← Book details Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 40

Sashe 4

Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗakinsa ta tura ta shiga yana zaune kan sallaya da waya a hannunsa da alama lokacin ya yi sallah, don ko tashi daga gurin bai yi ba. Zuciyarta ta ɓaci ganin tsadadden murmushi da yake yi a fuskarsa, amma sallamar da ta yi ya canza fuskar daga farinciki zuwa ɓaci rai.

"Abban Hairan, ina kwana?" Ta furta cikin sanyi ta tare da danna kishinta.

Harara ya watsa mata sannan ya ci gaba da danna wayarsa tuna abin da ya faru juya.

"Da ban kwana ba za ki ganni?"

Dariya ce ta suɓuce mata, ta san dama yana da shegen riƙo shi zai ɓata maka, kuma ya riƙe mutum sai su yi sati yana jin haushinta.

"Zan wuce school."

"Na riƙe ki ne?" Ya ba ta amsa tare da ije wayarta.

"WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme.

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423

*WASU MAZAN*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan

08144072423

PAGE 3

BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM

"Zan wuce school."

"Na riƙe ki ne?" Ya ba ta amsa tare da ije wayarta.

"A'a, Allah ya ba ka haƙuri." Ta furta tana ƙoƙarin juyawa.

Tsaki ya yi tare da gyaran murya."Umma ta gaida ashsha. Kin san dai ƙwandalata ba za ta yi ciwo ba, don ban aike ki ba. Shegen baƙinciki da son gogayya da ni, ya sanya kika nace karatun. In kika gama digirin sai ki ɗaura da masters sannan Phd kin ga mun zama ɗaya."

Ba ta ce masa komai ba ta miƙe za ta tafi.

"Nufin ki ba za ki haɗa mini breakfast ba za ki tafi? Kin san dai ba zan ci wannan ɗan iskan abincin, da kika cika gishiri da barkono ba."

"Sai mu da ba mu da gata." Ta ce a ranta amma a fili narai-narai ta yi da fuska.

"Haba Abban Hairan na yi matuƙar latti fa. Kuma in ban da tsatsuba yaushe rabon da ka yi breakfast a gidan nan?"

"Saboda ban da ra'ayi yau kuma yunwa nake ji, saboda jiya don mugunta abincin da na ci duk kin ƙwaƙule ni."

Harararsa ta yi jin abin da ya ce sai ta kalli agogo.

"Don Allah ka yi haƙuri ka je ka ci a inda ka saba ci, na riga na yi latti, kuma test na ke da shi."

"Allah ya sanya exam za ki zana wallahi sai kin dafa mini abinci. Ki ma godewa Allah indomie ne, kar kuma ki ja na ce taliya ko shinkafa."

Shiru kawai ta yi ta tsaya tana kallonsa don ta san zai iya.

"Ga shi." Ya ɗauki guda uku ya miƙa mata.

"Ki hanzarta ni ma zan yi latti."

Banza ta yi da shi ta juya tana ƙunkunai."Wallahi kika zage ni saina naɗa miki na jaki kuma babu inda za ki. Dama kwana biyu ban more fata ba." Ya ce tare da komawa ya zauna wannan karon da ya ɗauki wayar kiranta ya yi suna bidiyo call.

Cikin sauri ta kunna wutar, sannan ta zuba ruwan zafi Allah ya so ta tana da shi a fulas. Da sauri ta jajjaga sauran kayan miyan da ta rage jiya. Burinta ta gama kafin lokacin ya ƙure. Bayan ta gama, ta rage kaɗan ta zuba masa sauran don ta san in ta iba da yawa, zai iya mata tijara.

"Ga shi." Ta ce tana ƙoƙarin fita.

"Ina za ki?"
Ya yi mata tambayar tare da miƙewa, ya ƙaraso inda ta ije abincin ba tare da ya kashe wayar ba.

Ranta ya ɓaci hawaye suka zubo mata a fuskarta. Kauda kanta ta yi, daidai lokacin da ya kalli wacce suke wayar ya ce mata.

"Baby, zan kira ki I love yo..."

Maganar ta katse sakamakon ganinta da ya yi ta nufi gurin wayar cikin huci.

"Na gaji Faruk! Na gaji da tozarci da wulaƙanta ni da kake yi, domin na kasa gane mata ko baiwa ka ɗauke ni. Ba ni da 'yanci da ƙimar da za ka bari ka rinƙa waya da sheɗanun 'yan matanka?"

