana kallonsa sai kuma ta fara jijjiga. Kallon lamarin suke kamar wasa, amma sai suka fahimci ya wuce lamarin wasa. Ya ruɗe iya ruɗewa ganin da gaske yana shirin rasata. Yana tsaye a gurin kamar gunki aka canza mata kaya. Miƙa masa takkadda aka yi ya sanya hannu. Idanunsa suka kaɗa suka yi jajir, hankalinsa ya tashi matuƙar gaske!
Ya kama hannunta ya riƙe, daidai lokacin da aka gungurata zuwa cikin ɗakin. Tsayawa a gurin ya yi hawaye yana bin ƙuncinsa.
Sun yi jugum-jugum har da Marwana, da take jin kamar ta rufe idanunta ta zama lamarin da wasa. Kusan awa ɗaya suke tsaye ba tare da kowa ya fito ba. Ganin haka hankalinsa ya tashe, domin a wancan aikin da aka yi mata, uwar haka tuni an fito da ita. An nuna masa Marwana har ya yi mata huɗuba.
Tsoro fargaba da damuwa suka cika masa zuciya. Suna tsaye a gurin har lokacin da likitan ya fito. Ganin yadda ya yi kace-kace da jini gabansa ya faɗi.
"Doctor, ya take?" Suka yi masa tambayar cikin tsananin tashin hankali.
"Please, ku shiga tana son ku yi bankwana, saboda we tried our best, but unfortunately we couldn't, saboda kafin mu yi mata aikin ta haihu."
"No," Ya ce yana matsawa sai kuma ya riga ya shiga ciki, daidai lokacin da su Mommy suka shiga.
"Batula," Ya kira sunanta tare da riƙeta ba tare da ya damu da jinin da yake zuba ya ɓata jikinta ba.
"Kaga maganar da nake maka na cewar ba za mu rayu tare ba ya tabbata? Mutuwa zan yi! Jikinsa ya ba ni ba zan rayu ba, don Allah ka ɗora mini abin da na haifa a jikina, ka nuna mini shi."
Idanunsa ya kai kan jajirin da yake ta kuka yana neman nono. Hannu Mommy ta sanya ta ɗauko.mata, ta ɗora mata shi a saman ƙirjinta.
"Kin haifi ɗa namiji."
Murmushi ta yi tana kallon yaron."Allah ya yi maka albarka. Za ka rayu cikin maraicin uwa, amma na san mahaifinka zai kula da kai." Ta ce tana nuna alamun a ɗauke shi daga jikinta.
"Ina little Marwana? Don Allah ku kawo ta mu yi bankwana." Ta ce tana kallonsa.
Matsawa ya yi kawai yana kallon ikon Allah. Tunawa da ya yi mahaifinsa da zai mutu, haka ya rinƙa ba shi wasiyya. Tun yana ganin wasa yake yi, amma tafiyar da ya yi kenan, wanda har yau bai ƙara ganin sa ba.
Mommy ta fita cikin kuka tana kuka. Kallon da ta yi mata ya tabbatar mata da sai wani ikon Allah. Little Marwana ta ɗauko ta zo ta ɗora ta kan jikinta.
Hannunta ta kama tana murmushi."Allah ya yi miki albarka." Ta ce tana kallonta hawaye yana zuba a ƙuncinta.
"Don Allah ku ɗauke sa, ƙirjina zai fashe." Da sauri ya janye ta ganin tana tari.
Jini yana ta zuba. Iya ruɗewa sun ruɗe. Kuka suke yi sosai hankalinsu ya tashi matuƙa.
Duk yadda suke ɗaukar lamarin ya wuce wasa. Damir da ya ga numfashi yana ƙoƙarin bankwana da gangar jikinta. Ƙara ya saki cikin tashin hankali. Da sauri likitoci suka yi kan kanta.
"Da gaske mutuwa za ki yi? Don Allah kar ki mutu ki bar ni." Ya ce yana miƙa hannunta.
Da ƙyar likitocin suka yi nasarar fita da shi suka rufe ƙofa.
Tari ta fara tana faɗin,"Ruwa ku ba ni ruwa zan sha." Na take jikinta ya rikice.
Bayan fitarsu Nasreen ta shiga cikin tsananin tashin hankali. Ahmad shi ma tsaye ya yi yana mamakin lamarin. "Ya Ahmad, anya ina da sa'a a rayuwa? Dubi yadda suka shiga cikin damuwa saboda sun taimaka mini?" Ta yi masa tambayar tana zare idanunta kamar taɓaɓɓiya.
"Ki yi shiru in sha Allahu, komai zai wuce." Ya ce cikin damuwa yana kallonta.
"Wayyo Allah na! Da na sani da ban kira ta ba, wallahi na yi ta kiranka, amma wayarka a kashe. Don Allah ka je ka basu haƙuri su daina faɗa"
Kama hannunta ya yi ya riƙe yana rarrashi ganin yadda take ta kuka.
Kwanciya ta yi tana ta kuka, tana ganin duk abin da ya faru laifin Faruk ne. Da ace ya kula da ita babu wacce za ta kira. Tausayin Marwana ya kamata tana tunanin halin da take ciki.
Duk iya ƙoƙarin su, na son dawo da numfashinta da ya ɗauke sun gaza. Doctor Fadil ya janye mata oxygen da aka sanya mata bayan ya sanya farin ƙyalle ya rufe mata fuska.
