Sashe 5
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kina ji na ko? Kiyi haƙuri har yau ita ce kalmar da zan rinƙa baki. Na san halin da kike ciki, amma wallahi kin ji na rantse miki zaman gidanki yafi miki kwanciyar hankali. Ki karbi jarrabawar aurenki. Ubangiji yana sane dake. Ni kaina ina cikin damuwa. Jiya wallahi ba mu yi bacci ba, saboda ciwon Mama ya tashi. Yanzu haka na sanya Zainab ta gyara ta zamu wuce asibiti, kuma Baba ko ƙwandala bai bamu ba, tun da ya shigo ya yi mata sannu ya fice daga gidan."
Damuwarta ta ƙara yawa har ta ji dama ba ta kira shi ba.
"Yaya, Faruk baiwa ya ɗauke ni ba mata ba. Ina cikin damuw.."
"Hakurin da kike yi ki ƙara, yanxu zan sanya miki dubu ɗaya na san za ta ɗan yi miki kuɗin mota da ko gurasa ki ci a makaranta. Za mu wuce da Mama asibitin in an kwantar damu zan kira ki, sai ki taho in kuma dawowa mu ka yi duk zan gaya miki."
"Don Allah ka bani ita na gaishe da ita."
"Ba za ta iya ɗaga waya ba. Ki je makarantar Allah ya tsare."
"To Yaya Ahmad, ina dawo zan biyo, kuma ka bar kuɗin ina da sauran ɗari biyar, da ka bani ranar Monday na yi amfani da sauran na ije. Ka je ka kula da ita, zan tafi a mashin tun da na yi latti ina dawo sai na tako."
"Karki damu juya na yi aikii na samu kudi, saboda don ciwon Mama ya tashi dubu biyar zan tura miki."
Tausayinsa ya kamata ganin yadda yake ɗawainiya da ita." Na gode Allah ya ƙara budi ya biya maka buƙatunka."
"Amin ƙanwata." Fatana ki ci gaba da fito da sakamako mai kyau ki samu aiki ki tallabi rayuwarki."
"Da kuma na bukatun da na Mama da sauran ƙannina."
"Ina sha Allahu." Ya ce mata yana murmushi tare da kashe wayar.
Maganar da ta yi da shi, ya sa ya ta ji ɗan dama sama-sama, har ta iya taran acaɓa ta hau zuwa bakin get ɗin makarantar.
Wani ƙaton tangamemen falo ne wanda yake ɗauke da kaya na alfarma. Tabbas falon ya cancanci waɗannan kaya da aka shake falon dashi duba ga yadda ya tsare an kashe dukiya tamkar aljannar duniya.
Wata farar mace siriya take zaune da 'yarta ɗaya wacce take kan cinyarsa tana bacci.
Kyakkyawar matar waya ce a hannunta tana chatting, yayin da fuskarta ke bayyanar da wani irin tsantsan annuri, wanda zai tabbatar maka da wanda take chatting ɗin da shi mutum ne mai daraja da ƙima a gurinta. Darajarsa da ta wuce darajar gwal da Dirhami.
Murmushi ta yi, tare da amsa kiran da ya yi mata domin iya chatting ɗin ba zai gamsar da zuciyoyinsu ba. Sun dade suna waya tamkar ba za su rabo ba, sannan daga bisani suka yi sallama bayan ta yi masa kiss din da iya ƙwaƙwata ba zan iya lissafawa ba.
Kashe wayar ta yi sannan ta shiga cikin galary ta yi ta kallon hotunansa, duk da cewar akwai wani mai kyau wanda ya ɗauka da kayan saurauta a fuskar wayarta, amma bai ishe ta ba.
Hankalinta ta mayar kan tanƙamemen tibin bangon, da take kallo a cikinsa kafin ya kira wayar.
"Mommy, yaushe Daddy zai dawo?" Yar kyakkyawan yarinyar mai suna Marwana ta furta tana murza idanunta da bacci ba su gama sakin su ba.
"Daddy will come back tomorrow. Ok?"
"Yes, kuma ya siyo mini teddy ɗina?"
"Sure."
"Mommy how many?"
"Ten." Ta ba ta amsa wanda ya sa ta daki dariya tana tsalle murna.
"Mommy call daddy I will give him a peck."
"Ok,"Ta ce tare da ɗaukar wayar tana ƙoƙarin kira.
"Hello, babies." Ta ji muryarta cikin bazata ya buɗe ƙofar falon yana faɗin haka tare da ware hannunsa.