"Matar da zan aura kike kira sheɗaniya?"

"Wallahi in da abin da yafi sheɗaniya zan kirata. A cikin gidana kake waya da ita ki kunya ta ba ka ji. Ban isa na ga dariyar ka ba, sai in kana waya da wasu matan. Ni ma fa ina da haƙƙi a kanka kamar yadda kake iƙirarin kana da shi a kaina."

"Ke dai na lura wallahi baƙicikin zan yi ajalinki. Saboda kin ganta yar duma-duma kalar madara shi ne kake tada hankalinki. To ni dama mai zan janyo mini na je na ƙara ɗauki irinki? Ina ciyar dake ana zargina ina barin ki da yunwa. Kalle ki fa Nasreen kullum sai ƙara tsukewa kike kina komawa wata tsohuwa, saboda fitinar da kika sanya a kanki. Ki kula karki jawo abin da zai sanya na tura ki gidanku, kin ga wannan ya'yan na ki da yake tada jijiyan wuya ina barin ki da yunwa, sai na barki in gani in zai iya cida ke. Saboda baƙin ciki kamar jaka haka kike."

Wasu irin zafafan hawaye suka wanke mata fuska. Ji ta yi kamar ta mutu."Ni kake kira haka?"

"Ƙarya na yi in aka dafa taliya ɗaya tana kwana ta wuni?"

"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Allah ka jarabace ni da mijin da bai san darajar mace ba."

"Ni zan roƙa Allah ya kawo mini ɗauki da ya haɗa ni da mace bagidajiya mara wayewa. Sai aikin ɗaukar jaka da sunan an tafi makaranta. Haka kika ga matan jami'a suna yi? Ko irin shigar da kike yi suke yi? Ba kya ganin mata masu kyau da zubi da tsarin da suke sace zuciyar maza?"

"Kana siyen mini kayan ne Faruk? Tun da na shigo cikin gidanka yaushe ka siya mini sutura? Ko haihuwa na yi a gidanka turmi ɗaya ke haɗani da kai. Su kuwa maza na yi musu hidima. Ko fa gida ba ka iya siya mini ka ji tsoron Allah da ranar da Ubangiji zai tsayar da mu don yin hisabi."

"Ke ma ki ji tsoron Allah ranar da Allah zai tuhume ki bisa kasa ɗauke mini ido da kika kasa yi ga matan waje. Kullum sai dai na yi ta raba idanuna kallon abubuwa a gurin matan waje, amma matata ba ta da maraba da tsinke."

"Wayyo Allahna!" Ta ce tare da zubewa a ƙasa tana kuka.

"Ki mutu gaskiya ce ɗaci gareta kuma ba zan dai na gaya miki. Sai dai ta kashe ki." Ya furta yana saka lomar abinci a bakinsa.

Kallonta kawai ta yi sai ta miƙa tsam ta saba jakarta ganin ta yi latti.
Ɗaukar Musaddik ta yi za ta fita ba tare da ta yi masa magana, daidai lokacin da ya saki tsaki.

"Kuma wallahi kika daɗe ba ki dawo ba har inda kike zan biyo ki na tozarta ki. In aka ci amanar Allah ya isa ban yafe ba."

Da sauri ta juyo yayin da hawayen ta suka ci gaba da zuba, sai kuma ta fice ba tare da ta ce komai ba. Gurin famfo ta je ta buɗe ta wanke fuskarta da wasu hawayen suke zuba.

"Umma, kuka?" Musaddik ya ce yana goge mata hawayen da ya haɗe da ruwan fuska.

Sai da ta kai bakin get ɗin gidan ta tsaya ta ciro wayarta da duk ta ragwargwaje. Da kyar ta samu ta numbata domin kashe kanta take yi. Ɓacin assignment da take yi da ita, da tuni ta yi jifa da ita tun kafin ta yi ajalinta.

Numbar Ahmad ta laluba ta yi masa peep wanda ko minti ɗaya ba a yi ba, ya kira ta.

"Ya Ahmad!" Sai kawai ta fashe da kuka.

Daga can ɓangaren ya ja ajiyar zuciya, cikin damuwa yana jin yadda kukan yake damunsa.

"Nasreen!"

"Na'am." Ta amsa cikin sheshsheƙar kuka.
Chapter 4 · 0% Book details