Sashe 11
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme.
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43
*WASU MAZAN*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 7
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
"Kin ci abinci?"Tambayar da ya yi mata, ya sanya ta kasa amsa masa.
"Na san kema ba ki ci tuwon ba, tun da babu daɗi." Ya ƙarshe maganar tare da kama hannunta yana mata wani irin kallo ƙasa-kasa."Ga shi na siyo miki." Ya miƙa mata ledar da ta kasa amsa sai dai ya ɗora mata a jiki.
Ganin ta kasa ɗaukar ledar, tana mamakin sabon salon da ya fito da shi, wanda za ta iya cewar tun farkon amarcinsu. Aka yi yunwa halin kowa ya fito, ya dai na siya mata.
"Ki buɗe ladar mana, sai ki ije wa su Raihan na su." Ya ce mata wanda ya sanya ta yi namijin ƙoƙarin buɗewa..
"Ikon Allah! Tabbas akwai abin da ya shirya." Ta ce a ranta, amma kuma ta san dai cewa ba don haƙƙin kwanciya zai yi mata wannan tattashin ba, saboda zai iya sanya ƙarfinsa. Gabanta ne ya faɗi da zuciyarta ta ayyana mata ko aure zai yi.
"Kai ina ba aure bane, domin bani da ƙimar da don zai shigo da wata sai ya tattashe ni. To mene? Allah kaɗai masani da shi da ya shirya." Ta ba wa kanta amsa.
Ba ta ƙara shiga cikin tsananin mamaki ba, sai da ta buɗe ledar. Wasu irin haɗaɗɗun kaji guda biyu da Rufaida yogot.
"Na yanka maka ne?"
"A'a, na ki ne ke da yara ku ci." Ya ce yana murmushi tare da shafa bayanta.
Cikin tsoro da fargaba ta ci kazar da yogot ɗin, domin zuciyarta cike da fargabar abin da za ta biya da shi, don ta san in har ta kasa biya, sam ba zai yi mata sausauci ba.
Sai da ta ci ta kammala ta kora da ruwa, sannan ya kalle ta ya ce,"Ga shi daga yau za ki fara sha." Ya ce mata tare da ɓarewa ya miƙa mata sannan ya tura mata ledar ƙullin magani.
Cikin tsanannin mamaki ta kalli ƙullin maganin"Na sha magani, ba ni da lafiya ne?" Ta yi masa tambayar cikin zallar mamaki tare da juya ƙwayar maganin a hannunta.
"Ban sani ba, jahila ce ke da ba za ki duba ki ƙaranta ba?" Ya ce mata da ɗan ɗaga murya duk da yadda ya so ya danne zuciyarsa.
"Supplements na gyara jiki Abban Raihan ka siyo mini? Ce maka aka yi ina muzanta da yanayin surata?"
"A'a, saboda ina buƙatar na ganki kin zama 'yar duma-duma komai yana rawa a jikinki."
"You must be jorking Abban Raihan, don wallahi ba zan sha abu da zai cutar da ni ba."
"In da kuma kika yi kaɗan kenan, don ko ɗure zan yi miki sai na yi. Su sauran matan da suke sha mutuwa suka yi?"
"Akwai yiwuwar sun mutun, domin mata nawa na ji labarin shan supplements, na ƙara girman halitta ko canza fata ya sanya sun kamu da cutar kansa? Ni ba zan sha abin da zai cutar da ni ba, saboda ban taɓa jin na raina halittar da Allah ya yi mini ba. A haka ka ganni ka aure ni, in da ka san mace mai ƙiba kake so da ba ka aure ni ba."
"Sai kuma na yi laifi don na taimaka miki? Saboda na tabbata da ban aure ki ba, kina can kin yi kwantai. Ni ɗin ma tsautsayi da ƙaddara ya ja mini, in bacin haka ba zan sa ya kuɗina na auri mace kamar ki ba. Ke babu biyayya bare iya kissa da kwantar mini da hankali, sannan ɗan jikin ma ba za ki yi ba."
"Ni fa duk abin da za ka ce ba zan sha ba."
"Ki sha maganin nan tun kafin raina ya bace."Ya furta cikin ɓacin rai yana kallon ta.
"Ba zan sha ba ko kashe ni za ka yi." Ta ba shi amsa za ta wuce.
Fusata ya yi, tare da zare mata idanu ko mai ya tuna oho ya sausauta murya ya riƙe mata hannu. "Babu wani illa da yake sawa fa. Abokina ga ya siya wa matarsa, shi ne ni ma na ce zan siya miki. Da ma na sha tambayarsa yadda matarsa komai ya ji, ashe wannan maganin yake siya mata. Za ki sha safe da rana."
