Sashe 6
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
"Please kar mu yi haka dake. Na gaya miki duk wuya duk rintsi, muna tare ba zan taba rabuwa dake ba, kuma in sha Allahu za mu yi tsawon rayuwar da zamu tsufa tare."
"Ina fatan haka ina fatan na kasance da kai har abada mijina. Ka ci gaba da bani kulawar da kake bani, wanda na san ko akwai matan da suke samun kamarka ƙalilan ne. Ina sonka mijina yadda kake nuna mini tsantsan so da ƙauna. Zan yi kishin ka duk ranar da ka nuna kana son wata 'ya mace."
"Ke kadai kin ishe ni Batula, na gaya miki bani da ra'ayin ƙara mace. Kin ji kuma na rantse miki ba zan taba miki kishiya ba."Ya karashe maganar yana haɗe bakinsu.
An sha soyayya tare da biyan bashin kwanakin da ba su a tare. Bayan sun yi wanka suka rungume junansu bacci mai dadi ya tafi dasu.
Ba su tashi ba har ƙarfe huɗu saura. Shi ma bugun ƙofar Marwana ya tashe su.
"Daddy and Mommy, wake up." Suka ji tana fadi tare da buga ƙofar tana rungume da teddynta da sauri tana kiran su.
"Innalillahi! See time ban gaya wa Baba Azumi ba abin da za ta girka ba." Ta faɗa tana dan dukan filon da yake ya tashi.
Juyi ya yi tare da kai hannunsa zai rungume ta." Ban gaji da baccin ba, kar ki damu da abinci. Please mu kwanta."
"Subuhanallahi! Ashe har an yi la'asar."
Zubbur ya mike yana zare ido tare da ɗaukan agogo ya duba." Kai ina da an kira dole na tashi."
Dariya ta saki tare da sauka daga gadon." Ga shi nan na tashe ka."
Shi ma dariya ya yi yana shafa sunan kansa."Kin san lafiya ai."
Buɗe dakin ta yi Marwana ta nufa da sauri ta faɗa jikinsa.
"Baby, bari na sanar da Baba, Azumi abin da za ta girka."
"Kar ki damu ki gaya mata ta huta mu je na hada mana lunch."
"Don Allah ka gaji ka bari sai gobe." Karki damu just give me two minutes lemme go to resting room.
Ba tare da ya ji mai za ta ce ba ya shige bayin, ita kuma ta fita daga dakin bayan ta kama hannun Marwana.
"Baba, Azumi kin ga na sha bacci ko?"
"Eh, ai na so na taso ki, sai kuma na ga tun da mai gida yana nan bari na kyale ku. Na yi mana girki ni da masu aiki. Kuma Marwana ma ta ci, amma saboda ban san me kuke so ba sai barshi, don na san wataƙila mai gida zai yi da kansa."
Murmushi ta yi tana kallonta."Aiko Gara da ba ki yi ba don ya ce ki huta."
"Sanin hali, ai yafi sanin kama. Allah dai ya barku tare." Ta ce tare da komawa ta zauna, amma ganin ya shigo kicin din sai ta miƙe.
"Baby ina afron?" Ya yi mata tambayar yana amsa gaisuwar da azumi ke masa.
Dauko masa ta yi tare da ɗaukar masa sannan ta tsaya tana kallonsa.
Tana mishi hira tare da taimaka masa suka haɗa lafiyyayen abinci sannan suka dawo dining.
Shi ya rinƙa ba ta abincin, har ta ci ta ƙoshi sannan ya ci. Bayan ya ci suka koma falo suka zauna.
"Kin san rigimammiyar nan wai ni zan dauko ta a school, tun da na kira Hajiya, na gaya mata na dawo ta sanya rigima sai na zo, dama motarta ta samu matsala ba ta je da ita ba."
Dariya ta yi."Rigimarta ne kawai ya tashi, amma ko jiya a motarta muka je gidan Anty Ƴahanasu. Watakila canza mata take son ayi."
"Zan je na duba motar in tana bukatar canxawar ai sai ayi."
'Gaskiya ya kamata." Ta ce.
"Bari na shirya Little Marwana sai mu je tare."
"Ok, ka dawo lafiya." Ta furta tare da jan remote don ta canza tasha.
Shiga ya yi ta alfarma cikin suit masu kyau baƙaƙe. Wayarsa da key ɗin motarsa ya ɗauka.
Ganin kyau da ya yi Batula ta sauya wayarta za ta yi mishi hoto.
"Kai ka yi kyau matuƙa gaskiya Allah na gode maka da ka bani wannan gayen." Ta ce tare da jan kumatunsa.
Dariya ya yi ya ce," Ke ma kina da kyau ai." Ya ƙarshe maganar yana sumbatar ƙuncinta .
Har bakin mota ta raka su.
"Bye Mommy I will buy you chocolate."
"Ok baby, promise?" Ta ce mata tana daga mata hannu. Juyawa ta yi cikin farinciki ta koma ciki.
Nasreen kuwa, a lokacin da mai mashin ya sauke ta da sauri ta saɓa Musaddik ta fara tafiya. Tana tafiya ta tana kallon agogo ganin lokaci ya wuce har da minti goma. Ta san Malamin yana da tsananin zafi Allah ya sa ya barta.
Cikin sa'a ta shige ciki lokacin hankalinsa na kan ɗalibai da yake raba musu gurin zama.
Da sauri ta ji an kama hannunta ana faɗin," Ummu Hairan, zo mu zauna a nan." Ta ce mata tare da jan hannunta suka zauna.
Lecturer na kallonta ba tare da ya ce komai ba.
