← Book details Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 40

Sashe 13

Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki buɗe ƙofar nan, muje na tambayesa in kika ƙara sakan biyar wallahi a igiyoyin aurenki..."

Bai gama maganar ba ta fito, da hijabinta da ta yi sallah jin abin da ya ce."Da ki zauna kar ki fito, sai na ga gidan uban da za ki in na sake ki."

Tsaki ya yi ya juya ya fice, ganin haka ta ƙarashe goya Musaddik tana hawaye ta bi bayansa.

Yana isa ƙofar gidan ya fara sakin hon babu ƙaƙƙautawa.

Jin hon ɗin ya farkar da Baba, da yake ta sharan bacci, ya ƙi tashi ya yi sallah, duk da nacin tashin da Mama take mishi.

"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Yau kuma mai Nasreen ta yi wa wannan tsinannen mijin nata?" Ya yi tambayar tare da miƙewa yana zare ido.

Mama ita kanta jin hon ɗin na sa hankalinta ya yi matuƙar tashi.

Fita ya yi tare da ɗaukar rigarta yana da sanyawa.

"Yau wallahi yadda ba ni da ƙo ƙwandala, ya ce zai yi mini rashin kunya sai na ci ubansa." Ya faɗa tare da fita wajen.

"To isasshe ɗan ƙaruna. Ka kashe motar ma ka fito ba za ka iya ba, sai dai ka damu mutane da hon, kamar wanda ya zo da jirgin sama."

"A gurinku ai kamar tafi jirgin tun da ko keke ba ka da shi." Ya bashi amsa fuska a tamke, tamkar ba da surukinsa yake magana ba.

"Ka san ba mutunci ne da ni ba ko Faruk? Wallahi yanzu zan maka rashin mutunci. Da ma ba ka san haushinsa na ke ji ba. Ƙiri-kiri na nemi aro dubu goma ka hana. Sai kace dubu ɗari na nema."

"A kan me zan ba ka kuɗin bayan 'yarka da ka aura mini tana gasa mini gasa a hannu? Tambayeta rabon da ta bani haƙƙina kwana biyar kenan, saboda ta samu mazan jami'a, tana iskanci da su suna biya mata bukatunka."

Kallon mamaki ya yi mata jin abin da ya ce.

"Baba, wallahi ba haka ba ne, Baba bana kula ko wane ɗa namiji." Ta faɗa cikin muryar kuka tana gyara goyon Musaddik.

"Ƙarya zan yi miki kenan?" Ya ce tare da kai mata duka ta kauce.

"Faruk! Ko mutuwa tana jin kunyar mahaifi a gabana za ka duketa?"

"Ƙarya ta zan iya yi, domin zuciyata gaba take da ta bani shawarar na yi ajalinta. Matuƙar ba za ta gaya mini, wanda ya siya mata waɗannan ba." Ya ce tare da nuna masa.

Zare idanunsa ya yi, yana kallon wayar da laptop ɗin sai kuma ya juya yana kallonta.

"Zina take yi suka siya mata."

"Wallahi Baba ba zina na yi ba." Ta ƙara cewa."

Baba kuwa mamaki sosai ya kama shi, sai ya shiga tunanin wa ya siya mata, don ya san Ahmad ba shi da kudin da zai iya siyan mata.

"Nasreen, wa ya siya miki?"

"Na'am eh Ya Ahmad ne." Ta ba su amsa cikin kuka.

"Ahmad?" Ya yi tambayar yana kallonta.

Kafin ya ce wani abu Ahmad da ya dawo daga Masallaci, rike da karbi yana ja a hannunsa, ya ƙaraso da sauri ganin motarsa.

Harara suka ba ka ma junansu, domin tamkar mage da ɓera suke. Faruk yana ɗan shakkar Ahmad, saboda ba sa gama maciji, kuma ya san shi kamar zawayi yake. Sai ya ɗan rage hargowar da yake yi.

