Sashe 10
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ki gaya masa ba zan iya ci da mutane biyu ba. Ke kaɗai na aura, kuma ina da abin yi da kuɗina. Kar ya ƙara tambayata bashi."
"Ka gaya masa da bakinka tun da shi ya roƙa ba ni ba."
"Amma saboda ina aurenki ne ko? Ai tushiya mafarkin dawa."
Sosai ta fashe da kuka ta kasa cewa komai sai kallon sa take yi.
Tsaki ya ja tare da zama a kan kujera."in kin gama kukan kike ki ɗora mini girki, kuma yau tuwo da miya na ke jin ci."
Zare idanunta ta yi tana kallonsa tare da barin kukan."Tuwo da miya fa kace a wannan daren. Yau ma fa ba ka dawo da wuri ba, dubi lokaci sha biyu saura?"
"Ai kin san makaho ne ni. Kuma ai ba a dare a girki. Shi na ke jin ci, kwana biyu ba ci ba."
"Na gaji ni ba zan iya ba." Ta furta masa. A ranta kuwa cewa ta yi." Bana jin yunwa babu wanda ya isa ya sanya ni dole. Da ace ina jin yunwa ne dole na yi don cikina da 'ya'yana."
"Ke!" Ya daka mata tsawan da ya sanya ta tsaya cak.
"Wuce ki ɗora mini tuwo." Ya ce tare da nuna kicin yana zare mata ido.
Zumɓura baki ta yi, ta tsaya ba tare da ta ce masa komai ba. Ganin haka ya shiga ƙoƙarin neman abun duka. Da sauri ta shige tana hawaye.
Ruwa ta sanya a kettle sannan ta fara jajjage. Kafin ta gama ya tausa ta yi tankaɗe ta yi dame, tare da ɗora ruwan miyan a dayan murhun.
Tana girkin tana gyangyaɗi, har ta kamalla tuwon da taimakon Allah ta kawo masa.
"Allah ya sa ba ɗanye kira yi mini ba." Ya duba agogo ganin ɗaya ta yi.
Ba tare da ta tanka masa ba ta juya ta shige ciki.
Bayan ya gama cin abinci ya zauna yana kallo har ƙarfe biyu da rabi. Kashe kayan kallon ya yi, sannan ya shiga ɗakinsa ya kulle ƙofa.
Da asuba da ta tashi ta yi sallar asuba, don har ta so ta makara saboda girkin da ta yi. Tana ji yana wanka. Takaici da kishin sa ya kamata don ta san waya ya kwana yi da 'yan mata sa ya sanya shi wanka.
Tana ta sauraren ko zai fito sallah, amma har ta cire tsammani, ta ɗauki qur'aninta ta haye kan gadon yana karatu har lokacin tashi ta yi aiki ya yi.
Kicin ta nufa ta yi ɗumamen tuwon da ta yi, sannan ta ɗora ruwan indomie ta dafa wa Raihan ta sanya mata a kula.Wanka ta yi ta shirya ta tafi makaranta.
Marwana da Damir suna kan hanya zai kai ta makaranta. Hira take masa. Yawancin jiran kan karatunta ne, shi kuma yana ta dariya.
"Yauwa Yayana." Ta ce tare da kamo hannu sa ta riƙe wanda ba ya tuki.
"Akwai magana kenan" Ya yi mata maganar yana murmushi tare da kallonta sai kuma ya mayar kan hanya.
"Eh,"
"Ina jin ki ƙanwata."
"Ba ka ce za ka yi wa wannan matar kyauta ba?"
"Wacce?" Ya tambaya don shi ya manta da maganar da suka yi.
"Wannan 'yar makarantarmu."
"Ok, na gane ta." Ya ba ta masa tare da shiga get ɗin gidansu.
"Waya nake son na ka saya mata."
Da sauri ya kalle ta jin abin da ta ce."Waya kuma? Ita ta ce miki tana buƙatar haka ?"
"A'a." Ta ba shi amsa tana girgiza kai.
"Saboda me ya sa kika buƙata?"
"Dacewar hakan na gane Yaya, saboda ba ka wayar da take amfani da shi ba. Ko almajirin gidanmu ba zai rike ta ba."
Dariya sosai ya yi musamman yadda take yatsina fuska." Marwana rigima! Duk a gurin ki little Marwana, ta gaji nata rigimar. Ke in ban da abin ki. Allah bai halicce mu duka ɗaya ba. A haka da take da wannan wayar kar ki yi mamakin irin rayuwar farincikin da take yi, saboda Allah ya halicci mutane daban-daban, kuma rayuwarsu daban-daban."
"Na sani Ya Damir, amma ita tana da bukatar wayar. Tun da ka ga karatu take yi, in za ta yi assignment da karatu tana shan wahala."
"Duk da hakan ba ta wayar kamar shishshigi ne a rayuwarta."
"Ni dai Please Ya Damir, sai dai kuma in ba ka yi ninya ba."
"Na isa? Zan siya mata system da waya hakan ya yi miki?"
"Really?"
"Sure, for you sis." Ya ba ta amsa tare da ɗaga mata kai yana dariya.
"Na gode Ya Damir, Allah ya ƙara buɗi ya sanya ka fi haka."
"Amin sis," Ya ce mata.
Da ya sauke ta, gidan Hajiya ya wuce ya kai mata magani ta da ya siyan mata, sannan ya wuce gida don za su je check up yau.
