Sashe 27
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ke ce aka ibi jinin ɗana aka sanya miki ko? Wallahi in har ya mutu sai na ɗauke ki daga ke har dangin ki har sai igiya ta yi rara."
Jin abin da ta ce hankalinsu ya tashi. Suna kallon Marwana da take kuka cikin dana sani. Ta yi ninyar alkhairi sai ga shi ya koma ya zama tsiya. Ba ta ƙara shiga tashin hankali ba sai da ta ji Hajiya tana musu zagin fitar arziki. Ta rintse idanunsa cikin kuka ta kama hannunta.
"Ki hukunta ni wallahi bata da laifi."
Kau ta ƙara kaureta da mari."Ina nan zuwa gunki dama ba kyale ki zan yi ba."
Batula ce ta shigo cikin ɗakin tana haɗa hanya, Saboda kishi da ya rufe mata idanu ba ta gani. Kan gadon da take kwance ta ƙara da tana kallonta cikin tsanannin tsana
Tun da take a rayuwarta, ko 'yan mata ba ta taɓa ganin Damir ya kula su ba, sai matar aure wacce take talaka? Kai ina akwai lauje cikin naɗi! Anya ba asiri suka yi wa mijina ba, saboda ta samu ta kashe aure ya sake ta?" Ire-iren waɗannan tambayoyin suka cika mata zuciya, tare da makantar da ita, har ta kasa tuna waye mijinta da abin da zai aikata.
"Banza jaka da aurenki kike bibiyar mijin wata, har a rasa jin da za a sa ya miki sai na mijina, wato ga ki mai iya asiri kin yi masa asiri ya zama miki bita zaizai don ki shiga cikin ɗaula ko?"
Tsananin mamakin abin da ta furta, ya sanya ta ji tamkar an ɗora mata dutsen dala. Wasu irin zafafan tagwayen hawaye suka sauka a ƙuncinta. Zare idanunta ta yi tana kallon Batula jin abin da ta ce. Hakan ya tabbatar mata da ita ce matarsa.
Kalaman ta suka tayar da hankalin Marwana matuƙa gaya! Da sauri ta ƙarasa gabanta ta ce,"No Anty Batula, don girman Allah ƙarki wulaƙanta ta wallahi ba ta da laifi." Ta ƙarashe maganar cikin kuka ta haɗa hannunta tana roƙonta.
Tureta ta yi cikin tsananin zafin kishi."Wallahi jinin nan ba zai ƙarasa shiga cikin jikin ki ba, domin ba zan bari jinin mijina ya yi yawo a jikin wata ba." Ta kai hannu za ta fisge sauran ragowar jinin da ya kusa karewa.
Damir bayan ya farfaɗo, cikin dauriya ya fito daga cikin ɗakin da aka kwantar da shi, ya nufi inda aka kwantar da Nasreen hankalinsa a tashe. Ya san cewa yadda ran Hajiya ya ɓaci, sam ba za ta yi musu da daɗi ba. Sannan yana kallon irin kallon, da Batula take masa a lokacin da ta ji an ibi jininsa.
Yana daidai ƙofar ɗakin ya ji mugayen kalaman da take faɗi. Kansa ya sara, da sauri ya dafa bango jin abin da take fadi."Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Ya Allah taimako na yi sam zuciyata babu mugun nufi." Ya furta tare da shiga cikin ɗakin, daidai lokacin da ta yi nasarar fisgo allurar dake soke a hannunta.
Wani irin ƙara ta saki tare da rintse idanunta, tana jin tsananin azaba, yadda yake shiga cikin ƙwaƙwalwarta.
Da sauri Marwana da Faruk suka yi kan gadon, ganin za ta cutar da ita.
Hankalinta ya gusar da tunaninta, burinta kawai ta hana jinin mijinta shiga.
Ji ta yi an riƙe hannunta da sauri ta juyo.Ganinsa tsaye yana nishin wahala ya sanya ta fashe da kuka.
"Jininka fa ka yarda aka sanya mata zai rinƙa yawo a jikinta?Ni da bana fatar ka kula wata mace, amma sai ka yarda ka bada jinin ka aka sanya mata. Matar auren kake so?"
"Kau ya kaureta da mari jin abin da ta ce?" Kina da hankali? Ransa ya ɓaci! Idanusa suka firfito. Gabakiɗaya jijiyoyin jikinsa suka tashi."Kin san abin da kike faɗa? Taimako na zama sharri ne?"
Riƙe gurin ta yi tana hawaye jin abin da ya ce. "Marina ka yi, da tsohon cikinka a jikina?" Ta faɗa tana dage ƙaton cikinta da yake barazanar fitowa a kodayaushe.
