← Book details Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 40

Sashe 29

Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kama hannunsa ya yi suka ƙarasa inda take kwance."Ka yi mata addu'a dole a kaita makwancinta."

"Nazir, kai ma ka yadda Batula ta mutu?"

"Ka yi haƙuri lokacinta ya yi." Ya ce tare da kama hannunsa ya kai shi har gurin.
Durƙusawa ya yi ya fashe da kuka."Batula, kin ga ana son a raba mu? Don Allah ki tashi ki gaya masa ba ki mutu ba."

Ganin shiru babu magana ya sanya shi sakin kuka." Da gaske kin mutu? Ba za mu rayu tare ba?"

Da ƙyar ya miƙar da shi, sannan aka samu aka ɗaga makarar da su fice. Ganin haka Little Marwana ta riƙe tana kuka tana faɗin,"Mommy, ina za ki je? Daddy za su fita da Mommy." Jin abin da take faɗi ya ƙara tayar da hankalinsa. Ya ƙaraso da gudu ya riƙe makarar. Da ƙara aka samu aka raba shi da gawarta, sannan aka fita da shi. Ganin sun fita ya ƙara zubewa haka Marwana.

Rayuwa kenan mai canzawa. Suna cikin farin ciki 'yan awannin da suka wuce, amma yanzu komai ya canza musu. Daga farar takadda zuwa baƙa mara daɗin karantawa.

Faruk
Tun da suka gama wayar ya kashe wayar yana huci. Rashida ta so daga inda take, ta sanya hannunta ta jawo sa jikinsa. "Don Allah ka share su, kar maganar da suka gaya maka ya ɓata mood ɗin ka."

"Ki ƙyale ni da su marasa mutunci. Ni na rasa dalilin da ya sanya suke shiga cikin rayuwar iyalina."

Shiru ta yi ba ta ce masa komai ba. Ganin haka ya kwanta akan gadon yana mamakin Nasreen na da ciki, amma ba ta gaya masa ba."Kenan ɓoyewa ta yi sai dai ya ganta da shi kenan?" Ya tambayi kansa cikin tsananin mamaki.

Kwanciyarsa ya yi suka yi bacci da ba suka ci bashin sa. Sai kusan sha biyu sannan ya tashi ya yi wanka. Kallon Rashida ya yi, wacce ta fito daga bayin tana share ruwan kanta."Baby, bari na je na duba Nasreen, sannan zan yi wa Anty Asiya maganar tarewar mu."

"Ai da ka ƙyale su mu yi zamansu anan."

Wani banzan kallo ya yi mata jin abin da ta ce."An gaya miki yayo kuɗin na ke yi, da zan yi rayuwar aurena a hotel?"

Fita ya yi bayan ya yi mata sallama. Kwanciya ta yi tana tunanin hanyar da za ta ci kudinsa.

Jin abin da ya ce sai ta kalle shi kawai, dama ta san shi da shegen maƙo, don da bikin duk abin da ta ce za a yi sai ya rage kuɗin. Tsananin mamaki ya kamata da bai yi mata kyautar kuɗi ba, saboda maganin da Malam ya ba ta ya tabbatar mata da ingancinsa. Ko da ace bai tabbatar mata ba, yadda ta sha wahala a darenjiya ta san cewa yana da kyau. Tsanannin mamakin maƙonsa ya ƙara kama ta, amma a ranta ta sanya za ta yi maganinsa, duk hanyar da za ta fito, saboda ba zata iya rayuwa babu kuɗi ba, watakila kuma don bai san inkiyar sunanta Rashida lashe money ake kira ta ba. Tsakaninta da kuɗi akwai amana domin in har kana dasu sam baka da damuwa. Kudi kenan abokan harka. In har yana tarawa ba ya kashewa. Ita za ta koya masa yadda zai kashe. Wayarta ta ɗauko tana son kiran Malam. Sam zuwa gurin Nasreen da ya ce zai yi, bai dame ta ba, tun da ba ta a gabansa. Asalima ba ta jin kishinta, musamman yadda yake kusheta. Kamar yadda yake gaya mata ƙaddara ya sanya ya aureta, ta yarda da hakan, saboda kamarsa ɗan gayu babu yadda za a yi ya zauna da irinta a yadda yake fasaltata da kalmomi irin kucaka ƙazamiya wacce ba ta iya tarairayar namiji ba.

Faruk hon ya rinƙa yi a ƙofar gidan domin a tunaninsa ta dawo. Ganin ba a buɗe ba, ya sanya shi fitowa ya sanya ɗan makullinsa ya shiga.