Da ya isa ƙofar get ɗin gidan, ya yi hon mai gadi ya taso ya buɗe masa. Shiga da motar ya yi, sannan ya yi parking.
Kai tsaye falo ya shiga yana faɗin," Honey."
"Na'am." Ta amsa tare da rungume shi ta ba shi hot kiss.
"Ka dawo?"
"Eh, da fatan kin shirya."
"Am ready, we can go."
Ta ba shi amsa tare da ɗaukar jakarta.
"Karɓar jakar ya yi, sannan ya ɗauki makullin motarsa, ya kama hannunta suka fita suna sakarwa junasu murmushi.
A asibitin teaching hospital na Ahmadu Bello University Zariya. Suna zaune kan kujeru, hankalinsu ya ɗauki ga siririn likitan da yake ta yi musu bayani cikin harshen Nasara.
Jikin Damir ya yi sanyi, yana kallon abar ƙaunarsa da take kallon likita. Hannunta ya kama sannan ya ce,"Ina da burin matata ta haifa mini yara, amma saboda lafiyarta Doctor in ta haihu a juya mata mahaifar." Ya ƙarashe maganar cikin sanyi.
"Yanzu shi ke nan ya'ya biyu kawai zan haifa maka Baby? Tun kafin mu yi aure ka sanar mini kana son ka cika family ɗinku da 'ya'ya tun da ba ku da yawa. Kenan aure za ka ƙara?"
"Kece mace ta farko da na so kuma ta ƙarshe. Kin ji na yi miki alƙawarin ba zan taba auren wata 'ya mace ba."
Duk da abin da ya ce hankalinta bai kwanta ba.
Ƙara janke hannunta ya yi cikin wani yanayi. "Doc ka gaya mini yadda zan ƙara kula da lafiyarta saboda na rayu da ita har abada."
"Ba ka da matsala, saboda kana kula da duk wani abu da mai cutar sikila zai kula."
"Shi ke nan na gode. In Sha Allah, da zarar watan haihuwarsa ya tsaya zan kawo ta a cire babyn."
"Allah ya kaimu." Ya ba shi amsa tare da miƙewa ganin sun mike.
Jikinta a mace har suka isa gurin motarsu. Ya buɗe mata ta shiga. Zama ta yi bayan ya shigo ta rungume shi tare da fashewa da kuka.
"Ina sonka mijina, sai dai ina ji a jikinsa kamar ciwonka ba zai barni mu yi tsawon rayuwa ba. Ga shi kuma alamu sun fara nuna wa, tun da ba zan iya haifa maka yara ba. Dole ka yi wani auren, ka samu matar da za ta haifa maka yara" Ta ƙarashe maganar tana kara ƙanƙame shi.
"In har kika gaya mini haka sai na ji zuciyata ta sare. Ina jin za mu yi rayu dake har abada. Jikinsa yana bani kece mace ta farko kuma ta ƙarshe a gareni."
"Ina fatan hakan mijina. Ina son na rayu da kai har abada."
"Ni ma haka matata, in Sha Allahu zamu rayu tare." Ya furta yana shafa bayanta cikin tsigar rarrashi.
FARUK
Tun da daddaren da ya ci tuwon bai ƙara ci ba, don ko da safe da ta kai masa ɗumame, watsa mata mugun kallo ya yi.
"Ba zan ci ba saboda ɗanye kika yi mini. Shi zu ku ci har kwana biyu."
"Kwana biyu muna cin tuwo an ya da adalci kuwa?"
"Babu ai dama ba ki ganin adalcina." Ya ce mata cikin ɓaci rai.
"Gani na yi ko kai ba za ka iya cin tuwo har kwana biyu ba, don ba zai kai ba lalacewa zai yi."
"Kisa a firjin dama ai amfaninsa kenan."
"Tun da gas ɗin ya ƙare ka sanya ne?"
"Ni fa na gaji komai ki ce ni zan yi a gidan nan. Mene ne amfanin ki?"
"Lokaci ya kusa da zan taimaka."
Ɗaukar brief case ɗin da ya yi zai fice ba tare da ya ce mata komai ba.
"Allah ya dawo da kai lafiya." Ta ce tana kallon bayansa.Ba tare da ya amsa ba ya fice.
Tun da ta karya da tuwon ta kasa ci. Fita ta yi ta siyo musu awara da yaji suka ci da rana. Da daddaren daurewa ta yi, ta ɗunduma tuwon suka ci.
Cikin magagin bacci ta ji dirin motarsa. Da sauri ta sauko ta kunna fitilarsa, saboda babu wuta.
Fita waje ta yi ta bude masa get ɗin gida.
"Ba ki yi bacci ba?"
Tambayar ta yi mata bambarakwai! Wai namiji da suna Hajara.
"Na ɗauka kin yi bacci har zan buɗe get ɗin da kaina." Ya ce tare da rigata ɗaukar kayan da ya siyo.
Sororo ta yi tana kallonsa cikin alamun bacci.
"Mu shiga ciki." Ya ce mata cikin taushi murya yana mata kallon ƙasa-ƙasa, wanda ya sa ya ta ji wani iri.
Da suka shiga falo zama ya yi a two seater sannan ya ɗaga idanunsa yana kallonta da ta yi tsaye kamar soja."To ki zauna mana." Ya ce yana nuna mata gefensa.
Zama ta yi, tare da ƙasa da kanta tana mamakin canzawarsa.
"Kin ci abinci?"