"Kin yi matuƙar latti, har na fara tunanin ko ba za ki zo ba? Ina ta waige-waige na kuma tambayi wannan matar auren da kuke zuwa tare, sai ta ce mini wai ta kira numbarki ba ya shiga. Wannan dalilin ya sa ya na ban karɓi numbarki ba."
Yaƙe ta yi mata jin abin da ta ce, tana mamakin maganar da ta yi mata, domin za ta iya irga maganar da suka yi. Shi ma gaisuwa ne in sun haɗu a masallaci sai kuma in tana son assignment ta tambaye ta.
"Kin san am manna mana result?" Ta yi mata tamabayar cikin murna.
"A'a." Ta ce mata tana kallonta tare da kallon kayan alfarmar dake jikinta.
"Wallahi an manna. Ai tun jiya muke sa rai. Yau kuwa tun asuba na sanya Ya Muhsin ya kawo ni, na duba daga ke sai ni."
"Alhamdulillah!" Ta ce mata.
"Gaskiya kina da ilmi sosai kamata ya yi da result da kike beating gwamnati ta ɗauki nauyin karatunki, but you know how situation we are in Nigeria."
"Haka ne Allah ya rufa mana asiri." Ta ce tare da kama bakinta, ganin yadda yan ajin suke kallonta don Marwana ba ta cika kula kowa ba harkar gabanta take yi.
"Mu fara test ɗin." Ta ce bayan an rubuta a allo.
Ajin ya yi shiru, kowa na ƙoƙarin nuna ilmin da yake da shi, yi sai kuma masu ƙuskus 'yan satan amsa.
Marwana tana rubutu tana satan kallonta, dama so take ta ga satan amsa take yi, ko ƙoƙarin ta yake ba ta result ɗin, saboda so take ta ga babu wanda yake gabanta a result ta yadda Ƴaƴanta zai kaita abroad ta yi masters.
Ta cika mamakin ganin yadda ta cika paper. Ta yaba da ƙoƙarin ta domin tun da ta fuskar da kanta ba ta ɗago ba. Ganin gulma zai sanya ta ɓata lokacin ta ya sa ta fara rubutawa.
Bayan sun gama sun fito." Zo mu je mu ci abu yunwa na ke ji."
"No karki damu bana jin yunwa."
"To don Allah ki raka ni." Ta ce tare da karbar Musaddik da ta ije shi a gurin wata yar ajinsu kafin ita su shiga.
Murmushi yaƙe ta sake yi ganin yadda idanun ke kallonta.
Lura da hakan Marwana ta yi, sai ta kamo hannunta, suka fara tafiya har suka isa cafateria.
Abincin da ta yi oder ya yi matuƙar razana ta.
"No sis ba zan ci ba, na ci abinci daga gida."
Bata rai ta yi tana kallonta." Sheɗan ne kawai yake maida hannun kyauta baya."Ta ce tare da yin raurau alamun za ta yi kuka.
Dariya ta ɓata tana mamaki shagwaɓa irin na 'ya'yan masu da shi.
"Na ƙoshi ne fa so kike na yi amai?"
"Ok, ba damuwa bari na sa ayi miki a sanya mini a leda. Sai ki bawa kyakkyawan yaron ki ya ci. "
Murmushi ta yi ba ta ce komai ba. Mamakinta ta yi ganin yadda take ci tana bawa Musaddik a baki ba tare da ƙyamar sa ba.
"Kin ga kishin ki na ke yi fa."
Jin abin da ta ce ya sa ta ɗago tana kallonta da sauri.
"Kishi kuma ni? Mai na ke da shi har da kyakkyawar mace kamar ki, wacce take da kyau kamar an kyankyaso ki aka yi za ta yi kishi da ni?"
"Ilmin ki mana. Wallahi tun muna hundred level na ke jin haushi ke ce kike zuwa a gabana, domin da ni ce top a ajinmu yanzu ina abroad, kuma kin ga irin wannan kishin ai ya halasta ko addini sai na dage na wuce ki."
"To shi ne na ba ki da matsala. Wannan semester zan yi yadda za ki wuce ni sai ki cika burinki."
"Wow, sis you are so kind."
Murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba.
Wayarta ya yi ƙara sai kuma ta mike."Yauwa Yaya Damir ya iso. Zo mu je ku gaisa."
"No, kar ki damu kawo shi kawai." Ta ce mata bayan ta miƙe. Ita sam ba ta son shiga harkar masu da shi. Gara ta tsaya a matsayinta.
Za ta riƙe ta sai ta ga ta canza fuska. "Bari na je kawai tun da ba kya son zuwa, amma zan je da Musaddik."
"Ok, ki gaishe shi." Ta furta tare da wucewa.
"Oyoyo Yayana." Ta ce tare da rungume shi.
"Marwana, yaushe kika fara ɗaukar yara?" Ya yi mata tambayar yana kallon babyn.
Dariya ta yi ita ma shi take kallo." Ka ganshi kyakkyawa ko?" Ta furta tare da miƙa masa shi.
Hannu ya sa ya amsa yana fadin,"Eh, Allah ya sanya Mommy Little Marwana ta haifa mini kalarsa."
Hannunsa ta kama suka shiga cikin makarantar tana faɗin,"Mu je ka ga result ɗin mu."
Babu musu suka shiga ya tsaya yana dubawa."Gaskiya ƙanwata kanki na ja, amma wace ce wacce ta sha miki gaba?. Ni kuwa zan so na ganta."
"Maman yaron nan ne, kuma abin mamaki daga shigarta ba matar mai kuɗi bane" Ta nuna Musaddik dake hannunsa, bari na kira ta.".
"Ai shi Allah ba ruwan shi da duba wannan ya ba ka ilmi. Ki dage ki wuce ta kin ji."
"To bari na kira ta."