Tsananin mamaki ya kama shi ganin bushashshen jini a ɗakinta. Fita ya yi zuwa falo ya zauna. Wayarsa ya zaro ya kira numbarta. A wannan lokacin tana cikin halin gaba kura baya siyaki. Tun da ta ji Batula ta rasu, sai da ta yi suma.ya fi a ƙirga. Ahmad hankalinsa ya tashi. Shi kansa mutuwar ya gigita shi. Yana rungumeta da ita wacce ta fita hayyacinta.

"Yanzu da gaske ta mutu? Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Kaicona sun yi mini alkhairi na saka musu da tsiya." Ta ƙarashe maganar da sakin razanannen kuka.

"Nasreen, don Allah ki natsu wani bai isa ya kashe wani ba. Lokacinta ne ya yi. Ki duba halin da kike ciki." Ganin duk rarrashinta da yake yi, amma ta ƙi kwantar da hankalinsa ya sanya shi kiran gida. Mama da Zainab suka zo cikin tashin hankali.

Fita ya yi daga asibitin cikin tashin hankali. Lamarin ya ruɗa shi. Ofishin likitan ya shiga don ya bukaci ya ba su sallama, domin fitar da ita daga asibitin kawai zai sanya ta kwantar da hankalinta.

WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme.

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg

*WASU MAZAN*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan

08144072423

PAGE 17

Fita ya yi daga asibitin cikin tashin hankali. Lamarin ya ruɗa shi. Ofishin likitan ya shiga, don ya bukaci ya ba su sallama, domin fitar da ita daga asibitin kawai zai sanya ta kwantar da hankalinta.

Bayan fitarsa Faruk ya kira wayarta. Mama ta sanya Zainab ta ɗaga wayar.Tambayar da ta ji ya yi mata, ya sanya ta kalleta daidai lokacin da ta gaya masa."Dama wannan mara mutuncin bai zo asibitin ba?" Ta yi mata tambayar tamkar tana asibitin.

"Ban sani ba mama, ya dai tambaye ni kuma na gaya masa."

"Mai ya sa kika gaya masa?" Ahmad ya faɗa daidai lokacin da ya shigo ya ji abin da take faɗi.

Tsuru-tsuru ganin haka ya kalli Mama ya zauna gefenta ya ce,"Wallahi ban ga amfanin zama da Faruk da Nasreen take yi ba. Ya sake ta mana rabuwarsu ya fi kawai. Tun da ya yi aure Allah ya ba ta wanda ya fi shi. Da ace ya kula da ita da duk abin da yaru bai faru ba."

"Kai innalillahi! Wallahi lamarin bai yi daɗi ba. Kuma da gaske matarsa ta mutu?"

"Eh, dama tsohon ciki ne da ita, kuma likitocinsun gargaɗe ta, kar ta sake ta haihu a gida. Da zarar cikin ya shiga watannin haihuwa za a cire mata. Dalilin mijinta ya bawa Nasreen jini kishi ya sanya naƙuda ta tashi. Kamar wasa ta haihu ta rasu."

"Kai mutuwar kenan? Rai ba a bakin komai yake ba." Mama ta ce cikin kaɗuwa.

"Ki bari kawai Mama yau na shiga cikin tsananin tashin hankali.

"Allah ya yi mata rahma, amma babu abin da za mu yi suga farincikimu, kuma ya kamata mu je musu ta'aziya?"

"Ai ya zama dole."Ya furta cikin damuwa. Ya buɗe baki zai yi magana, sallamar Faruk ya katse shi. Da sauri ya miƙe ya ƙarasa ƙofar ya dakatar da shi.

"Uban me ka zo yi?"

"Ban gane ba? Matata na zo gani." Ya ce masa yana harararsa.

"Ka san Allah ba za ka shiga cikin ɗakin nan ba, kuma a yau sai ka rubuta saki ka bata."

Jin abin da ya ce ya ɗaga murya ya ce,"To sai na ga uban da zai sanya na saki matata. Banza wawa kawai don na taimaka ina zaune da ita. Karka manta amarya na yi jiya, in har na sake ta ita ce da wahala. Yarana kawai na ke tausayawa, amma kai ka san babu abin da zai sanya na ci gaba da rayuwa da bagidajiyar ƙanwarka."

Jin a bin yake faɗi sai kawai zuciya ta kai shi ya shake shi. Dabbe suka fara kicikici. Dama Ahmad jiran ranar yake, don haka ya fara aika masa da nushi.

Ganin suna shirin illanta juna Mama ta wanka wa Ahmad mari."In har ka ƙara kai masa nushi ban yafe maka ba Ahmad." Ta faɗa cikin Muryar kuka.

Cak ya tsaya yana huci, ganin haka Faruk galla masa harara, yana mai da numfashi.
Chapter 29 · 0% Book details