Ba tare da ya kalli Faruk ko Baba, ba ya karasa gurinta da ganinsa, ya sa ta fashe da kuka tare da kama hannunsa.

"Nasreen, mene ne?"

"Mazan jami'a take bi suka saya mata waya da laptop mai tsada."

Maganar ta buge shi, musamman da ya nuna masa wayar da laptop ɗin Shi kansa ya razana da ganin wayar.

"Ya Ahmad ka san halin ba zan taɓa bin wani ɗa namijin da aurenka ba. Na gaya mishi kai ka siya mini, amma ya ƙi yarda."

Jin abin da ta fada, ya sa shi ƙoƙarin shanye mamakin inda ta samo su.

"Ƙarya ne ba shi da kuɗin da zai iya siya miki." Faruk ya ce yana kaɗai makullin motarsa.

"Saboda ka mayar dani matsiyaci ko, sannan ka manta dare ɗaya Allah kan yi Bature? To ni na siya mata tun da kai ka kasa. Adashi na kwasa na siya mata, tun da kai ka kasa."

Kallon mamaki suka yi masa har da Baba.

"Yanzu dama Amadu, kana da kudin siyen waɗannan na yi da kai, jiya ka bani naira dubu shegiya ka hana?"

Ba tare da ya amsa masa ba, ya juya gurin Faruk."Na gaya maka ka daina dukanta, domin ita ba jaka bace."

"Dole na duketa, tun da ko addini ya bamu damar in mata mu suka ɓata mana mu duke su."

"Wannan fatawar na ka ya sanya na gane kai babban jahili ne. Ilmin boko kawai kake takama da shi."

"Na gode ma Allah tun da na yi bokon, kai kuma da ubanka ya kasa ba ka duka f.." Kafin ya ƙarashe ya ɗaya hannunsa zai kai masa mari, amma sai ya doje.

"Wallahi in har ka yi kuskuren marina, sai na kashe ƙanwarka da duka kuma ka yi zaman burtsuna."

"Kai Amadu wai mai ke damunka ne?In ka tunzura shi ya saketa, wallahi kai da ita sai dai ku bar mini gidana."

"Baba, Allah zai kama ka a kan haƙƙin Nasreen. Ka ba shi dama yana cutar da rayuwarta."

"Ka fita idona ɗan iska kawai! Uban me ka sani game da aure. In ta rabu da shi kasan mijin da za ta ƙara aure?"

"Ba..."

"Kar na ƙara jin muryarka. Wulaƙantaccen yaro kawai." Ya daka masa tsawa yana faɗin haka.

Ransa ne ya ɓaci hannunta ya ja za su shiga ciki.

"Kai Amadu! Gidan uban wa za ka kai ta?" Ya yi masa tambayar cikin ɓaci rai.

"Ka barshi ya shiga da ita ciki, ta zauna har illa ma sha'a. Ki an gaya masa amfani take mini? Ci da ita kawai zai zamar masa aiki." Ya ce yana ƙoƙarin shiga cikin motarsa.

"Ke Nasreen dawo ki tsaya kai kuma wuce." Ya ce mishi cikin tsawa.

Idanunsa suka kawo ruwa, ya kalle ta da take ta kuka, ganin har mutane sun fara tsayawa ana kallonsu.

Tausayinta ya sanya hawayensa zuba. Girgiza kansa ya yi, tare da wucewa ba tare da ya ƙara cewa komai ba.

"In kin san ba shi ya saya miki ba ki bawa mijinki hakuri, sannan ki kawo ni zan san yadda zan yi dasu." Ya faɗa tare da fatan Allah ya sa ta bashi ya siyar.

"Shi ne Baba."

"To ka ji ka yi hakuri kamata ya yi ya gaya maka."

Kallonsa ya yi don har yanzu bai yarda ba.

Ba tare da ya ce komai ba ya fara ƙoƙarin shiga motarsa.

