← Book details Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 40

Sashe 16

Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai kawai ta fashe musu da kuka sosai. Gabakiɗaya suka yi kanta.

"Mai ya faru? Suka yi mata tambayar cikin mamaki."

"Wallahi na fasa auren Ya Ashman in har haka auren yake." Ta ce tana share hawaye.

"Mai ya faru, wani abu ya yi miki?"

"Ya duketa ya fasa ya fasa mata kai, har yana cewa tana cin amanar sa, sannan ya tozarta iyayenta."

"Wa ke nan, ko ya yi aure ne bamu sa ni ba." Hajiya ta yi mata tambayar cikin mamakin kalamanta.

"Mijin Nasreen." Ta furta cikin muryar kuka.

"Nasreen?" Suka yi mata tambayar har da Damir, saboda shi ya manta da ya bawa wata kyauta.

"Nasreen ɗin da ta ke top a ajinmu wacce ka siya mata waya da laptop."

"Ohh," Ya ce tare da tunawa.

"Waye ita Damir?" Hajiya ta ce.

"Wata yarinya ce a ajinsu tana da ƙoƙari shi ne na ce zan yi mata kyauta. Ta ce na siya mata waya da laptop ta samu na karatu. Da na siya mata ta kai mata. Ina ga shi ne mijinta ya zargi wani abu." Ya ce cikin basar da zancen.

"Kuna da hankali kuwa? Dama dole ai ya nuna tashin hankalinsa, saboda yanzu duniya Babu tsoron Allah. Yin zanace-zinace ya yawaita ba 'yan mata ba, ba kuma zawarawa ba har matan aure marasa tsoron Allah suna aikatawa."

"Amma Hajiya kin ga dukan da ya yi mata? Ya fasa mata fuska, ko ina jikinta shafin duka ne."

"Bai kyauta ba saboda bai kamata ya duke ta ba." Cewar Hajiya.

"Kuma in ban da shi mahaukaci ne, iya zaman da suka yi ai ya kamata akwai yarda da amana a tsakaninsu. Ko da ace an gaya masa cewar matarsa na cin amanar sa bai kamata ya yarda ba."

"Abin da nake tunani kenan. In har babu yarda da ita ba. Ban ga dalilin da zai sanya ta zauna da shi ba. Yaran su biyu."

"Haka WASU MAZAN suke sun ɗauki mace kamar baiwa." Cewar Hajiya.

"Kuma abin mamaki she is young. Ba za ta wuce sanata ba, don zan iya girme mata." Ta faɗa tana kallon Damir da ransa ya ɓaci.

"Saboda wannan zai sa ya ki fasa auren Ashman? Ina ba zai taba aikata haka ba, kuma duk ranar da sheɗan ya sanya shi ya aikata. To nine ajalinsa. Ki kwantar da hankalinki matukar ina raye, babu wanda ya isa ya yi miki tsawa ballantana ya ɗora hannu a kanku."

"Na gode Yaya Damir, kuma ina godiya ga Allah da ya ba ni kai a matsayin Yaya. Allah ita ma ya bata Yaya kamar kai."

"Amin," Ya ce yana murmushi.

Ɗakinta ta shiga ta kulle ƙofa tare da zama kan gadon. Ɗan kwalinta ta cire cikin damuwa.

"Anya yana da imani kuwa?" Ta furta cikin takaici yayin da take ji kamar ta je ta rama mata.

A mota kuwa hankalinsa ya tashi matuƙar gaske! Ganin Marwana. Ya tabbata duk inda ta fito ta iyayenta ko mijinta suna da kuɗi.

Harararta ta gefen idanu yake yi cikin jin haushinta.

"Wallahi kin ji na gaya miki matuƙar kika ƙara kula yarinyar nan, sai na yi mugun saɓa miki, saboda daga ganin yarinyar nan, irin matan da suka gagari iyayensu ne."

Shiru ta yi ba ta tanka masa ba hawaye suke zuba a ƙuncinta.