Tsananin mamaki ya kamata, duk da cewar ya saba yi mata bazata, duk tafiyar da zai yi baya gaya mata lokacin da zai dawo. Wani lokacin in ta rage kwanakin sai ya ƙara in kuma ta ƙara sai ya rage, wannan dalilin ya sa sam ba ta shiri in zai dawo, duk da cewar da ma ko da yaushe cikin gayu da ƙwalisa take mace ce wacce take kula da kanta, saboda sanin mijinta kamar Bature yake. Akwai son classical things musamman ga matarsa. Everything na sa it is extraordinary and rare.
Da gudu suka ruga har da ita da take ɗauke da ƙaramin ciki wata huɗu."
"Oh no, baby easy." Ya furta tare da ƙarasowa ya haɗe su duka ya rungume yana kissing.
"I really missed you my babies like crazy!"
Dukan ƙirjinsa ta yi cikin wasa tana harararsa." Yanzu shikenan an tauye mini wannan yaƙin?"
"Subuhanallahi! Baby don't say that. Hakkinsa wajibi ne da ya kamata na sauke ke. Faɗa mini waya, mota jari ko abroad kike son zuwa? Ko kuma gidan ne kike son canzawa. In ma nine na fara miki tsufa sai na yi kwaskwarima You know." Ya faɗa yana kashe mata ido da cige lebbensa.
Dariya ta saki tana kashe masa ido sai kuma ta ɓata fuska.
"Haƙƙina da ake tauye mini, na rashin gaya mini lokacin da za a dawo don na gyara kaina, ta yadda zan sace zuciyarka na zama ni kaɗai."
"Aike kadai ce babu wata fa? Kin ga nan ɗina?" Ya nuna mata ƙirjinsa.
Dariya ta yi tare da ɗaya mata kai ta sumbaci goshinsa.
"Ke ce dai ke ba wata sai ke. A jirgi haka wata haɗaɗɗiyar bab ta rinƙa kallonta tana kashe mini ido. Ina gani na yi maza na ɗauke kyalle na rufe fuskanta har muka iso Nigeria."
"Oh my goodness baby, you are so funny." Ta ce masa cikin dariya wanda shi ma ya taya ta.
"Amma duk da haka I have to know."
"Do not worry ke fa zazzafa ce kullum a hot kike."
"Let's go and do shower then eating."
"No, shower then sleeping am very tire. Bacci ne kawai zai dawo dani daidai."
Hannunsa ta kama duka haye sama yana rungume da ita. Ji yake kamar ya kasheta don so.
Tun da yake bai taba son abu kamar ta ba sai ƙanwarsa Marwana. Hakika yana matuƙar don waɗannan halittu guda biyu kafin kuma ya haifa masa babu girl ya sanya mata, little Marwana da babu na biyu ta a duniyar sa.
Bayan ya yi wankan, ba ta barshi ya kwanta ba sai da ta ba shi tea mai zafi yana kauda fuska tana rarrashinsa. Sannan ya subbaci Marwana da ta yi bacci ya ɗauke ta.
"Bari na kaiwa Baba Azumi ita na dawo ki bani labarin baby na kuma tabbatar da lafiyarta, saboda shi zai watstsake mini gajiyata."
Dariya ta yi ba tare da ta ce komai ba sai raka shi da idanu da ta yi cikin so da ƙauna.
"Gaya mini duk abin da ya faru da bana nan?"
"Babu sai kewarka da kwana rungume da filo tun da babu kai."
"Karki damu jaririyata. Yau za ki yi filo dani har ki gaji." Ya ƙarshe maganar yana tusa kansa a cikin yar yaloluea rigarta.
"Kin je check up?" Ya yi mata tambayar bayan ya ɗago kansa tare da mayar da hankalinsa gareta.
"Na je Muhsin Hajiya ta Turo ta ya kaini. Likitan ya ƙara tabbatar mini aiki dole za a yi mini. Kamar na Marwana."
"Kar ki damu,ni kaina na fi so ayi miki aikin. Kin ga ba ki da wata isashshiyar lafiya ga condition ɗin ki. I think aikin will be saved."
"Ok," Ta ce tare da share hawayen da ya zubo mata.
"Please kar mu yi haka dake. Na gaya miki duk wuya duk rintsi muna tare ba zan taba rabuwa dake ba. Kuma in sha Allahu za mu yi tsawon rayuwar da zamu tsufa tare."
WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme.
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43
*WASU MAZAN*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 4