← Book details Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 40

Sashe 14

Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni dai ban yi sa'ar zuwan duniya ba, domin na kasance daga cikin wadanda suke karɓan ruwan mara daɗi a cikinta. Zaman aurena ba shi da maraba da bauta. Mijina bai bai ɗauke ni da wata daraja ba. Zuciyata zafi take yi tamkar za ta fito waje."

"Ki yi shiru ka yi mini bayani."

Sai da tasha kuka son ranta sannan ta kwashe lamarin ta gaya mata.

"Allah Sarki! Ita kuwa wannan wace ce ta shigo rayuwarki? Haƙiƙa na yi miki farincikin. Allah ya sanya ta zama sanadin da za ta kawo haske a cikin rayuwarki." Ta furta cikin tsananin farin ciki.

"Zan matar mata ba zan iya jurar toxarcin da nake fuskanta ba."

"Saboda me za ki mayar masa? Wallahi ina gaya miki matuƙar ba ki tashi kin nuna wa Faruk, ko babu shi za ki iya rayuwa ba. To rayuwarki na cikin siradi rayuwa. Nasreen, kina da kyan ki da ilmin ki. Sannan kuma da kyawawan halaye. Ko da ace mahaifinkk ya kore ki ba za ki rasa inda za ki zauna ba, har ki samu miji ki yi aure. Faruk ba mijin da mace za ta zauna da shi bane, domin so yake ya tsotse ƙwallon mangaron ya huta da ƙuda. Ki tashi ki nuna masa kema mace ce kina da gata. Talauci da 'ya'ya ba hauka bane da za ki kashe kanki saboda su. In har kika nuna masa ko babu shi za ki iya rayuwa, zai rage abin da yake yi, domin yana sonki.

Faruk! Rayuwar aure na ƙargin bauta bane da za ka mayar da mace tamkar jaka. Masu hali irin na Bana haƙiƙa suna kawa 'ya'yansu gori da tozarci.

Makaranta innsha Allahu yau zan yi posting safe da yamma a cigaba da surbubuɗo comments ❤️❤️❤️❤️💃💃💃💃
WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme.

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423

*WASU MAZAN*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan

08144072423

PAGE 9

BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
"Saboda me za ki mayar masa? Wallahi ina gaya miki matuƙar ba ki tashi kin nuna wa Faruk, ko babu shi za ki iya rayuwa ba. To rayuwarki na cikin siradin rayuwa. Nasreen, kina da kyan ki da ilmin ki. Sannan kuma da kyawawan halaye. Ko da ace mahaifinki ya kore ki ba za ki rasa inda za ki zauna ba, har ki samu miji ki yi aure. Faruk ba mijin da mace za ta zauna da shi bane, domin so yake ya tsotse ƙwallon mangaron ya huta da ƙuda. Ki tashi ki nuna masa kema mace ce kina da gata. Talauci da 'ya'ya ba hauka bane da za ki kashe kanki saboda su. In har kika nuna masa ko babu shi za ki iya rayuwa, zai rage abin da yake yi, domin yana sonki. Tsabar jahilci da rashin sanin darajar mace da kuma ɗaukar aure a matsayin ibada ba, ya sanya yake wulaƙanta rayuwarki."

Kamata ta yi ta rungume tana shafa bayan ta sannan ta ɗora da cewa,"Guda nawa kike da har za ki fuskanci wulaƙancin ɗa na miji?"

Kuka take yi sosai har ta gaji ta yi shiru sai ajiyar zuciya. Ba ta baki ta shiga yi har ta samu sauki a cikin zuciyarta. Wayarta ta ɗaya ta kira babbar 'yarta ta kawo musu abinci.

Ta daɗe tana gidan tana kwantar mata da hankali, sai da aka kusa kiran magariba sannan ta yi mata sallama ta tafi.

Bayan tafiyarsa ta gama gugan ta yi alwala ta yi sallah. Sannan ta ɗauki qur'ani tana karantawa har kusan a kira isha'i.

Ƙwankwasa get ɗin gidan da ake yi da dutse ya sa ta tashi ta je ta bude da tunanin waye cikin daren nan

"Wane ne?" Ta furta daidai lokacin da ta isa bakin get ɗin.

"Ahmad ne." Ya ba ta amsa tare da jefar da dutsen

Tana buɗe get ɗin gidan ta saka mishi kuka tare da faɗawa jikin shi.

"Mai ya sa kika aikata haka? Kin san za ku zo ai da kin kira ni."

"Na yi ta kira ka wayar a kashe." Ta ce masa cikin muryar kuka.

