Sashe 33
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Damir
Rayuwarsa ta zama abin tausayi domin ya canza kamar ba shi ba. Abin da ya ƙara rikitar da shi. Jaririn da Batula ta bari, cikin dare ya fara zazzaɓi mai zafi bai ɗauki wani tsawon lokaci ba ya koma ga mahallicinsa. Hakan ya ƙara rikitar da shi gabakiɗaya. Ya kasa yarda an yi masa rashina lokaci guda. Har yau ya kasa yarda cewa Batula ta tafi ta bar shi. In ya kalli Little Marwana sai ya ji kamar zai fasa ihu, saboda tausayinta. Yana mugun tausayinta sosai, ganin har yau ta kasa yarda cewar ta tafi ta barta. Kullum kuka take yi masa kan ya kaita gurin Mommy. Ya yi kuka har idanunsa sun ƙafe. Baya bacci sai sallama dare yana roƙon mata yafiya. Ya rame ya susuce ya fita hayyacinsa. Ya tara ƙasumba kamar sabon mahaukaci. Ya daina shiga cikin mutane yana cikin ɗakinta rungume da hotonta yana zubar hawaye. Ganin yadda yake son ya takura kansa in ya kalli little Marwana, ya sanya mommy ta dawo gidan kullum taba sashinta. Gabakiɗayan rayuwarsa ta canza. Damir da aka sanshi da haƙuri da tausayi da girmama mutane, sai ya zama mutum mafaɗaci. Sam ba ya uzuri ga kowa. Ko Marwana da ba ya iya mata tsawa bayan rasuwar rasuwar mari biyu ya yi mata.
Ganin yadda ya tashi hankalinsa Mommy ta sanya aka kwashe hotunanta. Hatta wayarsa sai da ta sanya aka goge, amma a banza domin ya adana hotunanta a inda ko da an goge zai gansu. Ganin yana shirin kashe kansa Mommy ta sanya shi a gaba cikin kuka. Lamarin ƙara girma yake yi, domin da ya rintse idanunsa sai ya ga batula tana masa gizo. Ganin haka hankalin Mommy ya tashi kan dole suka koma gidanta.
"Damir, ba a mutuwa mahaifinka ya mutu? Allah ya halicci Batula kuma ya ɗauke abinsa. Ka tuna kai ma watarana tafiya za ka yi. Rashin yadda da kaddarar da ba ka yi ba, tamkar kana ja da ikon Allah ne.".
Rungume ta ya yi jin abin da ta ce,"Ya zan yi Mommy? Na kasa yarda cewar Batula ta tafi ta birni. Ta yi mini nisa da ba zan ƙara ganinta ba."
"Ya za ka yi? Haka Allah ya ƙaddara sai ka yarda da ƙaddarar Ubangiji. Ka yi mata addu'a."
WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme.
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg
*WASU MAZAN*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 19
Rungume ta ya yi jin abin da ta ce,"Ya zan yi Mommy? Na kasa yarda cewar Batula ta tafi ta bar ni. Ta yi mini nisa da ba zan ƙara ganinta ba."

Durƙushe wa ya yi, ya saka kuka kamar ƙaramin yaro."Ki yafe mini Batula, saboda son zuciyata. Na taimaki wata can na bar matata ta mutu! Na san cewa abin da na yi ban kyauta ba, amma ki gafarce ni. Na karashe rayuwa ta ba tare da ƙara aure ba, shi zai sanya ki gafarta mini. Mu yi rayuwarmu a Aljanna. Ni Damir ina ƙara miki alƙawarin, ba zan..."
Da sauri Mommy ta sa ya hannu ta toshe bakinsa."Kar ka yi alkawarin da ba za ka ci ba, domin rayuwarmu tana hannun Ubangiji. In Allah ya tsara za ka yi aure, babu makawa sai ka ƙara. Sannan dole ka yi aure ka haifa mini wasu yara. Dubi tarin dukiyar da Allah ya ba ka? Nufin ka ba za ka samu ɗa namiji wanda zai gaje ka ba. Dole ka yi kaffara don ba zaka ƙarashe rayuwarka babu aure ba."
"Ba zan iya ba, ba zan iya karya alƙawarin da na yi mata ba. Kuma bayan iya ba zan iya auren ko wace mace ba."
"Zan nema maka aure dole ka yi aure! Ka manta alƙawarin da ka yi mini na cika family ɗin mu da zuriya?"
"I can't mommy ba zan iya ba."
