Sashe 22
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Hello Sahibata.."Maganar ta tsaya sakamakon ji da ta yi tana numfashi da ƙarfi ta ce,"Wash Allah! Marwana zan mutu cikina, don Allah ki sa ya direbana gidanku ya zo ya kaini asibiti. Na kira wayar ya Ahmad a kashe. Ɓari na yi." Ta ƙarshe maganar tare da sakin gigitaccen ƙarar da ya tayar da hankalinta.
"Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Nasreen ɓari ina Faruk?"
"Ki taimaka mini Faruk ba ya nan." Ta ce tare da kashe wayar.
Ruɗewa ta yi ta rasa yadda za ta yi. Har ta fita don ta sanar da direba ya fito su je, amma kuma sai ta fasa ta koma ciki. Ɗakin Damir ta shiga ƙwankwansawa cikin tashin hankali tana kiransa.
Damir da yake kwace rungume da matarsa yana tunanin halin da take ciki. Fatansa Ubangiji ya sauke ta lafiya, don ba zai iya rayuwa babu ita ba. Tun lokacin da ya haɗu da ita yake jin matuƙar ƙaunarta, ko lokacin da ya san cewar ita sikila ce, bai ji sonta ya ragu ba, sai dai tausayi. Soyayyarta daga Allah ne. Fatansa ta yi tsawon rayuwa, domin ba zai iya auren wata mace ba in har babu ita, ji yake da ta mutu gara ace shi ya rigata. Kullum tunani yake ina ma da za a ba shi damar ya zaɓi ciwon ya dawo jikinsa.
Kai bakinsa ya yi ya sumbaci goshinta yana shafa kanta. Ƙwankwasa ƙofa da kiran da Marwana take masa, ya sanya hankalinsa tashi matuƙar gaske! Shi a tunaninsa wani ne ya mutu.
Da sauri ya miƙe tare da sanya rigar da ya fito." Lafiya Marwana?" Ya ce mata tare da riƙeta ganin yadda ta ruɗe.
"Ya Damir, ƙawata Nasreen ba ta da lafiya za ta mutu, don Allah mu je mu kaita asibiti."
"Ke Marwana ki natsu ki yi mini bayani."
Jin bin da ya ce yana girgiza ta ya sanya ta fashe masa da kuka."Nasreen ƙawata 'yar ajinmu ta kira ni tana kuka za ta mutu ta yi ɓari jini yana ta zuba."
"Ɓari? " Ya yi mata tambayar cikin tsananin tashin hankali, sabida yana tausayin mata a wannan condition na ciki da haihuwa. Ya san cewa a wannan lokacin suna cikin tsakanin mutuwa da siraɗi.
"Ɓari ta yi Ya Damir." Ta ce masa tana share hawaye
"Ina mijinta?"
"Baya nan." Ta ba shi amsa.
"Kalli lokaci dare ya yi, kuma bai kamata mu fita ba, ina ga ba ri na kira Doctor Sadik ya je da ambulance a kai..."
"Please, Yaya ba zan iya kwana ba, ba tare da na san halin da take ciki ba. Babu nisa sosai kuma duka yanzu ten ta yi, don Allah ka taimaka mata kar ta mutu. Mijinta bai damu da ita ba, kuma wallahi in don ta shi zai iya barin ta mutu." Ta ƙarashe maganar tare da kama hannunsa.
Shuri ya yi yana jinjina lamari."Amma kin san abin da ya faru ko? Bana son matsala in kuma kin nace sai ku je da Idi direba."
"Please, Ya Damir don Allah mu je da kai, za ka fi gudu a mota, kuma ko asibiti muka je za a fi kula ta."
"Haba Marwa..."
"I insist Yaya Damir, please." Ta ce tare da haɗa hannunsa.
"Ba zan iya fita na bar ta ita kaɗai ba."
"Don Allah ka taimaka yanzu za mu dawo, kuma Baba tana nan."
Babu yadda zai yi, kan dole ya shiga ciki ya canza kayansa. A hankali ya ja mata ƙofar suka fice. Duk gudun da yake yi gani take ba ya gudu.
"Don Allah ka yi sauri kar ta mutu."
Da sauri ya kalleta yana mamakin abin da ta ce, tare da mamakin yadda take sonta. Shi a iya saninsa Marwana ba ta tara ƙawaye, sai ga shi ta yi ƙawa mace mai aure.
"Duk iya gudun da na ke yi kin raina? So kike na je na watsar damu? In kin raina sai ki karɓi tuƙin."
Jin ya yi magana cikin fushi ya sa ta ce,"Am sorry."
Da suka shiga cikin unguwar a lokacin goma har da minti goma. Kallonta ya yi, daidai lokacin da ya yi parking ba ta jira ya gama ba ta fice daga motar.
A lokacin Nasreen ta yi nasarar fitowa ta buɗe get ɗin gidan. A hanyar falo ta kusan tuntunɓe da ita. Har ta tsorata sai ta duƙa ta kama hannunta fahimtar ita ce a gurin.
"Nasreen ya jikin ki?' ta kama hannunta ta yi mata tambayar cikin tashin hankali ganin yadda ta koma.
"Marwana zan mutu ki taimake ni." Ta furta tana nishi da ƙyar.
"Ba za ki mutu ba." Ta ce tare da kama hannunta.
Bayan shigarta gidan Damir ya bi get ɗin gidan da kallo cikin mamaki. Shi kansa bai taɓa tunanin gidan mai kyau take ba, jin yadda take na shi labarin tana wahala. Sai ya jinjina kansa cikin mamaki yana mamakin WASU MAZAN da suke ƙuntatawa matansu alhalin suna da shi. Yana wannan tunanin ya hange su, sun fita kusan a jikin Marwana take. Da ƙyar Marwana take janta
Wani irin bugawa zuciyarsa ta yi, har sai da ya dafe gurin, yana jin yadda take masa zillo tamkar za ta fito waje. Hango ta ya yi a cikin duhun, amma sai ya ji ya tasa sukuninsa. Wani yana yi ya tsinci kansa wanda ya rasa wani irin yanayi ne.