Kama hannunta ya yi suka shiga ciki. Zaunar da ita ya yi, sannan ya zauna a gefenta.

"Faɗa mini wa ya ba ki waya da laptop masu tsada haka?"

"Ka yarda da ni Yaya Ah.."

"Da ma na zarge ki ne? Na san wace ce ke. Ko Baba ya rantse ba za ki taɓa kauce hanya ba. So kawai na ke na san inda kika samo su."

Cikin kuka ta sanar masa wanda ya cika da mamakin kyautar.

"Da kin sani da ni kika kawo mawa, sai na kawo masa na ce na saya miki, amma dama ko wane namiji ya ga matarsa, da abu mai tsada haka dole ya tambaye ta ba'asi."

"Na yi kuskure Yaya." Ta furta tana share hawaye.

Kwantar mata da hankali ya shiga yi har ta samu ta saki.

Ledar awara ya miƙa mata yana faɗin," Ga shi ki samu ki ci na san wataƙila ba ki ci komai ba."

"Maƙociyarta ta kawo mini."

"Allah ya saka mata da alkhairi."

"Amin," Ta furta tare da miƙewa ganin ya miƙe.

Ko da suka zo bakin get nasiha ya yi ta mata, sannan ya kawo Naira ɗari biyar ya ba ta.

Koma ɗauki ta yi ta kwanta yayin da hannunta ɗauke da carbi tana lazimi.

Faruk kuwa tun da ya fita ya rasa sukuni. Kallon wayar yake yi cikin tsananin mamaki, saboda wayar mai tsada ce. A yadda Ahmad ya ɗan nuna alamun rashin gaskiya, ya sa ya shi kokwanto kan siya mata da ya ce ya yi. Sannan ko da bai nuna ko kokwanto ba. Sam ba zai yarda ba don ba, shi da arzikin da zai iya sigar ko da wayarce.

A hanya yanke shawarar dole ya sa ya ta ta yi rantsuwa da qur'ani shi ya siya mata.

Saboda jaraba yana dawowa ɗakinta ya shiga, wacce ta yi nisa a duniyar tunani ba ta ji hon ɗin motarsa ba. Ballantana shigowarsa.

Ganinsa ya sa ta tsorata tare da miƙewa tamkar za ta ruga.

"Ka yi hakuri ban san ka..."

"Rufe mini baki banziya kawai! Da ma kina jin maganata ne? Ai kin raina ni duka kuwa kin saba kamar jaka!"

"Kawo qur'anin." Ya ce mata.

Mika masa da sauri ta yi tana ƙare kanta da hannu a tunaninta dukanta zai yi.

"Ka yi haƙuri don Allah."

"Ungo." Ya ce mata.

Da sauri ta karɓa a ranta tana mamakin dalilin da ya sanya ya karɓar da ya yi.

"So na ke ki rantse da qur'anin nan Ahmad ya siya miki."

Zare idanu ta yi har ta saki qur'anin zai faɗi, ta yi maza ta riƙe da sauri jikinta na mazari.

Ganin yadda ta firgita, ta shiga cikin tsananin tashin hankali, tare da hawaye ya sanya masa shakku a ransa.

"Ma za rantse na ce, saboda shi zai sanya na yarda dake. Na san yadda kike daraja qur'ani da kuma wanda ya yi, sam ba za ki iya rantse wa kan ƙarya ba. In har kika rantse yanzu zan ba ki na yi miki fatan alkhairi."

Ta yi shiru tana zare ido, a ranta ta fara tunanin ta gaya masa gaskiya ko ba zai yarda ba, domin ko da suka zai sanya mata a maƙoshi ba za ta rantse ba. Tana tsane da ko a kan gaskiya mutum ya rantse Allah zai iya hukunta shi, domin Alqur'ani ba abin wasa bane.

"Ki rantse na ce." Ya daka mata tsawar da ya ƙara firgita ta.

Ije wa ta yi tare da ƙara sakin kuka."Zan gaya maka gaskiya." Ta ce tana ɗaya yatsunta, kamar wata ƙaramar yarinya.

"Ina jin ki." Ya furta cikin mamaki yana kallonta.

"Wallahi wata 'yar ajinmu ta bani. Kuma in har ba ka yarda ba. Mu je makarantar na ma mayar mata."

"Ta ya ya zan yarda, in kun haɗa baki ne ita ke ɗora ki a hanya fa? Yar iska da aurena za ki ci amanata." Ya kai mata mari yana faɗin haka.
Chapter 14 · 0% Book details