← Book details Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 40

Sashe 15

Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wallahi ban taɓa cin amanar ka ba. Ba zan iya rantse wa kan wayar ba, amma zan rantse da qur'anin tun da na aurenka ban taɓa kallon wani ɗa namiji da sunan sha'awa ba. Kai ne namijin da na fara sani, kuma har yau ban taɓa kula wani ba. Ka yarda da..."

Ta kasa ƙarasa maganar sakamakon hamɓarin da ya kai mata a ciki.

Duƙawa ta yi tana jin yadda kayan cikinta ke juyawa. Jiri ya ibe ta. Da sauri ta dafe cikin tana faɗin,"Wayyo Allah! cikina za ka kashe ni."

"Eh gara na kashe ki don babu amfanin ki a duniya. Matar da take cin amanar mijinta, mutuwa ya fi a gareta. Kin ga ko banza na yi maganin irinku."

Kuka take yi sosai yana dukanta yana haurinta. Tun maƙota na jin kukan suka daurewa har suka gaza.

Cikin kuka Maman Muwadda ta kalli mijinta. "Kuna jin zai kashe ta? Saboda tsoron sa da masifarsa. Shi Allah ne? Wallahi zan fita na ɗauki icce na ragije shi." Ta furta cikin tsananin kuka.

"Me kike so na yi? Yaron nan mahaukaci ne. Kin san ba zai bar kowa ya shiga cikin gidan ba, kulle gidan yake yi. Kina sane da tozartar da ya yi mana da Alhaji Munir, saboda mun yi mishi nasiha. Ba zan shiga cikin rayuwar iyalin sa ba. Shi mahaifin na ta wane irin dabba ne?"

"Nasreen, ba da gata sai Allah. Ubangiji shi ne kawai gatanta, domin tana cikin wani mawuyacin hali. Wallahi in har ba ku taimaka wa rayuwarta ba sai Allah ya hukunta ku."

Miƙewa ya yi tare da ɗaukar wayarsa ya fice daga gidan.

Buga ƙofar da ya ji an dame shi ya sa ya daina dukanta, wacce ta yi lamo kukan ya gagareta sai nishi take yi.

"Gobe zan ɗauke ki muje cikin makarantar na tabbatar. Kuma wallahi in har ƙarya kike yi, sai na lahira yafi ki jin daɗi."

"Na yarda zan mayar mata, in haka zai sanya ka haƙura." Ta ce tana share hawaye a wahalce.

A daren ranar ta yi kuka har ta ji babu dadi. A gurin da ya gama dukanta ta samu da ƙyar baccin wahala ya ɗauke ta.

Baccin mai kama suma ta yi, sai da sanyin asuba ya fara sannan ta farfaɗo.

Cikin ƙarfin hali ta mike ta dafa ruwan zafi sosai ta gaza jikinta.

Kallon fuskarta ta yi, da yake mata wani irin zugi sai ta ga ashe ya fasa mata gefen idanunta.

Bayan ta yi wanka, ta shirya ta yi sallah tana kuka. Komawa ta yi ta kwanta har gari ya waye.

Ƙarfe tara na yi, ya sanya a cikin mota suka nufi makarantar.

Saboda yadda ya fasa mata jiki. Niƙabi ta sanya ta rufe fuskarta.

Cikin sa'a yana parking da motarsa, sai ga Marwana ta shigo gurin parking ɗin.

"Ga wacce ta bani can." Ta furta tana nuna ta da yatsa

Da ya ga motar da take hawa sai da gabanshi ya faɗi. Bai gama firgita ba sai da ya ga wata tsuleliya kyakkyawar gaske, fara mai kyawun diri da shiga ta alfarma ta fito

Idanunsa ya zare tare da kallonta, sosai bayan ya cire gilashin da ya sanya.

Jikinsa ya kama rawa yana kallonta." Irin wannan baby ɗin ne take kulata? Kai ina ni ya kamata na ta kula, amma ita ba."Ya ce yana ƙare mata kallo kamar maye.

"Ma za ki je ki bata."

"To," Ta amsa cikin sanyi tare da buɗe ƙofar ta fita.

Tun da ta fito Marwana ta bi ta da kallo, saboda tafiyarta ya yi mata kama da na Nasreen, amma kasancewar ba ta taɓa ganinta da niƙabi ba, sai ta ɗauka tafiyar ta su ce ta yi kama.

Ta fara tunanin ita ce ganin goyo a bayanta kuma tana dumfaro inda take. Ƙwayar idanunta ta kalla daidai lokacin da ta yi mata sallama.