Kallonsa ya yi kamar zautacce yana faɗin,"No! No doctor, ka da ka furta mini matata ta mutu? Don Allah kar ka ce ta mutu ta bar ni?" Ya yi masa tambayar yana jijjiga shi.
"Am so sorry to say, matarka Allah ya yi mata ras..."
"I said no! Batula ba za ta mutu ta bar ni ba." Ya furta tare da ƙwala ƙara. Ƙarar da ya ƙwala sai da asibitin ya ɗauka.
Nasreen hankalinta ya tashi matuƙa. Zabura ta yi za ta fita."Ba za ki iya fita ba, sam ba ki da ƙarfi."
"Don Allah ka bar ni na je, Allah ya sa matarsa ba ta mutu ba, a dalilina." Ta ce masa tana kuka.
Kamata ya yi ya kwantar yana rarrashinta. Kuka take sosai kamar ranta zai fita. Tunani take innhar matarsa ta mutu zai yafe mata kuwa?
Jin ihunsa ya sanya suka sheƙo da gudu zuwa ciki. Ganinsa zube a ƙasa ya sanya suka fahimci ta mutu.
"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! 😭 Batula Allah ya jikan ki." Ta furta tare da ƙarasawa gurin ta tana kallonta.
Jin abin da ta ce wani irin zabura Marwana ta yi. Hankalinta ya tashi matukar gaske. Gani take yi lamarin kamar a mafarki.
Ƙarasawa ta yi inda take kwance babu numfashi."Anty Batula," Ta ce tare da ɗaya ƙyallen da aka rufe mata fuska.
"Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Ta furta sai ga ta a ƙasa babu numfashi.
Gabakiɗaya sun rufe sun shiga cikin tsananin tashin hankali. Kuka suke yi sosai suna gani kamar za ta farfaɗo. A lokacin da ya farfaɗo ya karasa kan gadon. Tsayawa ya yi yana kallon ta tamkar ya zauce."Yanzu tafiya kika yi kika bar ni? Dama da gaske ne kike gaya mini ba za mu rayu har abada ba? Batula don Allah ki tashi ni da Little Marwana muna buƙatar ki." Ya faɗa yana girgiza ta. Ganin ta ƙi tashi sai kuma ya je ya ɗauko jaririn ya ƙara mata jikinta. "Kin ga yana kuka ko? Ki tashi ki ba shi nono."
Kuka suke yi sosai suna kallonta. Lailai rai ba a bakin kowa yake ba. Duniya kenan kana ciki yau babu kai. Ga Batula ta tafi ta bar su a cikin wani yanayi.
Jin kukan ya yi yawa ya sanya Ahmad fitowa. Tsananin ruɗani da tashin hankali ya shige shi. Duk da ba a mamaki da mutuwa, amma sai da mutuwarta ta buge shi.
Ɗaki ya dawo ya samu Nasreen tana ƙoƙarin miƙewa."Ki koma ki kwanta sai haƙuri. Allah ya yi wa matarsa...."
"No, Ya Ahmad!" Ta furta tana toshe kunninta.
"Don Allah don Annabi, kar ka ce mini na zama sanadin da matarsa ta mutu? Kaicona! Ba ni da amfani a duniya. Da ma ni na mutu ba ita ba." Kuka take yi sosai ta kasa daina surutu, sai sumbatu take yi. Ahmad tun yana rarrashinta har ya ga ji ya zuba mata idanu, yana mamakin faruwar lamarin.
"Ya kamata Ku ɗauke ta don kuke ku yi mata sutura." Likitan ya furta yana kallonsu cikin tausayawa.
Cikin mota aka sanya gawar. Har suka isa gida Damir yana jin lamarin kamar a mafarki. Tamkar mutum-mutumi ya dawo. Babu um babu a'a sai kallo. Ita kanta Marwana ji take kamar ta mutu, ganin lamarin duk ita ta zamo silar faruwarsa. Kuka kuwa tun tana yi har idanunta suka ƙafe.
Kafin kace me mutuwarta ta zaga duniya. Yan'uwa da abokan arziki suka fara zuwa cikin tsananin tashin hankali. Masu kuka na yi masu salati na yi. Damir zama ya yi ya tasa gawar da ido yana kallo. Shi har yanzu ji yake kamar ba ta mutu ba. Ya tuna a darenjiya da ta shayar da shi madarar ƙaunarta, da safe ma haka suka kasance cikin farinciki. In ya tun haka sai ya rintse idanunsa yana jin tsanar Nasreen. Ba ita ba hatta mai sunan da ya fara da harafin sunanta, ba ya kaunar ya gani. Ya yi kuka har ya gaji duk dauriyarsa.
Bai ƙara shiga cikin tashin hankali ba, sai da aka ce ya shiga ya yi bankwana da ita. Anan ya mike yana mazurai."Na rantse babu wanda ya isa ya fitar mini da matata, saboda ba ta mutu ba, tana numfashi ku lura ku gani." Ya ce yana ƙoƙarin janye likafanin.
"Ka yi haƙuri ka ɗauki ƙaddara, amma ta riga mu gidan gaskiya."
"Babu wanda ya isa ya ɗaukar mini mata, duk wanda ya ɗauke ta sai na kashe shi." Ya karashe maganar yana kallon abokinsa da ya furta maganar.