"Ka san yadda na tsani magani shi ne kake cewa na sha. Ni ba zan zama 'yar kwaya ba."
"Karɓa kisha tun muna mu biyu."
Tsaki ta ja za ta wuce. Kau ya kaureta da mari. "Ina wasa dake zan miki umurni ki musa, sannan kuma ki yi mini tsaki?"
Kuka ta fashe da shi tare da dafe ƙuncinta."Wallahi ko kashe ni za ka yi ba zan sha ba."
Ganin ya nufe ta da sauri ta ruga da gudu ta shige ɗaki ta kulle ƙofa.
Dukan ƙofar ya shiga yi, cikin tsananin fushi yana faɗin," Ki buɗe ƙofar na kafin na ƙaryata na canza miki halitta. Kin san nawa na sanya na siyo miki?"
"Ba zaka iya bani abinci masu gina jiki ba na yi kyau, sai dai maganin da zai cutar da lafiyata to ba zan sha ba." Ta ce mishi tare da kwanciyarta.
Tana jin yadda ya rinƙa buga ƙofar, amma ta yi banza da shi har ya gaji ya je ya kwanta.
Da safe komai a cikin ɗakinta ta yi, kasancewar asabar ce ta yi zamanta a cikin ɗaki har ya fita, sannan ta fito ta girka ragowar indomie guda ɗaya ta bar musu. Kamar yadda ba ta yi tunanin zai bar mata abin da ya siyo mata ba, haka ta zo ta ga ko ƙashi babu.
Wasan 'yar ɓuya suka fara har sai da suka yi kwana biyu. Ita ce ta fara gajiya da ɓuyan don kuɗin hannunta ya ƙare, sai garin kwaki da awara take ci. Ga shi Monday aka shiga dole ta nemi abin da za ta rinka bawa Raihan.
Ranar Monday duk yadda ta so ya kulata ya ki. Har duƙawa ta yi ta bashi hakuri, amma bai kulata ba ya sa kansa ya fice.
"Cikinku zai gaya miki." Ya faɗa yana murmushin mugunta.
Idanunta ya raina fata. Ahmad ta kira ya tura mata da dubu ɗaya, ta siya wa Raihan abin da za ta ci a makaranta sannan ta wuce school.
Marwana
Kamar yadda ya yi mata alkawarin ya siyasa, Nasreen laptop mai kyau da waya tsaddadiya Rungume shi ta yi cikin farinciki.
Dariya kawai ya yi mata ganin yadda take murna sosai.
Bayan sun tashi daga makarantar. Nasreen na ƙoƙarin fita daga ajin ta ƙara so gurinta.
"Ummu Raihan hanyarmu ɗaya, amma ba ki taɓa cewa na rage miki ba."
Murmushin yaƙe ta yi, don tana tunanin abin da za ta ci in ta koma.
"Ba haka bane. Na ga ke da ƙawayenki kuke tafiya."
"To daga yau babu wanda zai ƙara shiga mini mota, daga ke sai Musaddik."
Zare idanunta ta yi, jin abin da ta ce."Ayi haka? Mu dai shiga tare in ba zan takura ba?"
"No, daga ni sai ke za mu rinka komawa gida." Daɗi ta ji sosai domin duka ɗari biyu ta rage mata ba zai isheta ba.
"Bari na shiga, amma kar ki hana su." Ba tare da ta ce komai ba, ta buɗe mata gaba ta shiga sannan ta zagaya ta shiga ta tada motar.
Sun yi nisa babu wanda ya ce uffan. Marwana ta waiwayayo ta kalleta tare da mayar da hankalinta kan tuƙi.
"Hala tunani exam kike yi da aka sanya time table?"
"A'a, mai kika gani?" Ta ce mata tana kallonta.
"Babu." Suka yi shiru na 'yan daƙika.
Marwana tana mamakin yawan shirin da take yi.
"Kalli wayar nan da laptop ɗin na sun yi kyau?"
"Wow, sun yi kyau sosai wallahi."
"To na ki ne."
Tsananin mamaki ya sanya ta kalleta da sauri.
"Ni kuma?"
"Eh, Yayana ya siya miki."
Ranta ne ya ɓaci sosai." Saboda kin ga wayata shi ya sa kika sa ya siya mini? Bana buƙatar su domin wayar nan da kika gani tana mini komai."