"Wa ya sani ko 'yar lesbian ce, saboda irin wannan kyautar da ta yi miki in dai ba wani abu take buƙata daga gareni ba, to babu abin da zai sanya ta yi miki shi."

Nan ma ba ta ce masa kanzil ba, domin ba ta da abin da za ta ce.

Da suka koma gida wanka ya yi sannan ya fice daga gidan.

Tun da ya fita take kuka kamar za ta haɗiye ranta. Ta yi kukan har ta ji babu daɗi. Dana sani kuwa ya fi cikin kwanon masaki.

Ganin kukan ba shi ne mafita ba, ya sanya ta share hawayenta ta ɗauki qur'ani tana karantawa.

Sallamar Maman Muwadda ya katse mata karatun da take yi.

"So kike ki kashe kanku Nasreen? Dukan da yake miki bana hankali bane. Wallahi da na zauna da kalan mijinki gara na shiga duniya."

"Ba ni da zaɓi ne, zaman aure a shi ya fi mini kwanciyar hankali."

Ta furta tana kuk,a wanda ya sanya ta yi fushi ta bar mata gidan.

Cikin dare Marwana ta kasa bacci. Da ta rintse ido sai ta ga fuskar Nasreen tana kuka. Miƙewa ta yi ta zauna a tsakiyar gadon.

Tun bayan da ta dawo gida take ta neman layin ta amma a kulle.

Na damu da na ji halin da kike ciki Nasreen. Don Allah ki buɗe wayarki.

Ta tura mata tsaƙo kamar haka sannan ta koma ta kwanta.

Washegari da safe ta shirya don ta je makaranta.

Nasreen kamar ba za ta je makarantar ba, amma saboda gidan da ya yi mata ƙunci ya sanya ta shirya ta tafi.

Bayan ta ka Raihan makaranta ta wuce school.

Ganin ta ya sanya taso da sauri har tana tuntuɓe.

"Wallahi juya sai dai bacci ɓarawo ya sace ni. Nasreen, ban yi miki kyauta don ki samu matsala da mijinki ba. Na so ki bani da ma na yi masa bayani, watakila da ya fahimci nufina."

"Ba zai fahimce ki ba, ina son ki yi hakuri mu yanke alaƙarmu, saboda ya yi mini kashedi mai girma, daga ciki har da yanke igiyar aurenmu"

Zare idanunta ta yi sai hawaye shar suka wanke mata fuska.

"Har cikin raina na ke jin ki kamar 'yar'uwata, amma matuƙar zan zamo sanadin mutuwar auren ki zan yi nesa dake har abada, amma ki sani ya kamata ki gyara zaman auren ki da mijin, saboda mijinki bai yarda da ke ba, matukar da ace akwai yarda a tsakanin ku ba zai yi miki wannan dukan ba. Ina jiye miki gaba matuƙar ba ki gyara zaman aurenki ba, za ki yi dana sani a lokacin da ruwa ya ƙare wa ɗankada. Ina miki fatan alkhairi da zama mai ɗaurewa a rayuwar aurenki." Ta juya za ta tafi sai kawai ta fashe da kuka.

Mamakin kukan da take yi ya kamata ƙwarai. Ita kanta kukan take so ta yi. Ji take kamar ta ɗora hannu aka ta yi ta ihu, tana fadawa mutane abin da ke damunta, watakila ta samu rangwame na raɗaɗin da zuciyarta take yi."

Dama mai shirin kuka ne, aka jefe shi da kashin awaki, sai kawai ta fashe da kuka tare da rungume tana kuka.

"Ina cikin wani hali na fi buƙatar na mutu da rayuwar da nake yi. Duniya ba ta maraba da ni, kullum cikin kurɓar ruwan baƙinciki nake a cikinta. Zaman aurena ya zaman mini tamkar zaman gidan yari ko ƙangin bauta. Mijina bai damu da ni ba." Ya duke ni ya zagi iyayena, sannan babu yarda a tsakanin mu abincin da xanci baƙinciki yake ya bani."