"Kin cancanci fiye da haka Batula in har iya tsawon rayuwar da muka yi babu yadda a tsakaninmu."
Dukansa ta shiga yi a ƙirji tana faɗin,"Ka gaya mini ta yaya zan yarda da kai, bayan ka aikata abin da ko a duniyar mafarki ba zan yarda ba?"
Jikinsa ya yi sanyi duk da cewar bai ga lamarin da zafi ba, domin saboda Marwana ya yi, kuka ta san a rayuwar sa zai iya komai anything for her."
Jikinsa ya ƙara yin sanyi sosai, domin zai iya cewa wannan shine karo na farko, da ya taɓa kai hannu a cikinta. Hankalinsa ya tashi har yana jin ba zai yafewa kansa ba, ga tsohon ciki a jikinta."Kiyi haƙuri bai kamata ki yi mini wannan zargin ba, saboda kin fi kowa kusanci da ni. Ka da ki bari kishi ya rufe miki ido. Wallahi ban taɓa ganinta ba, kuma na taimake ta saboda Marwana." Ya ƙarashe maganar yana ƙoƙarin kamota ganin yadda take cige baki.
"Karka taɓa ni! Na tsane ka bana sonka mayaudari kawai." Ta ce masa sai kuka ta dafe cikinta tana nishi da ƙyar.
"Please kar kishi ya sa ya ki illata mini kanki da baby. Wallahi na rantse miki ban taɓa son wata ya mace ba, bayan ke ballantana matar aure."
"Anty Batula ki yarda da shi kar ji jawowa kanki wata cutar. Kin san a cikin satin nan za ki..."
Hajiya ce ta ƙara sauke mata mari."Rufe mini baki shashasha kawai, duk abin da ya faru ba ke kika kawo ba, saboda ba ki da hankali da tunan.." Maganar ta tsaya sakamakon Batula da ta dace cikinta ta ce,"Wayyo Allah!"
"Bayana, cikina, marata." Ta furta cikin gigitaccen ƙara.
"Please Batula, kar mu yi haka dake. Kar ki yi ƙoƙarin haihuwa kin san C.A sa a yi miki." Ya faɗa yana dakatar da ita da hannu, amma ina ya makaro, domin kafin wani lokacinta fita hayyacinta.
Hannu ya kai zai kamata sai ta ture hannun, ba tare da ya kula ba, cikin tsananin tashin hankali ya sungume ta zuwa cikin ofishin likita. Ganin halin da take ciki ya ruɗe yana kallonsa."Ka na sane da aiki za a yi mata, mai ya sa ka bari ta fara naƙuda da kanta?"
"Please we don't have time. Intentionally ya faru, don Allah ka duba ta." Ya faɗa tare ɗa ƙara matsawa gurinta daidai lokacin da ta kira sunansa ta ƙara ƙankame. hannunsa.
"Wayyo na shiga uku! Mutuwa zan yi!" Ta furta cikin tsananin tashin hankali tana nishin wahala. Jikinta zufa ya jiƙata sosai har ɗiga take. Kafin wani lokaci ta fita hayyacinta. Naƙuda ta taso mata gadan-gadan.
"No ba za ki mutu ba, don Allah kar ki haihu ki bari ayi miki aiki." Ya furta yana ƙara riƙe hannunta.
Tofa Batula wannan kishi haka?🙄🙄🙄 Wai Allah lamari fa ya rikice har na kasa cewa komai, saboda mai haihuwa akwai tausayi. Allah kawai ya san wahalar da iyayenmu suka sha. Allah ya ba su lafiya. Wannan page ɗin na duk wata uwa ce. Batula Allah ya sauke ki lafiya.
WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme.
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg
*WASU MAZAN*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 16
Duƙawa kan gadon da aka kwantar da ita ya yi. Cikin wani irin yanayi yake kallonta, ganin yadda ta fita hayyacinta."Saboda kishi sa ki yi mini asarar rayuwarki."
"Ka taimake ni, su cire mini cikin nan mutuwa zan yi, ka taimake ni ka sanya su cire mini cikin."
"No, ba za ki mutu ba, saboda inhar kika mutu, ni ma mutuwa zan yi." Ya furta yana tofa mata addu'a.
Ganin cikin ƙanƙanin lokaci ta fita hayyacinta. Hakan ya tayar da hankalin likitocin da su Damir. Tun sun ganin lamarin da sauƙi har ya tsananta.
A lokacin da Doctor ɗin ya fito yana share zufa. Da sauri ya ƙarasa gunsa."Kana ganin za ku iya ko na yi mata viser?"
Dafa kafaɗunsa ya yi,"A halin da take ciki ba za ka iya fita da ita ba. Ka yi mata addu'a domin matarka tana cikin wani yanayi."