"Subuhanallahi! Mai ya samu idanunki?" Ta yi mata tambayar, ba tare da ta amsa sallamar ba tana ƙoƙarin cire mata niƙabin

"Ga shi na dawo miki da kyautar ki. Da na san abin da zai faru a dalilin kyautar da ban karba ba. Mijina ya yi fushi kuma ya ce na mayar miki. Ki gaya wa yayanki na gode, zan ci gaba da karatuna ba tare da ina da su ba."

"Nasreen, wai me ya faru? Da ma kyauta yana zamo abin faɗa ne? Shi mijin na ki bai yarda dake bane?" Ta yi mata tarin tambayoyin tare da buɗe fuskarta.

Ja ta yi ta matsa cikin tashin hankali."Nasreen? Mai ya faru da ke?" Kawai sai kuka ta kai hannu za ta kamata.

"Ki fita daga rayuwata na ce!" Ta daka mata tsawa tana faɗin haka, sannan kuma ta ɗora da cewa,"Kin san abin da ya faru a dalilin kyautar nan? Ya ce ina cin amanar sa, kuma ya duke ni ya tozarta mahaifina. Na yi dana sanin karbar kyautar nan."

Tsananin tashin hankali ya bayyana a Kyakkyawar fuskarta. Kuka sosai ta rushe da shi ga in yadda halittun ta suka canza.

"Kina rayuwa da mijin da bai yarda da ke ba and you call this marriage Nasreen? What the hell kike yi har kika yarda namiji ya raina ki kamar haka? Dubi yadda ya canza kyakkyawar fuskarki. Kin san yadda fuskan ɗan adam take da daraja? Ko kin san darajar da Allah ya bawa 'ya'ya mata?"

"Ba na son jin komai daga gare ki, zan bi umurnin mijina saboda shi ne kawai gatan da na ke da shi.

"Namijin da zai duke ki shi ne kike kira miji?"

"Eh, saboda bani da wanda ya fishi. Ina rokonki da ki fita daga rayuwata. Na gode da taimakon ki." Ta ce tare da juyawa.

Ba tare da kula da ije mata da ta yi ba ta bi bayanta.

"Nasreen!" Ta furta daidai lokacin da ta ƙaraso motar.

Tsayawa ta yi ganin har ya tashi motar ya bar harabar makarantar.

Matuƙar mamaki ya kamata ganin mijinta na da mota. Sam ba ta taɓa tunanin mijinta yana da mota ba

Kuma mota mai tsadar gaske. Sannan shigarsa da yanayin sa ya tabbatar mata da yana da kyau da hutu, sannan ya yi karatun boko.

Kanta ya ɗauke wuta, har ta ji yana shirin sara mata. Zama a gurin ta yi cikin tsananin tashin hankali tana tunanin fuskarta.

"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Wannan aure take yi ko bauta? Ace mijin ka bai yarda da kai ba?"

Sosai hawaye yake zuba a ƙuncinta matuƙar tausayinta ya kamata. A maimakon ta fita daga rayuwata kamar yadda ta ce, sai ta ji wani irin mugun sonta da ƙaunarta, ya shiga cikin ranta har tana ji ta san rayuwar ta kuma ta san asalinta.

"Ta ce shi ne kawai gatanta marainiya ce?" Ta yi wa kanta tambayar hakan.

"A'a, ita ba marainiya nace, saboda na ji ta ce a dalilin kyautar ya wulaƙanta iyayenta." Ta bawa kanta amsa.

"To mai yasa take zaman aure a gidansa na ƙangin bauta?" Ta kasa gane dalilin haka.

Dama ta shigo ta je Library ta yi karatu ne. Faruwar abin ya sanya ta juya ta koma gida cikin tashin hankali. A hanya kuka take yi, tana tausayinta da mamakin rashin imaninsa da ya yi mata haka.

Tana isa cikin gidan ta yi parking sannan ta fito ta wuce ciki.

Mamaki sosai suka yi ganin ta dawo.

"Marwana, mantuwa kika yi?" Hajiya ta tambayeta cikin mamaki.

"A'a." Ta ba ta amsa tana zama a kan kujerar da take zaune, tare da ture Little Marwana da ta haye cinyarta tana faɗin,

" Anty."

Makaranta innsha Allahu yau zan yi posting safe da yamma a cigaba da surbubuɗo comments ❤️❤️❤️❤️💃💃💃💃
WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme.

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43

*WASU MAZAN*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan

08144072423

PAGE 10

BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM

"Marwana, mantuwa kika yi?" Hajiya ta tambayeta cikin mamaki.

"A'a." Ta ba ta amsa tana zama a kan kujerar da take zaune, tare da ture Little Marwana da ta haye cinyarta tana faɗin," Anty."

"Sis, lafiya?" Cewar Damir da yake zaune gefen Hajiya.
Chapter 15 · 0% Book details