"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Kuma kike zaune da shi Nasreen? Da kyanki da ilmin ki kika zauna baƙincikin ɗa namiji zai kashe ki? Dubi yadda kika rame kika koma duk adalilin ɗa namiji. Wallahi na tabbata kina ɗauke da ciwon depression."

"Ya zan yi? Zaman aure a shi ne kawai gatana da 'ya'yana."

"Ba ki da iyaye ne?"

Murmushin mai ciwo take tana kallonta."Wannan shine dalilin da na gaya miki zaman aure a shi ne kawai gatana. Mahaifina da shi da babu a cikin rayuwata duk ɗaya."

Zare idanunta ta yi tana mamakin abin da ta faɗa. A iya saninta iyaye sune ginshikin da kuma jigo ga 'ya'yansu. Matuƙar za ta furta haka kenan bai kasance bango abin jingina ba?

"Na san za ki yi mamakin dalilin da ya sa ya na ce miki haka. Mahaifina shi ne dalilin da rayuwata ta koma haka. Sam bai damu da rayuwarmu ba.

"Ina buƙatar na ji rayuwarki. Please mu je wani guri ki bani tarihin rayuwarki." Kama hannun ta ta yi suka shiga mota.

"A halin da na ke ciki ba zan iya ba ki labarina ba, amma na yi alkawarin zan sanar da ke wani lokacin."

Kallonta ta yi cikin tausaya jin abin da ta ce. Jakarta tana kallon Musaddik da yake son ya yi kuka. Hannu ta sanya ta ɗauke shi tana masa wasa.

"Shi kenan, zan jira ki duk lokacin da kika shirya. In sha Allahu zan samu Faruk na yi masa bayani..."

"Ba zai saurare ki ba."

"Zan jaraba saboda ya kamata na fiddaki cikin zargin da yake miki."

Ba tare da ta ce mata komai ba suka fara tafiya.

A maimakon su tafi makaranta su tafi gida ta biya da ita shopping mall ta yi musu soyayya sosai. Mamaki ya kamata ganin yadda ba ta jin ƙyashin kashe mata kuɗi.

Kamar yadda ta yi mata alkawari suka samu lokacinta ba ta labarinta. Mamaki sosai Marwana ta yi. Kallonta take cikin tsananin mamaki.

"Nasreen rabuwa da Faruk shi ne alkhari, saboda dole watarana za ku rabu."

"Bana sonsa na aure shi, amma ba ni da zaɓi saboda yarana. Bana son su samu tarbiyar wata. Uwa ita ce ginshiƙi ga rayuwar 'ya'yanta."

"To saboda yara za ki kashe kanki? Kina da tabbacin in kin ƙi rabuwa da shi zai zauna da ke? Nasreen Allah ba ya ɗorawa bawansa abin da ba zai iya ba, dai sai mu ɗorawa kanmu. Akwai buƙatar ki natsu ki yi tunanin makomar rayuwarki da Faruk. Ki rabu da shi zan ɗauki nauyin karatunki, sannan in kin gama zan sanya Ya Damir ya ba ki aiki a campaninsa. Rayuwarki za ta yi kyau za ki taimaki iyayenki, amma a haka wallahi matuƙar ba ki samar da kanki mafita ba za ki yi dana sani."

Sosai take kallonta yayin da maganganun ta duke yin tasiri a zuciyarta, amma kuma da ta suna a magantarta, dai ta ga zama da Faruk ya fi kan ta ɗora musu ɗawainiiyarta babu dangin iya ba na Baba."

"Na gode da ƙaunar da kike mini. In Sha Allahu zan ci gaba da addu'a, domin duk wanda ya roƙi Allah zai kawo masa mafita. Zan ci gaba da zama da Faruk saboda yarana."

"To shikenan tun da haka kika ce. Allah ya kaimu mu kammala karatun mu zan saya Yayana.ya ba ki aiki."
Chapter 16 · 0% Book details