"Please Ya Damir, ka buɗe bayan motar." Muryar Marwana ta katse shi tana faɗin haka.
Cikin hayyacinsa ya dawo, da sauri ya zagaya ya buɗe mata motar ta sanya ta a ciki.
"Marwana yarana suna ciki kuma babu kowa a gidan." Ta ce mata tana cige bakinta.
Jin abin da ta faɗa da sauri ta koma ciki. Yaran ta ɗauko ta sanya su cikin mota.
Shiga cikin motar ya yi, sannan ya tada tamkar wanda yake jin bacci.
Ganin halin da take ciki domin a wannan lokacin ta fita hayyacinta. Kai tsaye asibiti su ya kaita.
Suna isa likitoci suka karɓe ta tare da gungurata a kan gado sun yi ciki da ita.
Ganin yadda Marwana ta tayar da hankalinta kamar za ta yi hauka. Ya sanya shi jawo ta ya rungume daidai lokacin da ta yi kamar za ta shiga ciki
"Take easy za ta samu sauƙi. Kina sonta da yawa."
"Yaya Nasreen ba ta da gata sai Allah. Kai kanka in har ka ji rayuwarta za ka tausaya mata."
"Allah ya kawo mata ɗauki, amma ina mijinta yake a wannan lokacin? Ya san matarsa na da ciki ya tafi ya barta."
"Ban sani ba ta ce ya yi tafiya."
Jinjina kansa ya yi, ba tare da ya ƙara cewa komai ba.
Sun daɗe a gurin sannan likitan ya fito yana share zufa. Da sauri suka yi burinsa.
"Doctor how is she?" Damir ya riga ta tambayar ganin yadda ta damu da ita.
"She is getting better. Mun yi ƙoƙarin mun tsayar da jinin, yanzu so muke ta ɗan huta ayi mata wankin ciki."
Tausayinta ya sanya ta ja numfashi."Ok please do." Damir ya ce yana cusa hannunsa a aljihunsa.
"We will." Likitan ya amsa tare da ba shi hannu ya koma ciki.
"Marwana I think I will take my leave. Kin ga halin da Mommy Little Marwana take, bai kamata na barta a ita kaɗai ba."
"Ok Yaya, amma kwana zan yi saboda ba zan iya barin ta ba."
"Ƙarki damu zan dawo na kawo muku breakfast. Sai ki sanar da iyayenta, ki dawo gida."
"To Yaya, Please drive safe." Ta ce masa tana kallon sa.
Har ya kai baƙin ƙofa, sai ya dawo da ya tuna yaran suna cikin mota."Ina ga zan wuce da yaranta, tun da bai kamata su kwana a kwana asibiti ba."
"Haka ne Yaya, ka wuce da su da safe sai ka kawo mini su."
Kaɗa kansa ya yi, ba tare da ya ce komai ba, ya fice daga asibitin. A lokacin da ya isa gida sai ya kashe motar, bayan ya yi parking. Yaran ya ɗauka ya shiga ciki da su.
A lokacin da ya shigo cikin ɗakin, da ta farka ta shafa inda yake kwance ta ji babu shi. Tana tunanin yana bayi ne, don haka ta koma ta kwanta tana jiran ya fito. Jin shiru sai ta fara shiga damuwa.
A hankali ta miƙe ta shiga cikin bayin amma ba ya nan. Falo ta duba nan ma ba ya nan. Wayarta ta ɗauko tana ƙoƙarin kira, ganin sha biyu saura sai ta ji ƙarar motarsa. Daidai fitowar ta falon ta gan shi ya shigo da sallama rungume da yara.
Gabanta ya yi mugun faɗi, ta ƙara da burinsa daidai lokacin da ya kwantar da su. Kallon yaran ta yi ganin su kyawawa sosai kuma farare.
"Baby, ina ka samu yara?" Ta yi masa tambayar tana kallon sa, da yayin da zuciyarta ke kimtsa mata mugun tunani.
Yana ƙoƙarin amsawa sai ta katse shi da cewa,"Wai ina ka je da daddaren nan? Hankalina ya tashi ina ta nemanka."
Kallon yaran ya yi, yana mamakin kyawun yaran, domin suna da kyau sosai, musamman Raihan da har wani tsanwa take yi, kuma da ma Musaddik ya taɓa ganinsa. Tunani yake haka uwarsu take, amma mijin ta yake wulaƙanta su.
"Yaran ƙawar Marwana ne. Ina bacci ta tashe ni ta yi ɓari, kuma mijinta ba ya nan ya yi tafiya. Shi ne na ce su je da direba, amma kin san halin ta da rigima, kan dole ta sa ta muka je. Wallahi da muka je na tausaya mata sosai. Kai gaskiya wa WASU MAZAN ba sa yi wa matansu adalci.
Jin ta yi ba ya ce, sai ba ta ce komai ba, tana kallon yaran da ya kasa ɗauke idanunsa. Ta ja numfashi ta fesar sai kuma ta daure."Ikon Allah." Ta ce sai kuma ta kalle shi ta ce,"Shi ne ta rasa wacce za ta kira sai ƙawa? Ita ba ta da kowa ne?"
Tambayar da ta yi masa ya sanya ransa ya ɗan ɓaci, duk da cewar shi ma ya yi tunanin haka.
"Please dare ya yi bacci na ke son na yi. Ina ga wannan tambayar inta dawo sai ki yi mata. Yaran nan bari na kai su ɗakin little Marwana."