← Book details Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 40

Sashe 40

Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Ni kaina yadda ya dumfarota sai da na tsorata na yarda sahara, amma sai na ga ba ta razana ba. To fa Nasreen anya capacity Faruk zai ɗauka kuwa? Kin ga san halinsa. To ban dai san yadda kika ɗauki alwashin ƙwatowa kanki 'yanci ba, amma bari mu ci gaba da bibiyarki.

Laifin daɗi ƙarewa😁😁😁😁
Anan na kammala littafin WASU MAZAN book one sai mun hadu a book two wanda yake na kuɗi ne 500 in aka gama 800.

Allah Sarki Nasreen baiwar Allah. Ubangiji ya na sane da halin da kike ciki kuma ba ya bacci. Ki ci gaba da addu'a kina kai masa kukan. Watarana zai ɗube ki kuma ya kawo miki sauki. Masu karatu ya rayuwar Nasreen za ta cigaba da kasancewa a gidan Faruk?😭😭😭😭

Shin za su yi zaman lafiya da Rashida? Wane irin zaman kishi za a yi🙄🙄

Nasreen za ta ci gaba da hakuri ko za ta mike ta ƙwaci yancin ta? Kuna ganin faruk zai ɗauki abin da za ta yi masa?

Garin zai yi adalci kuwa tun da ya samu kalar madara zubin ajebota ko ina a cike?😆😆😆

Allah Sarki Damir bawon Allah zai dawo Nigeria kuwa? In har ya dawo wane irin rayuwa zai yi?

Ya labarin Ya Ahmad?😭😭😭😭😭

Marwana da take addu'ar Faruk ya rabu da Nasreen har take tunani Innhar ya saketa sai ta yi duk abin da za ta yi ta haɗa soyayya a tsakaninsu har ya aure ta🙄🙄🙄🙄 s. Shin kuna tunanin haka zai yiwu? Damir zai iya kallon Nasreen har ya aure ta su zauna lafiya, bayan babu wacce ya tsana samaa da ita?

Ƙarku manta har yanzu ba mu ji Asalinsa ba, sannan ya aka yi rayuwarsu ta rikiɗe ta koma haka.

Duk za su samu amsar tambayoyinku a cikin littafin WaSU MAZAN book two wanda paid book ne kan naira 500 zai zo muku, in kuma aka gama 800. Posting safe da yamma babu fashi, domin an riga an gama book ɗin. Ga masu son shiga don su karanta sai a tura kuɗin ta wannan account ɗin. 8144072423 Jamila Lawal opay
A turo shedar biya ta wannan numbar 07072971093

Kar ku sake a baku labari ku kasa sannan ku tare har ku karanta. Wannan dai maribuciyar taku ce, mai son faranta muku da kuma.sin ganin farincikin ku. Jamila Lawal Zango Jamsy. Ta shirya ta wasa ƙwaƙwalwaarta don ta sanya ku nishaɗi. Labarin yanzu aka fara don ba a je ko ina ba. Akwai wata irin soyayya mai kama da ƙiyaya, sannan akwai gaba mai ƙarfi da take haddasuwa a tsakanin abokan hamayya biyu.
Chapter 40 · 0% Book details