"Za ki shiga ki bi mijinki shashasha kawai! Kuma wallahi kika ƙara barin ya kawo ƙarni sai na saɓa miki."

Da sauri ta shiga tana kuka. Ganin ya shiga motar har ya tada ya sanya shi duƙawa.

"Faruk, tafiya za ka yi? Maganar kuɗin nan fa. Har gida zan zo na ja mata kunni."

"Ni fa kana isata 'yar ka babu tarbiya, amma kullum buƙatar da kake kawo mini daban. Wallahi na yi dana-sanin auren zuriyarka."

"Ka yi hakuri ba za ta ƙara ba."

Hannu ya sanya a aljihunsa, ya ciro kudi da yawa kamar zai bashi sai kuma ya fara irga dubu biyar.

"Iya wannan zan ba ka, kuma na rantse in ba ka dawo mini da su ba. Karka ƙara tunanin zan baka rance, tun da ba biya kake ba." Ya ce tare da kunna motarsu ya fara tafiya.

"Raba mugu da makami, ibada. Kuma wallahi ko kafi maye maita ba zan bayar ba. Ni zan yi dana sani da na ɗauka gidan da zan rinƙa zuwa maula na aurar da ita. Ashe ɗan Iskan ƙalƙo na aura mawa." Ya faɗa yana aika ma motar mugun kallo.

"Kai Allah na gode maka. Na tashi bani da ko fincika, amma na samu kudin da zan kashe har kwana uku.Na yarda da cewar dare ɗaya Allah kan yi Bature."

Suna hanya yana gudu sosai ya juyo ya kalleta."Kina ganin halin ubanki? Kina kallon duk abin da yake faruwa? Kin san baki da gatan da ya wuce gidana, amma ba za ki yi mini biyayya ba mu zauna lafiya. Wallahi in har kika ce saba mini za ki rinƙa yi sai na lahira yafi ki jin dadi."

Shiru ta yi ba tare da ta ce masa komai ba. Kuka take yi sosai har idanunta sun kubbura. Dana sanin zuwa ta duniya da tunanin makomar rayuwarta sun addabi zuciyarta, domin matuƙar mahaifinta zai cigaba da haka. Ba ta da kima da daraja a idanunsa.

Da suka isa gida, duk kukan da take yi haka ta taso ta buɗe masa ƙofa.

Fita ya yi daga motar, ba tare da ya kulle ba ya kalle ta ya ce," Ki wanke mini mota, tun da ba ki da amfani a matsayin matata, ba kya iya ɗauke mini damuwata, don haka komai ke za ki rinƙa mini."

"To," Ta furta tana share hawaye don wanke motar ba shi ne na farko ba

Har ya tafi ya dawo ya karbi wayar da laptop ɗin ya shige.

"Na shiga uku! Da na sani da ban ƙarfi kyautar nan ba. Dama ance dana sani ƙeya ce." Ta furta tana share hawaye.

"Umma, ki bar kuka ina girma sai na sanya 'yan sanda sun kama Abba." Raihan ta faɗa tana share mata hawaye.

Da ta gama wankin motar. Ƙullin kayansa ya ji ga mata ta wanke. "Kuma ki goge kafin na dawo." Ya ce mata tare da ficewa daga gidan.

Tun da ya fita take kuka. In ta tuna toxarcin da ya yi mata sai hawaye. Saboda fitan da suka yi Nasreen ba ta je makaranta ba. Ita kuma ba su da lecture sai ƙwara ɗaya kuma presentation suke yi group ɗin su sun yi.

Tana kwance bayan ta gama wankin tana jiran su bushe ta yi gugar. Maman Muwadda ta yi sallama ta shigo.

Gani ta ya karyar mata da zuciya ta fashe da kuka tare da rungume ta.

"Lafiya mai kuma ya ƙara faruwa?" Kuka sosai take yi har ta jin zuciyarta na yi mata zafi tamkar za ta fito waje.
Chapter 13 · 0% Book details