"Ka shirya gobe ka je Companyka ka ci gaba da kula da Company. Duniya babu amana mutane cuta ya yi musu yawa."
"Ban damu da na rasa komai ba tun da na rasa Batula. "Ya ce tare da shigewa cikin ɗakinsa.
"No dole za ka ci gaba da harkokinka haka rayuwa take, duk yadda muke son wani Allah ya karɓe shi. Kuka da alhini muke yi, sannan mu ci gaba da rayuwa. You have to move on, and start a fresh life."
Girgiza kansa kawai yake yi, domin ya san da wuya ya manta Batula, har ya yi farin ciki a rayuwarsa.
Kan dole washegari ya shirya cikin riga da wando na shadda sky blue, ya tafi aiki. Duk wanda ya Ganshi sai ya yi mamakin yadda ya koma. Sanin cewa shi ɗan gayu ne wanda ya iya ɗaukar wanka. Ƙasumbar da ya tara shi yafi bawa kowa mamaki.
Da isa cikin Company Muhsin ya tuka shi. Yana zaune a baya ya haɗa kai da gwiya. Hawaye yake yi sosai yana jin matsananciyar kewarta. Cikin rashin sa'a suka yi hon a get ɗin babu masu gadin gurin.
Damir da zuciya ta tuƙoshi, da sauri ya fice daga motar ya shiga ciki. Daidai lokacin da ɗaya daga cikin masu gadin gurin ya ƙara so.
Ba tare da wani dogon nazari ba, ya ƙara sa inda yake ya wanka masa mari, ji kake kau da ƙarfinsa.
"Ashe wawaye na ɗauka ban sani ba? Ina biyan ku kudi, amma kin kasa yin aikin ku?" Ya yi masa tambayar yana huci cikin tsananin bacin rai.
Da sauri Baba Bala ya kalle shi cikin tsananin mamaki. Ya san wane ne Damir da yadda yake jin daɗin kirkinsa. Matsawa ya yi, tare da dage ƙuncinsa yana mamakin marin da ya yi masa. Yadda ya koma da gashin da ya tara, yansa ya shi matsawa yana tsoro ko rasuwar matarsa ya haukatar da shi.
"Ka yi hakuri Yallaɓai."
"Ka je na sallame ku duka masu gadin gurin." Ya ce tare da fara tafiya daidai lokacin da Muhsin ya kama hannunsa suka shiga cikin campanin.
"Ka yi hakuri Yaya Damir."
"Ka tabbatar da ka sallame su." Ya ce masa tare da shiga cikin ofishin nasa. A ranar kowa ya san ba shi cikin hayyacinsa. Duk wanda ya kawo masa aiki zai yi musu fata-fata, duk da cewar daidai suka yi, amma sai ya kafe ba su yi aikin daidai ba. Mari kuwa shi kansa ba zai san mutanen da ya mara ba. Kallon tsoro ya yi ya yi masa a lokacin da ya fatattaki P.A ɗin da yana faɗin,"Nonsense, ka je na sallame ka tun da ba ka iya aikin ba."
Kwashe takaddar ya yi cikin tausayi yana kallon sa. Ya san wane ne Damir. Da irin kyautatawar da yake masa. Saboda tausayinsa bai san lokacin da hawaye suka wanke masa fuska ba.
Yana fita Damir ya watsa littafin da suke kan teburin."Na tsani kowa da duniyar da na ke ciki. Na fi buƙata na mutu na je na tarar da Batula." Ya ce cikin ƙaranci yana buga kansa da gini.
"Ka yi hakuri Ya Damir."Ya ce tare da kama shi."Mu koma gida kawai." Ya ce masa bayan ya kama hannunsa suka fita, domin in har bai koma gida ba, kafin ya tafi zai iya ƙona kampany.
Bayan sun koma Mommy hankalinsa ya tashi jin abin da ya ce."Haka rayuwa za ta tafi Damir?" Ta ce masa cikin kuka.
Rungume Little Marwana ya yi yana hawaye .
Ganin ya ƙi cewa komai Mommynta ce,"Ku shirya mu fita Ƙasar wajen wataƙila ya manta da komai."
Shiru ya yi yana kallon ya ji dadin abin da ta ce, saboda yana son ya yi nesa in da hali karya ƙara dawowa. Ya bar ƙasar ya daina tunanin wacce ta kashe masa mata tana nan a duniya tana numfashi.
Cikin ƙanƙanin lokaci suka fara shirye-shiryen tafiya. Marwana babu yadda za ta yi dole ta je makaranta don ta yi differing.